WHO ta yi gargadi kan bazuwar sabon nau’in korona da ke bazuwa kamar wutar-daji

Asalin hoton, Reuters
Hukumar Lafiya ta Duniya WHO, ta ce yanzu an samu tabbacin bazuwar sabon nau'in kwayar cutar korona, Omicron a kasashe 89, inda yawan mutanen da ke kamuwa ke ninkawa biyu a duk kwana daya da rabi zuwa kwana uku.
Daman a farkon makon nan da ke karewa hukumar ta WHO, ta yi gargadi cewa asibitoci su shirya kan gagarumin Karin da za a samu na yawan marassa lafiya, kuma ta shawarce su kan su tanadi karin ma'aikata da gadaje da kuma iskar oxygen da ake sanya wa marassa lafiya.
Wani abu da za a ce al'umma sun kwana da sani a kan sabon nau'in kwayar cutar koronar, shi ne wannan nau'i yana bazuwa cikin sauri fiye da duk wani nau'i da aka sani a baya.

Asalin hoton, Reuters
A kasashen da ba a yi allurar riga kafin cutar ba sosai da ma inda aka yi rigakafin sosai yawan mutanen da ke kamuwa na karuwa.
Sai dai babu isassun bayanai da za su nuna da kashi nawa ne nau'in na Omicron ke bijire wa riga-kafi.
Ba a dai sani ba ko kwayar cutar nau'in Omicron tana iya janyo rashin lafiya maras tsanani da kuma mai tsanani ba, ko kuma allurar riga-kafin korona na kare mutane daga samun rashin lafiya mai tsanani.
Da yawa daga cikin mutane hadi da kwararru harkar lafiya sun yi fatan wannan lokacin huturu zai kasance farkon karshen wannan annoba.
To amma sai ya kasance kuma maimakon a ga hakan sai aka samu kai a wani yanayi na yaki cikin duhu, abin da ya sa har Hukumar Lafiya ta Duniya ke fargaba zai iya kusan durkusar da tsarin kula da lafiya na duniya.

Asalin hoton, EPA
A Birtaniya hukumomi sun bayyana cewa sama da sabbin mutane dubu goma ne suka kamu da sabo nau'in cutar, Omicron yayin da yake ta bazuwa a fadin kasar.
Bayanai sun ce an samu karin mutane 90,418 da ke kamuwa da cutar ta korona a kullum a fadin kasar a ranar Asabar, bayan kwanaki da aka yi ana samun mutane masu yawa da ke kamuwa.
Masu bayar da shawara kan harkokin kimiyya sun yi gargadin cewa mutanen da ake kwantarwa a asibitocin Ingila za su iya kaiwa dubu uku a kullum, idan ba a dauki sabbin matakan hana bazuwar cutar ba.
Yanzu dai kasashen duniya na ta daukar matakai na tsaurara wa domin hana bazuwar wannan sabon nau'i na cutar ta korona, inda a wasu kasashen har an fara hana bude wasu kantina da takaita lokacin zuwa wasu wuraren.











