EU ta hana ƴan Afirka da aka yi wa riga-kafin AstraZeneca shiga yankinta

Asalin hoton, Getty Images
Ƴan Afirka suna ta mayar da martani kan labarin da ke cewa ba za su iya yin tafiye-tafiye zuwa ƙasashe mambobin Tarayyar Turai ba daga ranar 1 ga watan Yuli idan har sun karɓi allurar rga-kafin cutar korona ta AstraZeneca da aka samar Indiya.
Hukumar Lafiya Ta Duniya WHO ta ce ba zai yiwu ƴan Afirka su sake fuskantar wasu dokoki na taƙaitawa ba saboda har yanzu nahiyar na fama da matsalar samun rigakafin.
Allurar rigakafin wanda kamfanin Serum Institute ya samar a Indiya bai samu sahalewar tafiye-tafiye ta ƙasashen Tarayyar Turai ba.
Daga cikin dukkanin rigakafi takwas din da WHO ta amince da su, huɗu ne kawai Ƙungiyar Magungunan Tarrayar Turai EMA ta sanya a cikin jerin wadanda ta amince da su.
A wani saƙo da shugaban cibiyar Serum ta Indiya Adar Poonawalla ya wallafa a Tuwita a ranar Litinin, ya ce tuni ya kai batun gaban masu sanya ido da kuma ƙasashen.
WHO ta ce Ƙungiyar EMA tana fuska yin biyu ta hanyar tambayar kamfanin Serum Institute na Indiya don samun amincewarsa kan rigakafin da ba a rarraba shi a ƙasashen Tarayyar Turai ba.
A baya Ƙungiyar Sufurin Jiragen Sama ta bayyana cewa ya kamata gwamnatoci su amince da dukkan rigakafin da WHO ta yarda da shi a wajen bayar da izinin shiga ƙasashensu.
Tuni dai ƙasashe da dama na EU suka fara amfani da tsarin, da suka haɗa da Spain da Jamus da Girka da Poland.
Ana sa ran sauran ma za su fara amfani da shi a watan Yuli.











