Yadda malaman addinai ke yaɗa labaran ƙarya kan riga-kafin cutar korona
Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:
A yayin da ake ci gaba da yi wa mutane allurar riga-kafin cutar korona a faɗin duniya, shugabanni na aiki tuƙuru don sa wa mutane ƙwarin gwiwar yarda a yi musu allurar.
Malaman addiani a hannu guda za su taka muhimmiyar rawa wajen jan hankalin mutane a yi musu allurar.
Wasu da dama kuma na ta ƙoƙrin yaɗa bayanan cewa alluran ba su da illa kuma suna aiki, amma a kowane addini akwai waɗanda ake samu su kuma suna kushewa, inda wasu ke yaɗa labaran ƙarya cewa allurar riga-kafin na jawo wa mutane abubuwa marasa kyau da yawa.
A wannan bidiyon, BBC ta yi duba kan hakan.