Hikayata 2021: Ana dab da sanin gwarzuwar gasar ta bana

Nana Aicha Abdoulaye da Aishatu Musa Dalil da Zulaihat Abdullahi su ne marubutan da labaransu suka yi zarra a bana.
Bayanan hoto, Nana Aicha Hamissou Abdoulaye da Aishatu Musa Dalil da Zulaihat Abdullahi su ne marubutan da labaransu suka yi zarra a bana

Ranar 26 ga watan Nuwamban 2021 ne za a sanar da gwarzuwar gasar Hikayata ta shekarar 2021.

Wannan ne karo na shida na gasar wadda aka fara a shekarar 2016 inda Aisha Sabitu ta zama gwarzuwar gasar ta farko. A shekarar da ta biyo bayanta kuma Maimuna S Beli ce ta kasance gwarzuwar gasar sannan Safiyya Jibril Abubakar a shekarar 2018.

A shekarar 2019 ne Safiyya Ahmad ta yi nasarar zama gwarzuwar gasar sannan a 2020 Maryam Umar ta zama gwarzuwar gasar.

A bana kuwa, mata uku ne za su fafata wajen darewa kujerar gwarzuwar gasar Hikayata - Nana Aicha Hamissou Abdoulaye ƴar asalin jihar Maraɗi ta Jamhuriyar Nijar da Zulaihat Alhassan ƴar jihar Kaduna a Najeriya da Aishatu Musa Dalili ita ma ƴar jihar Kaduna a Najeriya.

Wadda ta yi nasarar zuwa ta ɗaya a gasar za ta samu kyautar kuɗi dala dubu biyu ($2,000) da lambar yabo. Wadda ta zo zo ta biyu za ta samu lambar yabo da kyautar kuɗi dala dubu ɗaya ($1,000), ita kuma wadda ta zo ta uku za ta samu kyautar kuɗi dala ɗari biyar ($500) da lambar yabo.

Rufaida Umar Ibrahim da Maryam Umar da Surayya Zakari Yahaya
Bayanan hoto, A shekarar 2020, Maryam Umar (a tsakiya) ce ta zama gwarzuwar gasar Hikayata da labarinta mai suna Rai da Cuta yayin da Surayya Zakari Yahaya (a hannun hagu) ta zo ta biyu. Rufaida Umar Ibrahim ce ta uku a gasar.

BBC Hausa ta samar da gasar Hikayata ne don ƙarfafa wa mata marubuta guiwa da kuma haɓaka rubutu a harshen Hausa.

Shugaban Sashen Hausa na BBC, Aliyu Tanko ya ce "gasar ta kasance wata turba ga mata marubuta wurin fito da batutuwan da suka shafe su da zaƙulo hanyoyin matsalolin da suke fuskanta. Kuma mu dama fatanmu kenan."

Ita ma jagorar alƙalan gasar a bana Dokta Hauwa Bugaje ta jami'ar Ahmadu Bello da ke Zariya ta ce "kullum mata marubuta a ƙasar Hausa ƙara gogewa suke yi saboda damarmaki irin wannan gasa da ake ba su. A bana mun ga labarai masu nagarta, kuma wannan na nuna cewa kwalliya na biyan kuɗin sabulu."

A shekarar 2019, Safiyya Ahmad (a tsakiya) ce gwarzuwar gasar, Jamila Abdullahi Rijiyar Lemo ta zo ta biyu yayin da Jamila Babayo ta zo ta uku
Bayanan hoto, A shekarar 2019, Safiyya Ahmad (a tsakiya) ce gwarzuwar gasar da labarinta mai suna Maraici, Jamila Abdullahi Rijiyar Lemo (a hannun hagu) ta zo ta biyu yayin da Jamila Babayo (A hannun dama) ta zo ta uku

Labarin Maraici na Safiyya Ahmad labarin wata yarinya ce mai suna Karima wadda iyayenta suka mutu kuma riƙonta ya koma hannun gidan marayu. Daga baya ta yi aure amma ta yi rashin sa'a mijin ya riƙa gallaza mata.

Safiyyah Jibril Abubakar

Asalin hoton, Safiyyah Jibril Abubakar

Bayanan hoto, Labarin Safiyyah Jibril Abubakar ne ya yi zarra a cikin labarai kusan 300 da aka shigar gasar

Labarin 'Ya Mace na Safiyyah Jibril Abubakar labari ne na wata budurwa mai suna Halima wadda ta shiga tasku bayan ta kai shekara 17 babu wani tsayayye, alhali a bisa al'adar gidansu da yarinya ta kai shekara 14 ake aurar da ita.

Matsin lambar da take fuskanta daga iyayenta da sauran dangi ya sa ta amince ta auri Garba duk da cewa ba a gudanar da wani bincike a kan shi ba. Ga shi kuma mahaifinta ya ja mata kunne cewa kada ta kuskura a sake ta don idan ta dawo gida ba shi da halin daukar nauyinta.

Maimuna S Beli
Bayanan hoto, Maimuna S Beli ce gwarzuwar gasar ta 2017 da labarinta mai suna Bai Kai Zuci Ba

Labarin Bai Kai Zuci Ba na Maimuna S Beli ya bi rayuwar wata mata wadda ta mutu amma take yin fatalwa ta koma gidanta don ganin yadda rayuwar mijinta da ƴaƴanta ke gudana bayan mutuwarta.

Aisha Sabitu
Bayanan hoto, Aisha Sabitu ce gwarzuwa gasar ta farko a shekarar 2016 da labarinta mai suna Sansanin Ƴan Gudun Hijira

Sansanin Ƴan Gudun Hijara na Aisha Muhammad Sabitu labari ne da ya yi tsokaci ne kan mawuyacin halin da 'yan gudun hijirar da rikicin Boko Haram ya raba da gidajensu suka samu kansu a wani sansani da ke jihar Adamawa.

BBC Hausa Hikayata

Asalin hoton, BBC