Hanyoyi bakwai da za a iya magance sauyin yanayi

Asalin hoton, Getty Images
Ana bayyana taron sauyin yanayi na COP26 wanda ake yi a Glasgow a matsayin matakin ƙarshe na taƙaita ɗumamar yanayi zuwa matakin 1.5 a ma'aunin celcius.
Baya ga irin yarjejeniyoyin da aka cimmawa, waɗanne irin manyan abubuwa ne ya kamata ƙasashe su yi domin daƙile matsalolin da suka shafi sauyin yanayi.
1. Barin makamashin al'ada daban-daban cikin ƙasa
Ƙona makamashi daban-daban kamar su ɗanyen man fetur da gas da kuma musamman gawayi wanda ke fitar da iskar carbon dioxide zuwa sararin samaniya da hakan ke haddasa riƙe zafi da kuma ƙara zafi a yanayin duniya baki ɗaya.
Wannan wata matsala ce da ake da buƙatar magance ta a matakin gwamnati muddin ana so a taƙaita zafi a matakin 1.5 a ma'aunin celcius - wanda shi ne matakin da ake gani a matsayin wata hanya da idan aka wuce ta za ta kawo mummunan sauyin yanayi.
2. Daƙile fitar da sinadarin methane
Wani rahoton baya-bayan nan na Majalisar Ɗinkin Duniya ya bayar da shawara kan cewa rage fitar da methane ko gas maras wari zai iya bayar da gudunmawa matuƙa wajen daƙile matsalolin sauyin yanayi.

Asalin hoton, Getty Images
Akwai adadi mai yawa na methane wanda ake fitarwa sakamakon ƙona gas a lokacin da ake haƙo ɗanyen mai kuma za a iya dakatar da hakan idan aka ɗauki matakan yin hakan. Ƙara nemo hanyoyi na zubar da bola na da muhimmanci, sakamakon wuraren da ake cikawa da bola su ma suna zama wata ƙarin matsala na samar da sinadarin methane.
A taron COP26, kusan ƙasashe 100 ne suka amince su daƙile fitar da sinadarin methane a wata yarjejeniya da aka cimmawa tsakanin Amurka da Tarayyar Turai. Ƙasashen duniya sun ɗauki alƙawarin rage fitar da sinadarin methane da kashi 30 ckin 100 idan aka kwatanta da matakin da ake kai a shekarar 2020.
3. A koma amfani da makamashin da ba ya ƙarewa
Samar da wutar lantarki da kuma amfani da abubuwa masu fitar da zafi sun fi bayar da gudunmawa fiye da kowane ɓangare.
Sauya amfani da makamashi a duniya daga wanda aka fi dogara da shi wato na al'ada zuwa wanda ya fi zama tsaftattace na da muhimanci matuƙa wajen rage ɗumamar yanayi.

Asalin hoton, PA Media
Akwai buƙatar amfani da iska da kuma samar da lantarki ta hanyar amfani da hasken rana su zama hanyoyin da aka dogara da su zuwa 2050 idan ana so ƙasashe su cimma burin da ake so a cimmawa zuwa shekarar 2050.
Ƙalubalen dai ƙadan ne. Domin ƙarancin iska na nufin ƙarancin lantarki sai dai amfani da batira zai taimaka matuƙa wajen ajiye wutar da aka samar idan ana son amfani da wutar.
4. Barin amfani da fetir da diesel
Ana buƙatar a sauya hanyar da ake amfani da ita wajen tafiyar da abubuwan da ake amfani a su wajen sufuri kamar mota da jirgin sama da na ruwa.
Jingine amfani da motocin da ke amfani da fetir da diesel da kuma koma wa amfani da motoci masu amfani da lantarki zai zama abu mai sarƙaƙiya.

Asalin hoton, Getty Images
Za a iya amfani da hydrogen wajen tafiyar da motoci ƙirar bas ta hanyar makamashi maras ƙarewa.
Haka kuma masana kimiyya na aikin samar da makamashin da za a rinƙa amfani da shi domin tafiyar da jirage duk da cewa masu fafutika na roƙon mutane su rage amfani da jiragen sama a matsayin hanyr sufuri.
5. Ƙara shuka itatuwa
Wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya a 2018 ya bayyana cewa idan ana so zafin duniya y taya ƙasa da 1.5C dole ne a cire Carbon Dioxide daga iska.
Dazuzzuka na bayar da gudunmawa wajen tsotse shi daga duniyarmu, wanda hakan wani dalili ne da masu fafutika da masana kimiyya suka dage kan cewa akwai buƙatar a rage sare itatuwa a duniya.

Asalin hoton, Reuters
Ana kallon shirye-shiryen da ake yi na shuka itatuwa sosai a matsayin hanyar daƙile sinadarin C02 wato Carbon dioxide.
6. Daƙile iska gruɓatacciya daga sararin samaniya
Sabbin fasahohi da ke fitowa waɗanda ke cire C02 daga sararin samaniya da kuma dakatar da da shi zai iya ak rawa muhimmiya.
Ana ta gina wurare da suke taimkawa wajen totse irin waɗannan sinadaran a Texas da Switzerland. Wuraren na amfani da fankoki ne domin kora iska ta hanyar wata matatar sinadarai.

Asalin hoton, Climeworks
7. Bai wa ƙasashe masu tasowa taimakon kuɗi
A taron sauyin yanayi da aka yi a 2009 a Copehagen, ƙasashe masu ƙafin tattalin arziki sun yi alƙawarin bayar da dala biliyan ɗaya a matsayin taimako zuwa 2020, waɗanda kuɗin za a iya amfani da su wajen yaƙi da sauyin yanayi.
Ƙasashe sun kasa cika wannan alƙawari, duk da cewa gwamnatin Birtaniya waɗanda ke jagorantar taron na sauyin yanayi ba da daɗewa ba suka fito da tsarin bayar da kuɗin zuwa shekarar 2023.











