Sauyin Yanayi: Hanyoyi 10 na yaƙar illolin sauyin yanayi

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Daga Roger Harrabin
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC environment analyst
Masu binciken sun tattara wasu hanyoyi da suka fi dacewa mutane su bi don rage abubuwan da ke kawo sauyin yanayi.
Matakan da aka dauka dangane da annobar cutar korona sun nuna cewa duniyar a shirye take ta karbi manyan sauye-sauye idan tana ganin sun zama dole, a cewarsu.
Kuma rahotan ya kara da cewa dole ne gwamnati ta sake fasalin ayyukanta.
Dole ne kare doron kasa ya zama kan gaba ga masu madafun iko, a cewar rahoton.
Masu binciken sun bukaci al'umma ta taiamka wajen daukar matakan rage abubuwan da ke sauya yanayi.
Kang aba a jerin shi ne rayuwa ba tare da mallakar mot aba, wanda zai sa mutum daya ya rage kusan tan 2.04 na iskar carbon da yake fitarwa duk shekara.
Wannan ya biyo bayan tuka mota mai amfani da batir - wanda zai rage tan 1.95 na iskar carbon da mutum daya ke fitarwa duk shekara - da rage a hawa jirgin sama a kalla sau daya a shekara - wanda zai rage tan 1.68 na iskar carbon duk mutum daya.
Jerin ya nuna cewa ayyuka kamar sake amfani da wasu abubuwa na da muhimmanci amma bas a rage fitar da gurbatacciyar iska sosai.
Sauya tunani
Shugabar masu binciken, Dakta Diana Ivanova ta Jami'ar Leeds ta shaida wa BBC News cewa: "muna bukatar mu sauya tunaninmu gaba daya.
"Dole ne mu amince kan yawan iskar carbon da za mu rika fitarwa dangane da sharuddan yawanta da duniyar mu ke iya dauka - sai mu gina rayuwarmu kan wadannan sharudda.
"Zabi 10 muke da su yanzu, ba tare da wasu sabbin kirkire-kirkire masu rikitarwa ba."
Dakta Ivanova ta ce kullen cutar korona ta nuna cewa mutane da yawa na iya rayuwa ba tare da mot aba idan aka inganta motocin haya da zaburar da mutane su rika daba sayyada da tuka keke.
Bincikekenta ya nuna cewa masu hannu da shuni sun fi hawa jirgin sama kuma sun fi tuka manyan motoci sannan sun fi cin abinci.
'Batun dacewa da rashinsa'
Ta ce: " Gaba daya duniya na fama da sauyin yanayi, amma ba mai karamin karfi ne ke hawa jirgin sama a kai a kai ba - masu hawan bas u da yawa, kuma harajin jirage bai taka kara ya karya ba. Batu ne na abin da ya dace da akasin haka."
A jerin da ta yi, ta sa amfani da makamashi marar karewa da hawa motar haya na hudu da na biyar.
Na shida kuwa shi ne dumama gidanka yadda ya kamata wanda kerage kwatankwacin iskar carbon tan 0.895.
Na bakwai shi ne daina cin nama da kwai da madara zuwa cin kayan itatuwa kawai wanda ke rage tan 0.8 na iskar carbon.
Sauran manyan ayyukan su hada da yin amfani da na'urar sanyayawa da dumama wuri; daina amfani da abin girki na zamani zuwa mafani da makamashi marar karewa.
Dakta Ivanova ta ce idan mutane suka dauki wadannan matakan, za a rage kwatankwacin iskar carbon da ake fitarwa duk mutum daya ko wace shekara da tan 9.
A muhallai yanzu a Burtaniya ana fitar da tan 10 na isakar carbon yayin da a Amurka ake fitar da tan 17.

Asalin hoton, PA Media
'Bincike mai amfani'
Binciken, wanda mujallar Environmental Research za ta buga kwanan nan, y ace wadannan abubuwan na da muhimmanci matuka, amma bas a yin wani tasiri sosai ga yanayi: rufin gida da ake shuka tsirrai a kai; rage amfani da takarda; sayen kaya da za su dade; rage karfin na'urar dumama gida da sake amfani da wasu kayan gida, wanda ke rage kwatankwacin iskar carbon tan 0.01 duk shekara in ji Dakta Ivanova.
Za a kalubalanci wasu abubuwan da binciken ya gano. Wasu na ganin cewa yanayi na da matukar muhimmanci kamar yadda cutar korona ke da muhimmanci yayin da wasu bas a ganin haka.
Farfesa Tommy Wiedman na Jami'ar New South Wales a Australia y ace: "Wannan bincike ne mai dumbin amfani. Amma ya duba yawan iskar carbon da mutane ke amfani da shi ne kawai, bai duba sauran abubuwa kamar rashin isasshen ruwa ba saboda hakar karfen lithium da ake yi don sarrafa motoci basu amfani da batir.
Libby Peake, ta kungiyar bincike ta Green Alliance ta shaida wa BBC cewa: "Kada mutane su daina ayyukan kwarai kamar sake amfani da wasu kayan gida, wanda ke rage yawan iskar carbon da ake fitarwa kuma yake hana barna."
"Inganta kayayyaki zai bai wa mutane damar sayen kayan kadan amma masu inganci kuma su yi rayuwa a gidajen da ba a cika fitar da iskar carbon ba. Wannan binciken bai duba wadannan abubuwan ba."

Asalin hoton, Reuters











