Ko sauyin yanayi ya haifar da zafi mai kisa?

A man drinks water from a bottle in front of a hot Sun

Asalin hoton, Getty Images

Masu bincike a bangaren sauyin yanayi sun dade suna gargadin cewa doron kasa zai fuskanci yanayi wanda "kusan mutane ba za su iya zama a kansa ba" zuwa shekarar 2070.

Amma wani sabon bincike da aka wallafa a mujallar kimiyya ta Science Advances ya gano cewa an fara fuskantar wannan yanayi.

Yanayi masu hadari da suka hada zafi da rashin kadawar iska na bayyana a fadin duniya, kuma duk da cewa wadannan yanayi kan faru ne tsawon sa'o'I, suna faruwa a-kai-a-kai kuma suna da tsanani, a cewar masu binciken.

Sun duba bayanai sa'a-sa'a daga cibiyoyin da ke duba yanayi 7, 877 tsakanin shekarun 1980 zuwa 2010.

Sakamakon binciken ya nuna cewa yanayin tsananin zafi ya rubanya a wasu yankunan masu zafi.

Ko wane yanayi na zuwa da zafi da rashin kadawar isak wanda idan suka dade suna iya kisa.

A ina aka ga irin wannan yanayi?

An ga aukuwar wadannan yanayi a bangarori da daman a Indiya da Bnagladesh da Pakistan da arewa maso yammacin Australiya da gabar tekun Bahar Rum da yankin Gulf na Mexico a Calofornia.

Alkaluma mafi muni da ka iya kisa da aka gani sau 14 a biranen Dhahran/Dammam a Saudiyya da Doha a Qatar da Ras Al Khaimah a Hadaddiyar Daular Larabawa, wadanda idan aka hada suke da yawan mutane sama da miliyan biyu.

Wasu bangarorin kudu maso gabashin Asiya da kudancin China da yankunan Afrika masu zafi da yankin Caribbean na cikin wuraren da aka ga irin wanann yanayi.

A man and two children in traditional dress stare across water at a city in the Persian Gulf

Asalin hoton, Getty Images

Yankin kudu maso gabashin Amurka ya fuskanci yanayi masu tsanani musamman a kusa da gabashin Texas da Louisiana da Mississippi da Alabama da Florida. Biranen New Orleans da Biloxi sun fi kowanne fuskantar mummunan yanayi.

Yadda zafi ke kisa

Mafi yawan cibiyoyin gwada yanayi a fadin duniya na gwajin ne da na'urorin thermometer biyu.

Ta farkon na daukar alkaluman yanayi a isan - sune alkaluman da muke gani a manhajojin da ke nuna yanayi ko a talabijin.

Daya na'urar kuma na gwada yawan ruwan da ke cikin iska. Ana gwada shi ne ta hanyar nade na'urar thermometer a cikin jikakken kyalle kuma yawanci sakamakon basu kai wa yawan makin yanayin iska zalla.

Ga mutane, wannan matsanancin yanayi na zafi na iya janyo munanan lamurra nan gaba a duniya mai dumi.

Wannan ne ya sa gwajin yanayi da na'urar thermometer mai amfani da kyalle mai danshi ke da matukar muhimmanci.

Yayin da yanayin jikin dan Adam ya ke maki 37 a ma'aunin Celcius, fatarmu ba ta wuce maki 35 a ma'aunin Celcius.

Wanann yanayin yana ba mu damar yin gumi don sanyaya jikinmu: ruwa na fita daga fatarmu don mu rage zafin cikin jikinmu, kuma idan ruwan ya bi iska yana rage mana jin zafi.

Yayin da wannan tsarin ke aiki da kyau a sahara, bai cika aiki sosai ba a wurare masu zafi inda isak ke cike da danshi.

Don haka idan yawan ruwan da ke cikin iska ya karu kuma yanayi ya kai maki 35 a ma'aunin celcius ko ya haura, zufar da ke jikinmu ba za ta yi saurin bushewa ba kuma jikinmu zai rage aikinsa na fitar da zafi.

A wasu lokutan ma, jiki na iya daina fitar da zafi kwata-kwata. Idan aka kai ga haka, idan har ba a shiga wuri mai sanyi ba, misali inda aka kunna na'urar sanyaya daki, zafin da ke jiki na iya saw a kayan jikin mutum kamar koda da hanta su daina aiki.

The Sun sets on a beach as two people sit by a lookout tower

Asalin hoton, Getty Images

Ko mutumin da ke da cikakkaiyar lafiya na iya mutuwa cikin sa'o'I 6.

Kawo yanzu, ana tunanin cewa na'urar gwada yanayi ta thermometer mai amfani da kyalle mai danshi ba ta cika gano yanayin da makinsa ya haura 31 ba.

Sai da a 2015, a birnin Bandar Mahshahr na Iran, masu gwada yanayi suka gano yanayi da ya kusa maki 35 a ma'aunin Celsius. Yanayin isakr wurin a lokacin ta kai maki 43.

Amma a cewar binciken na baya-bayan nan, an samu kololuwar yanayin na maki 35 a ma'aunin Celsius a kasashen yankin Gulf fiye da sau 12 a lokacin da ake gudanar da binciken, tsakanin sa'a daya zuwa biyu.

"Yawan ruwan da ke iska ke haifar da tsananin zafin na yankin Gulf ba yanayi ba, amma kuma sai idan yanayi yah aura kima sannan ake samun irin haka," a cewar shugaban masu binciken Colin Raymond, wani mai bincike a Jami'ar Colombia.

Ta yaya Karin bayani zai taimaka?

Mafi yawan bincike kan yanayi a baya sun gaza gano wadannan sauye-sauye da ke afkuwa, a cewar binciken, saboda masu bincikena na duba matsakaicin zafi da yawan ruwan da ke iska ne a wurare masu girma, kuma a lokuta masu tsawo.

Colin Raymond da abokan aikinsa sun duba bayanau na sa'a-sa'a daga cibiyoyin da ke sa ido kan yanayi a fadin duniya, don gano irin wadannan yanayi da ke afkuwa na dan kankanin lokaci a wuraren da bas u fiye girma ba.

"Bincikenmu ya amince da na baya da ke nuna cewa za a iya samun yanayin da zai haura maki 35 a matsakaicin wuri nan da shekara ta 2100," in ji Colin.

"Abin da kawai muka kara shi ne na wani dan lokaci kuma a wuraren da bas u fiye girma ba, ana ganin irin wannan matsanancin yanayin, kuma yana da muhimmanci mu samu sahihan bayanai."

Wa ya fi shiga hadari?

Mafi yawan wadannan lamurran yanayi sun fi aukuwa a garuruwan da ke gabar teku inda ruwan tekun da ke shiga iska ke samar da yawan danshin da iska za ta janye.

Bincike ya nuna cewa mafi yawan Indiya da Pakistan da Bangladesh za su fuskanci yanayi mai tsanani kuma wanda ya yi kusa da wanda aka yi has ashen yana iya kasha mutane zuwa shekarar 2100.

Tsananin zafin saman teku da tsananin zafin kasa na iya haduwa su samar da tsananin zafi.

"Sahihan bayanai za su taimaka mu fahimci inda mutanen da wannan yanayi ya fi shafa suke da kuma yadda za mu gargade su idan muka ga yanayin na karatowa," a cewarsa.

"Haka kuma zai taimaka su shirya wajen sayen na'urar sanyaya daki, da rage gudanar ayyuka a waje tare da daukar wasu matakan na dogon zango."

A man fills plastic containers with water on a cart drawn by a donkey

Asalin hoton, Getty Images

Binciken ya janyo fargaba kan mutanen da ke zaune a yankuna masu zafi kuma unguwannin marasa galihu wadanda ba za su iya kare kansu daga tsananin zafin ba.

"Mutane da yawa da ke kasashe masu karamin karfi na cikin hadari kuma bas u da wutar lantarki," a cewar Radley Horton, wani masanin kimiyya mai bincike a Lamont-Doherty kuma wanda ya sa hannu a binciken.

"Mutane da yawa a can sun dogara ne da noma wanda ke bukatar aikin karfi da kuma aiki a waje. Wannan na iya nufin ba za a iya zama a yankunan da wannan mummunan yanayi zai shafa ba nan gaba."

A cewar Steven Sherwood, wani masanin yanayi a Jami'ar New South Wales ta Australiya: Wadannan alkaluman na nufin cewa wasu bangarorin doron kasa na daf da fuskantar yanayin zafi wanda mutum ba zai iya jure masa ba.

"A da can an yi tunanin muna da sauran lokaci kafin a kai wannan matakin."