Coronavirus a Najeriya: Yawancin jihohi 'ba za su iya biyan albashi a shekarar nan ba'

Gwamnonin Najeriya

Asalin hoton, TWITTER/@ELRUFAI

Wani rahoton kungiyar kwararru kan tattalin arzikin Najeriya ya ce zai yi wahala yawancin jihohin kasar su iya biyan albashin ma'aikata a wannan shekara saboda rashin cimma bukatun Najeriya na kudaden shiga da ƙasar ta yi hasashe sakamakon tasirin annobar korona.

Rahoton kungiyar Nigerian Economic summit group ya ce kasancewar Najeriya mai dogaro da arzikin mai, tana fuskantar manyan kalubale guda biyu na faduwar farashin mai da kuma tabarbarewar tattalin arzikin duniya da annobar korona ke ci gaba da yi wa illa.

Binciken ya ce yadda jihohin Najeriya suka dogara da kason da suke samu daga gwamnatin tarayya da ke dogaro da arzikin fetir, hakan na nufin faduwar farashin mai zai sa jihohi su kasa biyan albashin ma'aikata.

To sai dai kuma masana tattalin arziki na ganin akwai gyara a rahoton.

Dr Muhammad Shamsuddeen, masani tattalin ariki ne a Najeriya ya kuma shaida wa BBC cewa akwai abubuwan da ya kamata ace an duba ba wai batun mai ba kawai.

Ya ce da farko dai a cikin kasafin kudin 2020 da aka yi a Najeriya, an kiyasta cewa man fetur zai iya kawo naira tiliyan biyu da biliyan dari shida da arba'in.

Masanin tattalin arzikin ya ce idan aka duba abin da man fetur din zai kawo bai kai kashi 30 cikin 100 na abin da gwamnatin kasar ke tunanin zata samu na kudi ba wanda ya haura naira tiliyan takwas.

Ya ce, rasa abin da bai kai kashi talatin cikin 100 ba,ba lallai ya zama barazanar da har za a ce ba za a iya biyan albashi ba.

Dr Muhammad Shamsudden, ya ce, ya kamata jihohi su rinka duba wadanne hanyoyi za su bi na habaka kudaden shiga da kuma rage dogaro da kudaden gwamnatin tarayya.

Ya ce wani abu kuma shi ne yawan ciwo bashi ba shi da wani alfanu musamman a wannan yanayi da ake ciki na annoba wadda ta zamo ruwan dare gama duniya.

Karin bayani kan coronavirus