Coronavirus a Kano: Yadda Ganduje ya rage albashin ma'aikatan gwamnati

Ganduje

Asalin hoton, Facebook/ Abba Anwar

Ma'aikatan gwamnatin jihar Kano da ke Najeriya sun yi zargin cewa gwamnatin Abdullahi Umar Gandue ta zaftare musu albashi a daidai lokacin da suke shirye-shiryen ƙaramar Sallah.

Galibin ma'aikatan da BBC ta yi hira da su sun ce an biya su albashi a tsohon tsari - wato kafin a yi karin albashi - kuma an zaftare kashi 10 zuwa 20 cikin 100.

"Albashin ya zo a tsohon tsari na minimun wage; a baya, ina daukar N76, 000 yanzu kuma ya koma N72, 000. Shi mai girma Gwamna ya fadi wadanda za a yi wa ragi, babu wanda aka ambata a cikin ma'aikatan gwamnati aka ce zai samu ragi," a cewar daya daga cikin ma'aikatan da lamarin ya shafa.

Wani kuma ya ce: "Albashi da aka biya gaskiya kusan tsohon albashi aka bayar, ma'ana katrin da aka yi na minimum wage an cire shi gaba daya."

A cewarsu, lamarin ya jefa su cikin halin ƙunci da rashin tabbas, ganin yadda ƙungiyar ƙwadago a jihar ke cewa ba a tuntuɓe ta ba kafin daukar wannan matsaya.

A makon jiya gwamnatin ta sanar da rage wa masu muƙaman siyasa rabin albashi saboda raguwar kuɗaɗen shiga dalilin faɗuwar farashin man fetur sakamakon annobar korona.

Kasashen duniya da dama dai sun rage ma'aikata, yayin da wasu kuma suka rage albashin ma'aikata a yayin da cutar korona take ci gaba da yin mummunan tasiri a kan tattalin arzikin duniya.