Hanyoyin da wata ke haifar da sauyin yanayi a duniya

Asalin hoton, Getty Images
Shekaru da yawa mutane suna duban wata don alamun canjin yanayi kuma sun yi imani cewa wata mai launi yana nufin ruwan sama, jan watan yana nufin igiyar ruwa yayin da farin wata ke nufin babu alamar ruwan sama ko kankara.
Gaskiya ne wata na nuna tasirin rinjayar yanayin duniya da sauyin yanayi ta hanyoyi da dama.
A cikin shekaru biliyan hudu da rabi da suka gabata, duniyoyin biyu sun yi karo da juna kuma suka faɗo cikin duniya ɗaya.
A lokacin karo na waɗannan duniyoyin biyu, duniya nan da wata duniya mai sunan Theia - wani karamin dutse ya fito ya zama duniyar wata da muka sani yanzu. Shi ya sa halin wata yana da tasiri sosai a rayuwar duniya.
Amma duk da haka yanayin wata da tasirinsa a doron kasa ba a cika fahimtar su ba. Yanzu ƙalubalen shi ne rarrabe tatsuniyoyi da gaskiya game da tasirin wata a doron ƙasa.
Babban tasirin da ake gani daga wata zuwa duniya shine igiyar ruwan teku. Yayin da duniya ke jujjuyawa a kullum, ruwan tekun na tsotso zafin watan, kuma hakan na sa ruwan ya yi zafi.
Yanzu NASA ta ce tunbatsar teku sakamakon canjin yanayi da zafin hasken wata na taka rawa wajen karuwar matsalolin ambaliyar ruwa daga igiyar teku a shekarun 2000.

Asalin hoton, Getty Images
Benjamin Hamlington, masanin kimiyyar bincike kuma shugaban ƙungiyar masana kimiyya da ke nazarin canje -canjen teku a NASA, ya lura da yadda igiyar ruwan tekun ke sauyawa bisa ga wasu dabi'u ko abubuwan halitta ɗan adam da kuma tasirinsu a kan biranen bakin teku.
Hamlington ya ce ambaliyar ruwa a yankunan bakin teku, wanda wata ke haddasa, na iya haifar da mummunan lalacewar ababen more rayuwa da sauya yankunan da ke gabar teku.
"Muna iya ganin yadda ake sake samun karuwar ambaliyar ruwa da ta ninka har sau hudu ko sama da haka. Tumbatsar da teku ke yi na karuwa a ko'ina don muna iya ganin wadannan ambaliyar ruwa a fadin duniya.
Elijah Rochlin, farfesa a Kwalejin Rutgers ya ce "Tsarin duniyar wata na iya zama kalubale ga mutane amma ga dabbobin daji yankunan bakin teku na iya zama babbar barazana gare su."
Rochlin ya ce "Lokacin da ake samun karuwar matsalolin yanayi da wata ke haifarwa, manyan teku na tunbatsa da tilasta ko kora sauraye gidajen ko fitowa su addabi mutane."
Idan babu igiyar ruwa, yanayin duniya zai bambanta. Igiyar ke da alhakin motsi na ruwa wanda ke sa ruwa ya yi zafi da sanyi a sassa daban -daban na duniya.

Asalin hoton, Alamy
Ana sa ran jujjuyawar wata zai sauya cikin 'yan shekarun nan gaba masu zuwa amma duk da haka wata yana shafar duniya ta wasu hanyoyi.
Ana kuma ganin wata na taimakawa wajen dumamar yanayi, musamman a yankin Arctic.
Hotunan tauraron dan adam sun nuna cewa yanayin zafi a yankin Arctic zai karu da digiri 0.55C a duk tsawon watan.
Wata yana ba da gudummawa ga kasancewar igiyar ruwa a sama da ƙasan teku a cewar Chris Wilson, ƙwararre a cikin teku.
Yayin da ruwa da kankara a cikin tekuna ba su ne kawai yankunan duniya da igiyar ruwa ke shafar su ba, wata kuma yana da tasiri a busasshiyar ƙasa kuma yanayi wani lamari ne da ke shafar yanayi.











