Ƴan ci-ranin da suka buɗe cibiyar bayar da tallafin kayan abinci

Matan yan Afrikan da suke aikin sa kai domin bayar da kayayyakin abinci a matsayin tallafi

Asalin hoton, Kate Stanworth

Bayanan hoto, Matan yan Afrikan da suke aikin sa kai domin bayar da kayayyakin abinci a matsayin tallafi

A cikin wasiƙun da ƴan jarida daga nahiyar Afrika suke turo mana, Ismail Einahe ya yi duba kan yadda ƴan ci-rani daga nahiyar Afrika ke taimakon juna a tsibirin Sicily na Italiya.

Short presentational grey line

A wata safiya a tarihin Palermo babban birnin Sicily, wani rukunin mata ƴan Najeriya ne ke ƙoƙarin buɗe wurin tattara abincin taimako ga iyalan ƴan ci-ranin Afrika.

Osas Egbon ce ke shirya wannan shiri a duk wata domin taimaka wa miskinai waɗanda suka shiga wani hali saboda annobar korona.

Wannan aikin na daga cikin tsarin da matan Benin City na Najeriya suka fito, kuma Ms Egbon ɗin ce ta ƙirƙiro wannan shiri tun a 2015 tare da wasu mata waɗanda aka yi safarar su zuwa Italiya.

Da dama daga cikinsu daga jihar Edo ta Najeriya kuma an kai su Italiya ne domin tilasta musu yin karuwanci.

Wata ƙungiyar bayar da agaji ta bayar da ɗakuna biyu ga shirin tattara abincin domin ajiye abincin. An bayar da ɗakunan ne a wata cibiya da ake kira Spazio Montevergine community centre.

Ƴan ci-rani da dama na ɗaukar Osas Egbon a matsayin mahaifiyarsu

Asalin hoton, Kate Stanworth

Bayanan hoto, Ƴan ci-rani da dama na ɗaukar Osas Egbon a matsayin mahaifiyarsu

A wajen wurin, wani taron matan Najeriya ne suka yi layi suna jira. Da ka ga matan wurin ka san suna jiran a ba su wani abu ne.

Wasu daga cikinsu sun zo da baro, da jakunan siyayya domin kwasar kaya.

A yayin da suke wannan jira, wasu daga cikinsu na danna waya wasu kuma na labari da wasu ƴan Italiya a Turancin Ingilishi da harshen Edo.

Wata yarinya ƴar shekara huɗu ta shiga cibiyar inda ta kira Ms Egbon "mamma", a yayin da mahaifiyarta ke jira a waje.

Wannan matar ta samu kayayyakin tallafin da aka bayar inda take hanyar komawa gida

Asalin hoton, Kate Stanworth

Bayanan hoto, Wannan matar ta samu kayayyakin tallafin da aka bayar inda take hanyar komawa gida

"Ni uwar kowa ce," in ji Ms Egbon, wadda shekararta 40 kuma take zaune a Sicily tsawon shekara 19.

Ana barin matan suna shiga cibiyar ɗaya bayan ɗaya. A cikin wurin, Ms Egbon tana kula da bayar da umarni kan yadda ake gudanar da abubuwa tare da masu taimaka mata waɗanda daga cikinsu akwai ma ƴan Italiya.

Suna ta ƙoƙarin saka abincin da za a bayar cikin jaka waɗanda dama suka shirya tun ranar da ta gabata.

Shinkafar Risotto

Ms Egbon ta bayyana cewa a kowane wata suna samun kusan iyalai 40 sun zo cibiyar da suke bayar da abincin.

Dukansu sun dogara ne a kan waɗannan kayayyakin, waɗanda cikin kayayyakin akwai man gyaɗa da taliya da shinkafa da abincin gwangwani kamar naman shanu da tumatir.

Osas Egbon ta rubuta abubuwan da ake da su waɗanda za a bayar a watan

Asalin hoton, Kate Stanworth

Bayanan hoto, Osas Egbon ta rubuta abubuwan da ake da su waɗanda za a bayar a watan

Wasu daga cikin abubuwan da kuma aka bayar da kyautar su har da man shanu da naman alade.

Mutane ba za su tambayi abin da suke so ba a ba su, amma dai za su iya musanya da wasu a yi bani gishiri na ba ka manda.

Har sai da wata mata ƴar Najeriya ta tmbya ko me za ta yi da shinkafar risotto idan an ba ta ganin cewa ba ta saba amfani da ita ba.

Ana amfani da wasu ɗakuna biyu a wata cibiya domin ajiye kayayyakin tallafin

Asalin hoton, Kate Stanworth

Bayanan hoto, Ana amfani da wasu ɗakuna biyu a wata cibiya domin ajiye kayayyakin tallafin

Wasu daga cikin waɗanda suka samu wannan tallafi har da wata uwa matashiya wadda aka yi safarar ta daga Najeriya domin tilasta mata ta yi karuwanci a Italiya.

Da ƙyar ta samu ta biya waɗanda suka yi safararta waɗanda kuɗin za su iya kaiwa dala dubu 35 - ba da daɗewa ba bayan ta iso ta haɗu da wanda suke dadiro tare.

Kamar yadda da dama daga cikin ƴan ci-ranin Afrika da suke a Palermo, ta dogara ne ga ayyuka irin waɗanda a samu yau gobe ba lallai ba, waɗanda ayyukan ba za su ba mutum kuɗin da ya kamata ba har su kai shi ƙarshen wata ba.

Ƴar ƙaramar ribar da suke samu ba ta isarsu su ciyar da iyalansu wanda hakan ke ja dole su je wajen bayar da tallafin abincin.

Ms Egbon, wadda take da wani masauki a wajen Palermo ga mata da ke son guduwa daga waɗanda suka yi safararsu, ta ce ta soma shirin bayar da abincin shekara guda kafin annobar korona.

Sai dai yadda ake buƙatar abincin ya ƙaru matuƙa sakamakon yadda mutane da dama suka rasa ayukansu.

Sakamakon hakan, an tilasta wa iyalai da dama faɗawa cikin talauci. Da dama daga cikinsu ba su da takardun zama a Italiya wanda hakan ya sa ba za su iya samun wani taimako daga ƙasar ba.

Osas Egbon daga haggu da sauran masu aikin sa kai inda take neman taimako daga coci da ƴan kasuwa

Asalin hoton, Kate Stanworth

Bayanan hoto, Osas Egbon daga haggu da sauran masu aikin sa kai inda take neman taimako daga coci da ƴan kasuwa
Presentational grey line

Kusan kashi 33 cikin 100 na baƙin da ke zaune a Sicily shekara biyu da suka gabata daga Afrika suke - amma akwai dubbai da ba bisa ƙa'ida suke zaune ba, kuma birnin na da mutum kusan miliyan 1.3.

Shi wannan shirin na bayar da agajin abincin ana yin sa ne a matsayin aikin sa kai - kuma MS Egbon na amfani da sanayyar mutane a Palermo da coci da kuma wuraren sana'o'i domin tattara abin da ya sawwaƙa a duk lokacin da ta samu sarari.

Amma dai ƙungiyar Ms Egbon tana samun taimako daga Banco Alimentare, wani babban wajen bayar da tallafin abinci wanda ke taimakonta da wasu kayayyaki.

A daidai lokacin da gari ke neman wayewa, ana kawo wasu kayayyaki da ba na abinci ba, inda aka ajiye wata kujerar guragu. Nan take Ms Egbon ta ce ta san iyalan da za su buƙaci wannan kujerar.

A lokacin da mace ta ƙarshe ke barin wurin bayar da abincin, a lokacin ne Ms Egbon za ta fara tattaunawa kan yadda za a samu abincin da za a bayar a wata mai zuwa.

A composite image showing the BBC Africa logo and a man reading on his smartphone.