Bidiyo: Garin da ake sarrafa tsummokara zuwa sabbin tufafi
Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:
Ɗinki na daga cikin sana'o'in da ke gurɓata muhalli a duniya. Kusan tan miliyan 100 na kaya ake zubarwa duk shekara.
Amma dama a ce mana za a iya adana waɗannan kayan da ake zubarwa - a mayar da su wani abu daban?
Wani ƙaramin gari a Italiya ya samar da wani tsari na sarrafa tsummokarai - kuma a yanzu hakan na taimaka wa masana'antar ɗinki.
Sofia Bettiza za ta ba mu labarin yadda abin yake.