Bidiyo: Bahaushiyar da ta ƙware a harshen Igbo
Ku latsa hoton da ke sama don kallon wannan bidiyo:
Hajia Safiya Ali, wata mace ce daga da ke zaune a jihar Enugun Najeriya fiye da shekaru 25. Hakan ya sa ta koyi harshen Igbo har ta ƙware.
Ta faɗa wa BBC cewa tana zaman lafiya a Enugu kuma ba ta ganin kanta a kowane waje idan ba Enugu ba.
Tana zaune da mijinta da 'ya'yanta 11 inda take magana da su da harsuna biyu wato Hausa da Igbo.
Tace bidiyo: Fatima Othman