Bidiyo: Makarantar da ake koya wa maza renon yara a Najeriya

Bayanan bidiyo, Bidiyon makarantar da ake koya wa maza renon yara a Najeriya

Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

Tolulope Adeleke wata unguwarzoma ce a Birtaniya da ta koma birnin Legas da ke kudancin Najeriya da zama, don ta samar da akukuwan da maza za su dinga zuwa don koyon yadda ake renon yara.

A makarantar tata ana koyar da ɗaura wa jarirai ƙunguzu da cire musu da sauran abubuwa da suka shafi hakan.

Ta ce ta yi hakan ne don ganin yadda a mafi yawan lokuta ake neman buƙatar namiji ya taya matarsa wasu hidindimun da suka shafi reno musamman a halin rashin lafiya amma sai mazan su kasa.

Wasu bidiyon da za ku so ku kalla