Boko Haram: Abin da BBC Hausa ta gano da ta je Zabarmari
Latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:
BBC Hausa ta bi tawagar majalisar dinkin duniya zuwa kauyen Zabarmari da ke jihar Boron Najeriya inda mayakan Boko Haram suka kashe gomman mutane a karshen makon jiya.
Jami'an majalisar dinkin duniyar sun ce an kai ziyarar ne da nufi n gano hakikanin abin da ya faru sakamakon kisan manoma fiye da 40 a kauyen.
Mazauna kauyen na Zabarmari sun ce ba su taba fuskantar bala'i irin wannan ba a rayuwarsu.
Sun yi kira ga gwamnatin kasar ta tsaurara matakan tsaro a yankin arewa maso gabashin kasar.
Wannan kisa ya tayar da hankalin 'yan kasar da ma duniya, lamarin da ya kai ga kira ga Shugaba Muhammadu Buhari ya sauka daga mulki.