Bidiyo: Matashiyar da ta rungumi sana'ar zayyana a Kaduna
Latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:
Maryam Aminu Maikudi Tela, wata matashiya da ke sana'ar zayyana a Najeriya, ta shaida wa BBC abin da ya ja hankalinta ta rungumi wannan sana'a.
Maryam, wadda take karantar kimiyyar hada magunguna a Jami'ar jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya, ta ce tun tana karama ta soma sha'awar zayyana.
A cewarta, tana kara samun kwarewa a fannin zayyana ne ta hanyar kallon bidiyon yadda ake yi a YouTube.
Maryam ta ce da farko ba ta dauki zayyana a matsayin sana'a ba amma daga bisani ta gane cewa hakan zai iya zama abin dogaro bayan da wasu 'yan uwanta da kawaye suka karfafa mata gwiwa.
Ɗaukar bidiyo da tacewa: Yusuf Yakasai