Yadda yarinya mai wasan barkwanci a Najeriya ta gina wa maihaifiyarta gida
Latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:
Fitacciyar yarinyar nan mai wasan barkwanci a shafin YouTube Emmanuella ta ce ta gina wa mahaifiyarta gida ne saboda irin kaunar da ke tsakaninsu.
Ta shaida wa BBC cewa mahaifiyarta ba ta taba zaton gidan da ake gina wa nata ba ne sai lokacin da aka mika mata makullansa.
A cewarta, za ta ci gaba da bai wa mahaifanta mamaki ta hanyar yi musu abubuwan da suke bukata.
Ta ce nan ba da jimawa ba za ta saya wa mahaifinta mota.