Bidiyo: Mutanen da ke tiyatar ƙara tsawo don yin ƙara kyau
Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:
Tiyatar ƙara tsawo al'amari ne mai wahalar yi da ya haɗa da sanya farce kai tsaye cikin ƙasusuwan ƙafar mutum - da ke bai wa wanda aka yi wa damar ƙara tsayi da santimita 13.
A baya a kan yi wa mutanen da ke da wata naƙasa ce kawai ko ciwo, amma a yanzu a kan yi wa ɗaruruwan mutane a shekara a asibitoci masu zaman kansu da dama a faɗin duniya da nufin ƙara musu tsayi don su yi kyau.
Tiyatar na da tsada, da cin lokaci da kuma ciwo, sannan akwai hadarin fuskantar matsaloli, amma mutane da dama sun gwammace su ɗauki kasadar.