Hikayata: Bidiyo bikin karrama gwarazan gasar 2020

Bayanan bidiyo, Hikayata: Bidiyo bikin karrama gwarazan gasar 2020

A ranar Juma'a ne aka yi bikin karrama gwarazan gasar Hikayata ta BBC Hausa ta mata zalla a Abuja, babban birnin Najeria.

Shekara ta biyar ke nan a jere da BBC take shirya gasar ga mata ta gajerun kagaggun labarai.

A bana wasu matasan 'yan mata uku ne suka yi zarra a gasar, wato Maryam Umar wacce ta yi ta daya ta kuma samu kyautar dala dubu biyu, kwatankwacin Naira miliyan daya.

Sai Surayya Zakari Yahaya da ta zo ta biyu ta kuma samu kyautar dala 1,000, kwatankwacin Naira 500,000, yayin da Rufaida Umar Ibrahim ta zo ta uku, ta kuma samu kyautar dala 500, kwatankwacin Naira 250,000.

Duk da yake takaitaccen taro aka yi bana, manyan baki sun samu halartar taron inda su ma suka jinjinawa gwarazana gasar ta bana.