Bidiyo: Mutanen da suka sa Najeriya ta zama cibiyar damfara ta intanet a duniya
Latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:
Kutse a shafukan intanet da zummar damfara na cikin manyan laifukan da aka fi aikatawa.
Hukumar tsaron Amurka ta FBI ta yi kiyasin cewa masu wannan ta'asa sun sa mutane sun yi asarar kusan $9bn a duk shekara.
A cewarta, Najeriya ce cibiyar masu kutse a intanet.
BBC ta tattauna da wani dan damfarar intanet da ke Najeriya domin sanin yadda suke gudanar da wannan damfara, da kuma ko suna yin nadama.