Matan da suka haɗa kuɗi don sayen mota saboda zuwa haihuwa asibiti a Jigawa
Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon
Matan wani kauye da ake kira Bardo a karamar hukumar Taura da ke jihar Jigawa a Najeriya sun yi karo-karon kudi inda suka sayo motar daukar mata masu juna-biyu zuwa asibiti domin haihuwa.
Matan sun samar da kudin ne inda aka sayi motar domin a rinka kai matan kauyen asibiti idan buƙatar hakan ta taso musamman ma haihuwa saboda matsalar sufuri da ake fuskanta a yankin.
Daga kauyen zuwa asibitin Jahun da ake kai matan haihuwa akwai tazarar kilomita 29, kuma kauyen ya kasance a lungu yake ga rashin kyawun hanya saboda ramuka.