Rasha da Belarus sun sa hannu kan yarjejeniyar haɗin kai

.

Asalin hoton, EPA

Shugaba Vladimir Putin na Rasha ya yi alƙwarin cewa ƙasarsa da Belarus za su haɗa kai domin yaƙi da duk wani na'ui na katsalandan da ƙasashen waje za su yi ƙoƙarin yi musu a harkokinsu na cikin gida.

Mista Putin din ya bayyana haka ne jim kaɗan bayan shi da Shugaban Belarus Alexander Lukashenko sun sa hannu a wata yarjejeniya da zata ƙara danƙon zumunci tsakanin ƙasashen biyu.

Yarjejeniyar ta ƙunshi abubuwa da dama da suka haɗa da haɗin kan ƙasashen biyu ta fannin tattalin arziki da kuma batun aikin soji da batun ƴan gudun hijira. Dama tun a baya ƙasashen na shiri da juna sai dai abotar da ke tsakani ta ƙara ƙarfi tun a bara bayan da Shugaban Belarus Alexander Lukashenko ya yi iƙirarin lashe zaɓen ƙasar wanda aka yi ta sukar ingancinsa.

A wani taro da aka yi ta intanet, Mista Lukashenko ya ce ƙasarsa na son abota ta ƙut da ƙut da Rasha.

"Haɗin kan ƙasashen biyu ne abu mafi muhimmanci ga ƴan Belarus. A yanzu mun haɗe kanmu wanda hakan zai bai wa ƴan ƙasar Rasha da Belarus ƴanci iri ɗaya da kuma ƙara ƙarfin tattalin arziki. Mun haɗa kanmu ta fannoni da dama kuma muna sa ran nan gaba za mu ƙara faɗaɗa lamuranmu."

Shi ma Shugaban Rasha Vladimir Putin ya ce akwai fannoni daban-daban da ƙasashen za su iya aiki kafaɗa da kafaɗa

"Abin takaici a fannoni da dama bayan rushewar Tarayyar Soviet, an bar mu a baya, ba mu amfani da damar da muke da ita tun ma a lokaci Tarayyar Soviet. Ina magana ne kan abubuwan more rayuwa da kuma harshen Rasha da muke magana da shi da ya haɗa kanmu kuma ya sa muke iya magana da juna cikin sauƙi."

A yanzu dai duk ƴan adawan Belarus sun bayyana cewa duk wata yarjejeniya da Mista Lukashenko zai saka wa hannu ba ta da amfani. Mista Putin dai na goyon bayan Mista Lukashenko ganin cewa ba a jituwa tsakanin aminin na sa da kuma Tarayyar Turai