Jam'iyyar Putin ta Rasha na fuskantar kalubale a zaben kananan hukumomi

Asalin hoton, EPA
Al'ummar Rasha, na tururuwar zuwa rumfunan zabe a yau, don jefa kuri'a a zaben kananan hukumomi da ake kallo a matsayin muhimmin gwaji ga jam'iyyar hadin kan kasar ta shugaba Vladmir Putin.
Masharhanta na ganin cewa jam'iyyar na rasa karfinta sannu a hankali, saboda durkushewar bangaren haraji da dokar nan ta biyan fansho mai cike da sarkakiya da karuwar cin hanci da rashawa.
Babban mai hamayya da shugaba Putin Alexei Navalny wanda yanzu haka ke farfadowa a asibiti, ya jima yana goyon bayan wadanda ke kalubalantar jam'iyyar shugaban a zabukan gwamnoni.
Rahotanni sun ce duk da yana ci gaba da farfadowar tawagarsa na ci gaba da kokarin rage tasirin jam'iyyar a mulkin kasar.
Yayin da ake zaben a lardunan kasar da dama suna kokarin bin salon yakin neman zaben Mista Navalny don goya baya ga 'yan takarar da ke da farin jinin kayar da na jam'iyyar Putin, a wasu wuraren da dama irin wadannan 'yan takara makusantan Mista Navalnyn ne.
Yadda aka sawa Navalny guba

Asalin hoton, Getty Images
Gwamnatin Jamus ta ce gubar Novichok aka sanya wa jagoran adawa na Rasha Alexei Navalny.
Ta ce wani gwaji da aka yi ya gano ''tabbas hakika'' gubar Novichok ce a jikinsa.
A watan da ya gabata ne aka garzaya da Mr Navalny birnin Berlin na Jamus don a yi masa magani bayan da ya fara rashin lafiya a yayin da yake tafiya a cikin jirgi zuwa yankin Siberia na kasar Rasha.
Tawagarsa ta ce guba aka sanya masa a bisa umarnin Shugaba Vladimir Putin, Amma Fadar Kremlin ta yi watsi da zargin.
Gwamnatin Jamus ta ce ta yi Allah-wadai da harin da babbar murya ta kuma yi kira ga Rasha da ta yi gaggawar yin bayani.
"Abun daga hankali ne cewa an sanya wa Alexei Navalny guba a Rasha,'' in ji ta.











