Wagner: Ana neman ɗan marigayi Gaddafi ruwa a jallo a kan alaƙarsa da sojojin haya na Rasha

Asalin hoton, Getty Images
Masu gabatar da ƙara a Libya sun bayar da sammacin kama Saif al-Islam Gaddafi, ɗan marigayi shugaban Libya Muammar Gaddafi, bisa zargin alaƙa da sojojin haya na Rasha.
Binciken da BBC ta yi ya bankaɗo alaƙar da ke tsakanin hare-haren mayakan kamfanin Wagner a Libya da laifukan yaƙi da aka aikata kan 'yan kasar.
Mayaƙan na Rasha sun fara bayyana ne a Libya a shekarar 2019 lokacin da suka hada kai da dakarun Janar Khalifa Haftar wajen kai hari kan gwamnatin da ke samun goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya a Tripoli babban birnin kasar.
Rikicin ya zo karshe bayan da bangarorin biyu suka amince su dakatar da bude wuta a watan Oktoba na 2020.
An fara gano mayakan kungiyar ta Wagner ne a shekarar 2014, lokacin da take goyon bayan 'yan a-ware masu goyon bayan Rasha a rikicin gabashin Ukraine.
Tun daga wancan lokacin ta shiga cikin wasu kasashe da suka hada da Siriya da Mozambique da Sudan da Jamhuriyar Afirka Ta Tsakiya.
Shin me yasa babu doka da oda a Libya?
Mai gabatar da kara Mohammed Gharouda ya ba da umarnin kama Saif al-Islam Gaddafi a cikin gida ga hukumomin tsaro na Libya a ranar 5 ga watan Agusta, amma an sanar da al'umma ne bayan da aka watsa binciken da BBC ta yi .
Wanene Saif al-Islam Gaddafi?
An dade ana zargin Saif al-IslamGaddafi da alaka da Rasha.
Kafin boren da ya faru a shekarar 2011, wasu sun yi ammanar cewa shi ne zai kawo sauyi a kasar ta Libya, wanda mahaifinsa Muammar ke mulkin tun shekarar 1969.
Sauran 'yan uwansa sun rasa rayukansu ko sun tsere daga kasar. Shi kuwa Saif al-Islam mayakan 'yan tawaye ne suka cafke shi a karshen shekarar 2011 inda suka wuce da shi garin Zintan da ke kudu maso yammacin Tripoli.
Mayakan sa-kai da ke tsare da shi sun sake shi bayan ya yi shekara 6 a hannunsu.
Fitaccen mai magana da harshen turancin Ingilishi wanda ya yi karatu a babbar Makarantar Tattalin Arziki ta London, an daɗe ana kallonsa a matsayin ɗaya daga cikin mutanen da ke da tasiri a ƙasar, kuma mai yiwuwa ya gaji mahaifinsa.
Sai dai zanga-zangar nuna rashin amincewa da gwamnatin kasar a shekarar 2011 ta sa Gaddafi ya shiga cikin masu murkushe masu zanga-zanga.

Asalin hoton, Reuters
A lokacin da ake tsare da shi, wata kotu a Tripoli ta yanke masa hukuncin kisa ba tare da ya gurfana a gabanta ba game da kisan masu zanga-zanga a shekarar 2011.
Kotun hukunta manyan laifuka ta duniya (ICC) tana kuma neman sa bisa laifukan cin zarafin bil adama da aka aikata a lokacin da aka murkushe masu zanga-zangar.
Duk da cewa an shafe tsawon shekaru ba a gan shi a bainar jama'a ba, Gaddafi ya yi hira da jaridar New York Times a watan Yuli, inda ya yi magana kan shirinsa na komawa siyasa.
A cewar majiyoyi a Tripoli, akwai yiwuwar har yanzu yana buya a Zintan.
Alakar da ke tsakanin Seif da Rasha
A lokacin da ake hada shirin na BBC a kan ayyukan kungiyar Wagner a Libya, BBC ta gana da jami'an leken asirin Libya wadanda suka yi magana kan alakar da ke tsakanin Gaddafi da Moscow tare da bayyana shi a matsayin "dan takarar da Rasha ta fi so ya mallaki Libya".
Jami'an leken asirin na binciken Maxim Shugaley, dan kasar Rasha wanda aka kama a Tripoli a watan Mayun 2019 bisa zargin leken asiri.
Ana zarginsa da ya yi wa Yevgeny Prigozhin aiki, wanda hamshaƙin ɗan kasuwa ne da ke da kusanci da Shugaba Vladimir Putin, a matsayin wani ɓangare na yaƙin neman zaɓe da aka tsara don kafa Gaddafi a matsayin mai mulkin Libya a lokacin da Janar Haftar ya kai hari kan babban birnin.
An saki Mr Shugaley, tare da mai yi masa tafinta wanda aka kama tare da shi a karshen 2020.
Rahotanni sun ce Mista Shugaley da kansa ya gana da Gaddafi lokacin yana Libya. Har ma Rasha ta shirya fina-finai guda biyu kan kamun Mista Shugaley, wanda aka buga a YouTube kuma aka nuna Gaddafi a matsayin "mai ceton Libya" da Mr Shugaley a matsayin "gwarzon Rasha".
Wani jami'in leken asirin Libya ya shaida wa BBC cewa: "Da komai ya tafi daidai kamar yadda Rasha ta so, to da mun ga Saif [al-Islam] Gaddafi yana ba da jawabin nasararsa a shahararren dandalin shahidai na Tripoli."











