Amurka ta ƙaƙaba wa Rasha takunkumi kan Navalny

Asalin hoton, Getty Images
Amurka ta kakaba wa wasu 'yan kasar Rasha da wasu hukumomin kasar takunkumi saboda abn da ta kira yunkurin Rashar na hallaka jagoran 'yan adawa Alexei Navalny.
Manyan jami'an hukumomin leken asiri na Amurka sun ce suna da hujjoji masu kwari cewa an nemi kashe Mista Navalny ne da guba a watan Agustan bara.
Wannan ne matakin farko da gwamnatin Joe Biden ta dauka na mayar da martani kan abin da ta kira mugunyar halayyar Rasha.
Jami'an gwamnatin Amurka sun ce za a dauki matakin kakaba takunkmi kan wasu manyan jami'an gwamnatin Rasha su bakwai saboda hannun da su ke da shi a harin gubar da aka kai kan Alexie Navalny, da kuma tsare shin da aka yi daga baya.
Amurkar za ta kuma hana wasu hukumomin Rasha 14 fitar da wasu kayayyaki saboda ayyukan da su ke yi na hada sinadarai irin wanda aka yi amfani da shi kan Mista Navalny mai hallaka mutum cikin kankanin lokaci ba tare da a gane sanadin mutuwar ba.
Amurka ta dauki wadannan matakan ne tare da hadin gwuiar Tarayyar Turai.

Asalin hoton, Reuters
Jami'an sun kuma ce matakan da Amurkar ke dauka za su karfafa wadanda kasashen na Turai su ka dauka ne kan kasar tuntuni, saboda tshon shugaba Donald Trump ya ki daukan matakin ladabtarwa kan Rasha saboda harin gubar da ta kai wa Alexie Navalny.
Ban da wadannan jerin matakan, akwai wasu kuma guda uku da Amurk ke dubawa, kuma ta sanar cewa za ta dauki wasu karin matakai nan ba da jimawa ba.
Sauran wuraren sun hada da katsalandan kan ayyukan zaben Amurka da Rasha ke yi, da hare-haren da ta ke kai wa kan komfutocin Amurkar da kuma tuhumar da ta ke yi cewa gwamnatin ta Moscow ta rika biya 'yan Taliban kudade domin kashe sojojin Amurka a Aghanistan.











