Mutanen karkara a Afghanistan sun rungumi mulkin Taliban

Goljuma (dama) ta yabi Taliban: "Mata iri na ba kamar matan Kabul bane"
Bayanan hoto, Goljuma (dama) ta yabi Taliban: "Mata iri na ba kamar matan Kabul bane"
    • Marubuci, Daga Jeremy Bowen
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Editan BBC a Gabas Ta Tsakiya

Kwalliyar cikin dakin an yi ta ne da wani jan bulo kanana da aka yi da tabo mai ban sha'awa.

Wani mutum da ake kira Shamsullah da ke jaye da wani yaro ya fito inda ya yi maraba da bakinsa.

A kasan dakin kuma kafet ne shimfida a ko'ina, ga wasu tika-tikan kujeru, an kuma makala ababen kawata daki a bango.

Shi ma dakin dafa abincin an kawata shi sosai da kayan cin abinci. Amma duk da haka masu gidan talakawa ne, kuma duka abin da suka mallaka an sace shi ko an lalata shi a tsawon shekaru 20 da aka yi na yaki.

Amma dai ko ba komai suna da inda suke fake wa daga rana da kura idan ta taso. Haka ma gidan na zagaye da katanga da aka yi da tabo.

Shamsulla ya shigo da mahaifiyarsa Goljuma wadda ya ce shekarunta 65. Jikinta duka a rufe yake da daga sama har kasa, illa dai ana iya ganin idanunta.

Shamsullah shi ne dan autanta kuma shekarunsa 24, amma idan ka gan shi za ka kara masa shekaru 10 akai.

Dan Goljuma na farko Zia Ul Huq ya mutu shekaru 11 da suka wuce, wanda mamba ne a kungiyar Taliban. '' Da na ya shiga Taliban ne bayan da ya fahimci cewa Amurka na son wargaza musulunci da Afghanistan, In ji ta.

Sauran ya'yanta uku sun mutu ne a shekarar 2014. An kashe Quadratallah a wani hari ta sama. Aka kuma kama Hayatullah da Aminullah aka tursasa musu shiga aikin soji a cewar kanensu Shamsullah, inda ya ce a wurin aikin suka mutu.

A matsayin da daya tilo da ya rage a gidansu, Shamsullah ya ce Allah ya bar shi ne don ya kula da gidannasu.

Shamsullah ya ce wasu daga cikin abubuwan da yake yi sun hada da daukar nauyin matar da yayansa ya mutu ya bari.

''Ina kewar 'yan uwana. Yayana ya auri matar babban yayanmu bayan ya mutu. Shi kuma wanda ke bi masa ya sake auren ta bayan an kashe shi. Shi kuma bayan an kashe shi wanda na ke bi ya sake auren ta. Bayan mutuwarsa ni kuma na aure ta.''

A shekarar 2010 Shugaban Amurka Barack Obama ya zabi Marjah a matsayin karin yankunan da za sake kitsa hare hare a Afghanistan.

Dalili shi ne a ganinsu kara jami'an tsaro zai taimakawa hadakar kasashen da ke yaki a lokacin da suka hada da gwamnatin Afghanistan da Amurka da Burtaniya.

''Idan muka matse Taliban har suka fice za a samu ci gaba mai kyau: makarantu masu kyau da asibitoci da ma kasuwanni,'' in ji wata sanarwa da sojojin Amurka suka fitar a lokacin.

Sai dai yankin Marjah da ke zagaye da gonakin auduga ya zame wa sojojin kasashen waje wani mummunan mafarki a karon-battar da suka rika yi da mayakan Taliban.

Watanni uku da fara yaki yankin kwamandan sojojin Amurka Stanley McChrystal ya kira Marjah da ''gyambon da ke jini,'' don an shafe shekaru 10 a na gumurzu a nan.

Goljuma ba ta yadda da manufar shugbannin kasashen waje ba game da kasarta ba cewa za su kawo mata sauyi mai kyau. ''ban fahimci manufarsu ba. Sun wargaza mana kasa.'' Inji ta.

''Jama'a da dama sun sha wahala. Sun kashe mana mazaje da yayye da 'ya'ya. Kuma ni ina son Taliban don suna son musulunci. Mata irina a nan ba kamar matan da ke Kabul su ke ba.''

Ta ce kafin Taliban ta kwace mulki kowa tsoronsu yake yi. Amma yanzu hankalin kowa ya kwanta.

Taliban soldiers in Lashkar Gah
Bayanan hoto, Mayakan Taliban a Lashkar Gah inda kungiyar ta kwace ikon Kabul a ranar 15 ga Agusta

Sai dai abun tambaya a nan shi ne shin Goljuma ra'ayinta ne ta ke fadi ko kuma abin da ake so ta fadi?

A lokacin da zamu tafi wurin tattaunawa da ita Taliban ta hada mu da ma'aikacin ofishinta na sadarwa da kuma sojanta a matsayin sharadi na tattaunawar.

Ba don haka ba da wata kila mun samu wasu bayanai marar dadi da ke damun al'umma game da mulkin Taliban.

Amma na yadda da nuna damuwa da Goljuma ta yi na lalata harkar noma da sojojin kasashen waje suka yi da kuma kisan 'ya'yanta hudu.

A shekarar 2001 jim kadan bayan hare-haren 9/11 a birnin New York, kasashen Amurka da Birtaniya da kawayensu sun kutsa Afghanistan da nufin murkushe al-Qaeda da kuma hukunta Taliban da ta ba su mafaka.

Sai dai abin da ya biyo baya ne ke da daure kai. An dai kasa samun samun nasara a yakin, an kuma kasa inganta rayuwar Afganistawa.

Ci gaba kamar dimokradiyya ne, ba za a iya samun nasarar su da bakin bindiga ba.

Kasashen Yamma sun samu nasarori ta wasu hanyoyi. Sannan mazauna birane maza da mata sun samu ilimi da sauyin rayuwa.

Amma kuma nasarori ne da ba su kai ga talakawa ba da ke cikin lunguna kamar iyalan Goljuma.

line

A lokacin ta Taliban ta fara kwace mulki a 1996 sun yi amfani da karfi wurin tursasawa al'umma addini da al'ada.

Amma a yanzu matasa da dama a Afghanistan sun yi kanana su iya tuna mulkin da aka yi kafin harin 9/11 da kuma shigar kasashen waje kasar.

A Lashkar Gah da ganin kamarorin BBC matasa suka rika fito wayoyinsu suna daukar mu hoto har suna daukar hotunan dauki da kanka na selfie tare da mu.

Kuma data na da araha a nan. Jami'in Taliban da ke rakiyarmu ya kalli Sashen Pashto na BBC a wayarsa.

Sun shedi cewa duniya ta waye ba kamar a shekarun 1990 ba, lokacin da Taliban ta hana daukar hoto kwata-kwata.

Mayakan kungiyar kansu sun girma ne lokacin da duniya ta waye kuma suna da masaniya kan hakan.

Saboda haka Taliban za ta tursasa sojojinta ne kafin ma ta zo kan fararen hula na su daina amfani da wayoyin zamani da intanet da sauran wayewar da suka dandana?

A wannan karon kam watakila abu ne mai matukar wahala kungiyar ta karya ba gaba kamar yadda ta yi a baya.

Dole ta kawar da ido ga wasu abubuwan da zamani ya riga ya shiga gabanta a kansu.