Afghanistan: Muhawara ta ɓarke tsakanin ƙungiyoyin 'Jihadi na duniya' kan makomar Taliban

Asalin hoton, AFP
Ƙungiyoyin da ke ikirarin jihadi a duniya suna ta taya Taliban murnar ƙwace iko da ƙasar Afghanistan, bayan da ƙungiyar ta kammala karɓar birnin Kabul.
Wani babba a ƙungiyar al-Qaeda, Warith al-Qassam, a ranar Lahadi ya ce "A bana zagayowar ranar da aka kai harin 9/11 na Amurka zai zama daban, saboda nasarar da aka yi ta ƙwato Afghanistan."
Ƙungiyoyin da ke ikirarin jihadin sun yi ta yaɗa hotunan manyan kwamandojin Taliban a shafukan sada zumunta, a lokacin da suka kutsa fadar gwamnati a Kabul.
Sai dai kuma a wani lamarin na daban, ƙungiyoyin na ta tafka muhawara a shafin Telegram kan makomar Taliban ɗin, musamman ganin cewa ta nuna alamun ƙulla alaƙar difilomasiyya da wasu ƙasashen duniya da kuma alƙawarin ba za ta bari a mayar da Afghanistan wajen kai hare-hare kan ƙasashen Yamma ba.
Sannan suna ta yaɗa duk wani labari da ya fito kan abin da ya shafi nasarar Taliban ɗin a manhajar Telegram.
Wasu magoya bayan al-Qaeda suna ikirarin cewa Musulmai a fadin duniya na ta raba alewa da kuma gabatar da wasu al'adu "don murnar nasarar Taliban."
Warith al-Qassam ya yaɗa jerin bidiyo da ke nuna yadda suke murnar.
Daya daga cikinsu na masu ta da ƙayar baya ne a yankin da suke iko da shi a Idlib a arewa maso yammacin Syria, da ke nuna lasifikokin da aka daddasa a kan tituna ana kiran "Allahu-Akbar... da kuma Godiya ta tabbata ga Allah". Amma wasu manyan titunan kuma babu wani abu da yake faruwa.
Wani bidiyon kuma da aka ce a Yemen aka ɗauka ya nuna yadda ake wasan tartsatsin wuta, sai kuma muryar wani mutum da aka ji ba tare da an ga fuskarsa ba yana cewa Ƙungiyar Ansar al-Sharia al-Qaeda da ke Yemen - na taya ƴan uwansu na Taliban murna.
'Ana ta raba alewa don murna'
A can Gaza kuma wata ƙungiyar ta Jaysh al-Umma ce aka ga hotunan mayaƙanta suna rarraba wa mutane alewa a kan titi.
Al-Qassam ya kuma yi ikirarin cewa a garin Kidal na Mali ma an yi ta murna, inda wasu suka dinga yaɗa taswirar Afghanistan da ke nuna yadda Taliban ta mamaye.
Ita ma kungiyar masu ikirarin Jihadi ta al-Shabab da ke Somaliya ta yi murnar nasarar da Taliban ta samu na kwace iko da Afghanistan.
Wasu kafafen yada labarai masu alaka da ita suka wallafa sako kamar haka: "Allah Mai Girma: sojonin Musulunci sun kwace iko da Kabul.
"Ana ta shagulgulan murna a kasar inda ake tayar da tutocin kungiyar Taliban da na Musulunci," in ji kafar Calamada.
Ta ce Taliban ta yi nasara a kan shugabannin Afghanistan da dubun-dubatar dakatun kasashen waje bayan shafe shekara ana fafutuka.
Al-Shabab kawar al-Qaeda ce kuma tun tsakiyar shekarun 2000 take fada da gwamnatin Somaliya da kungiyar Tarayyar Afirka ta yarda da ita.
Manyan jami'ai a ƙungiyar masu jihadi ta Hayat Tahrir al-Sham (HTS), a Syria, da take da iko da yankin Idlib, ta wallafa nata saƙon taya murnar ga Taliban a Telegram, tana mai bayyana ta a matsayin abar koyi.
Jami'an HTS Abu Mariya al-Qahtani da Muzhir al-Ways dukkanasu sun yaba wa Taliban.
Wasu masu tsattsaurar aƙida daga cikin magoya bayan al-Qaeda sun shawarci ƴan uwansu da su ci gaba da alfahari da ayyukan Taliban a yanzu don kar su kashe karsashin nasarar da aka samu da wasu-wasin da ke zuciyoyinsu.
Daga cikin saƙe-saƙen da wasu masu ikirarin jihadin ke yi har da saƙon alaƙar diflomasiyya mai kyau da Taliban ɗin ke aike wa maƙwabtanta, da kuma alwashin da ta sha cewa ba za ta bari a yi amfani da Afghanistan wajen mayar da ita sansanin kai hare-hare kan ƙasashen yamma ba.
'Sanya damuwa'
Wannan ya sanya damuwa a zuƙatan masu tsattsauran ra'ayi daga cikinsu, ciki har da mayaƙan Taliban, kan cewa ba lallai ƙungiyar ta tabbatar da cikakkiyar Shari'ar Musulunci ba a Afghanistan.
Amma wannan muhawara ta tsaya ne kawai a ƙuryar shafin Telegram, wanda murnar da ake yi ta shafe ta.
Sannan yawanci 'yan ƙungiyar IS ne suke tayar da kokwanton, wacce dama abokiyar adawar Taliban ce.
Wani fitaccen mai goyon bayan al-Qaeda, Shibl Osama, ya rubuta cewa masu goyon bayan Taliban za su gabatar da shawarwari da nuna mata kura-kuranta a inda ta gaza da zuciya ɗaya.
Ya jaddada cewa Taliban ba ita ce ma'aunin Tauhidi ba.
Sannan wani magoyin bayan al-Qaeda Jallad al-Murji'ah, ya roƙi mutane kar su bar kokwanton nan ya daƙushe kaifin murnarsu. "Yanzu ba lokaci ne na fadar abin da ke rayukanmu ba na murna ne.
Su kuwa magoya bayan ƙungiyar IS da take ayyukanta a yankin Khorasan a Afghanistan a wani lamari mai ban mamaki suna sukar Taliban.
Babbar hujjar da suka bayar ita ce Taliban karen farautar Amurka ce kuma Amurka ta miƙa wa masu ta da ƙayar bayan Afghanistan ne bayan cimma yarjejeniyar siyasa, wanda a idonsu hakan ya rage ƙimar Taliban.
Wasu ma na cewa idan ba haka ba me zai sa Amurka kwashe ƴan ƙasarta cikin lumana a lokacin da Taliban ɗin suka dakatar da kutsensu cikin Kabul.
Wasu kuwa na alaƙanta lamarin da abin da ya faru a Iraƙi lokacin da Amurka ta damƙa wa Shi'a wuƙa da nama.

Magoya bayan IS na ikirarin a yanzu Taliban "za ta yi mummunan aiki" ga Amurkawa a yankin, da suka haɗa da yaƙar mayaƙan IS.
Sai dai wani babban ɗan IS Sawt al-Zarqawi ya ga wata gwaggwaɓar dama ga IS. Ya ce yanayin da ake ciki a Afghanistan a yau ya yi wa IS daɗi don a yanzu maƙiyi ɗaya za ta yi faɗa da shi, wato Taliban.
Kafin wannan lokacin IS ta sha kai wa Taliban hari da kuma dakarun Afghanistan da na ƙasashen waje.
Ya ce a yanzu babu Amurkan da za ta taimaka wa Taliban.











