Abduljabbar Kabara: Abin da wasiƙar wasu iyalan Sheikh Nasiru ga Buhari ta ƙunsa

Asalin hoton, Kabara Family
Wasu daga cikin iyalan tsohon shugaban ɗariƙar Ƙadiriyya ta Afirka marigayi Sheikh Nasiru Kabara sun kai ƙarar wasu malaman jihar Kano da ke arewa maso yammacin Najeriya wajen Shugaba Muhammadu Buhari, kan lamarin da ya shafi ɗan uwansu Sheikh Abduljabbar.
Hakan na ƙunshe ne a wata wasiƙa da suka rubuta wa shugaban ƙasar mai ɗauke da sa hannun ɗaya daga cikinsu Sheikh Sidi Musal Qasuyuni Nasir Kabara.
A wasiƙar dai, 'ƴan uwan 19 sun buƙaci shugaban ƙasar da ya yi ƙoƙarin dakatar da duk wata "muzgunawa" da "rashin adalcin" da suka ce an shirya yi wa ɗan uwan nasu.
Sai dai a jerin sunayen ƴaƴan da suka rubuta wasiƙar babu sunan babban ɗan Sheikh Nasirun, wanda shi ne shugaban Ƙadiriyyar a yanzu, wato Sheikh Ƙaribullah Kabara.
Kazalika sun kuma buƙaci Shugaba Buharin ya saka baki a saki Sheikh Abduljabbar, wanda a yanzu haka yake tsare bisa tuhumarsa da ake yi da yin ɓatanci ga Manzon Allah S.A.W.
A ranar 15 ga watan Yulin da ya gabata ne rundunar .ƴan sandan jihar Kano ta kama fitaccen malamin addinin Musuluncin.
Daga baya kuma an mayar da shi gidan yari har zuwa lokacin da za a gama sauraren shari'ar tasa.


Me wasiƙar ta ƙunsa?
"Tare da dukkan girmamawa da ƙanƙan da kai gare ka ranka ya daɗe, mu ƴaƴan Dr Sheikh Muhammad Nasir Kabara, muna so mu gabatar da ƙorafinmu a gare ka, a matsayinka na uban dukkan ƴan Najeriya, wanda ba zai taɓa goyon bayan rashin adalci ba a kowane yanayi.
"Muna amfani da wannan kafar ce don gabatar da ƙorafinmu a wajenka, ka shiga cikin lamarin nan da ya shafi ɗan uwanmu na jini Sheikh Abduljabbar Nasir Kabara, wanda wasu malamai a Kano ke zarginsa bisa rashin adalci.
"Malaman na zarginsa ne bisa son kai da wasu bambance-bambance marasa tushe da ke tsakaninsu, don cimma manufarsu a kansa, inda su waɗannan malaman da gangan suka sassauya wasu wa'azuzzuka na ɗan uwanmu da kuma zarginsa da yin kalaman ɓatanci ga Annabi Muhammad SAW.
"Sun yi hakan ne da niyyar lalata ƙimarsa a idon duniya da kuma son ganin sun kawar da shi daga doron ƙasa.
"Duk waɗannan abubuwa da suk yi na son rai ne, kawai saboda suna da bambancin aƙidu da kuma wani faɗansu can da shi ɗan uwanmu Sheikh Adbuljabbar Kabara.
"Ya mai girma shugaban ƙasa, muna tabbatar maka da cewa dukkan zarge-zargen da wadannan malamai ke yi ƙage ne kan ɗan uwanmu Sheikh Adbuljabbar Kabara saboda wani ɓoyayyen abu da suke son cimma.
"A haƙiƙanin gaskiya, abin da suke ƙoƙarin maƙalawa ɗan uwanmu abu ne da tuntuni yake ƙoƙarin kawar da su.
"Muna tabbatar wa shugaban ƙasa cewa mu ƴaƴan Sheikh Nasir Kabara, duba da koyarwar da muka samu daga marigayi mahaifinmu, na so da ƙaunar Manzon Allah SAW, ba za mu taɓa goyon bayan wani mutum da zai taɓa janibin Annabi ba.
"Idan kuwa hakan ta faru, to za mu zama na farko wajen ƙalubalantar ko ma waye.
"Kazalika duk wanda ya san ɗan uwanmu Sheikh Abduljabbar ya san shi a gaba-gaba wajen kare martabar Manzon Allah SAW da ƙoƙarin cusa soyayyarsa a zuƙatan al'ummar Musulmai da nuna musu girmansa.
"Cikin girmamawa ranka ya dade muna son ka gaggauta shiga lamarin nan tare da dakatar da muzgunawar da ake yi wa ɗan uwanmu da rashin adalcin da wasu mutane ke kitsa masa ba tare da hujja ba.
"A ƙarshe muna maka fatan alheri da lafiya da nasara.
"Muna godiya a yayin da muke sa ran za ka duba batun.

Sunayen waɗanda suka rubuta wasiƙar
Cikin ƴaƴan Sheikh Nasir Kabara 33 da suke raye, 19 ne suke rattaba hannu a kan wasiƙar wacce aka rubuta sunayensu, maza biyar, mata 14.
- Sheikh Ibrahim Mu'azzam Sheikh Nasir Kabara
- Sheikh Sidi Musal Qasuyuni Sheikh Nasir Kabara
- Malam Askiya Sheikh Nasir Kabara
- Malam Yahya Sheikh Nasir Kabara
- Malam Aburumana Sheikh Nasir Kabara
- Sayyidah Saratu Sheikh Nasir Kabara
- Sayyidah Nafisatu Sheikh Nasir Kabara
- Sayyidah Khudriyya Sheikh Nasir Kabara
- Sayyidah Zam'atu Sheikh Nasir Kabara
- Sayyidah Saffanatu Sheikh Nasir Kabara
- Sayyidah Aishatu Mannubiyyah Sheikh Nasir Kabara
- Sayyidah Ummu Aimanal Habashiyyah Sheikh Nasir Kabara
- Sayyidah Khadijatul Habashiyya Sheikh Nasir Kabara
- Sayyidah Huza'iyyah Sheikh Nasir Kabara
- Sayyidah Jamila Sheikh Nasir Kabara
- Sayyidah Bulkisa Sheikh Nasir Kabara
- Sayyidah Rukayyah Sheikh Nasir Kabara
- Sayyidah Hansa'u Sheikh Nasir Kabara
- Sayyidah Umamatu Sheikh Nasir Kabara.

Matashiya

A ranar Asabar 10 ga watan Yuli ne aka gudanar da muƙabala tsakanin Malamin da sauran Malaman Jihar Kano bisa bukatarsa ta ƙalubalantarsu kan da'awarsa wadda suke ganin ba daidai yake ba.
An yi wa Malamin tambayoyi da dama amma ya gaza amsa wa, inda yake ta nanata cewa mintinan da ake ba shi domin ya yi bayanin da'awarsa sun yi masa kaɗan.
Haka dai aka kammala wannan muƙabala ba tare da ya yi bayanin da ya gamsar da malaman da ya nemi zaman muƙabalar da su ba.
Daga baya ya fitar da wani bidiyo wanda a ciki ya nemi afuwar mabiyansa da duk wanda abin ya bata masa yana cewa duk abin da yake yi yana yin sa ne min kare mutuncin ma'aiki.
Sai dai a ranar a ranar 15 ga watan Yulin da ya gabata ne rundunar ƴan sandan jihar Kano ta kama fitaccen malamin addinin Musuluncin.
Kazalika a ranar 28 ga watan Yulin wata Kotun Shari'ar Musulunci da ke birnin Kanon ta soma shari'ar malamin, amma an ɗage shari'ar zuwa ranar 18 ga watan Agustan 2021.












