Sheikh Abduljabbar Kabara: Kotu ta mayar da Malamin kurkuku

Wata Kotun Shari'ar Musulunci da ke birnin Kano a arewacin Najeriya tana can ta soma shari'ar malamin nan na jihar Sheikh Abduljabbar Kabara.
Jami'an gidan gyaran hali ne suka kai malamin kotu da safiyar Laraba domin a soma shari'arsa a kotun wadda mai shari'a Ibrahim Sarki Yola yake jagoranta.
Ranar Juma'a 16 ga watan Yuli ne gwamnatin jihar Kano ta gurfanar da malamin a gaban kotu bisa zargin ɓatanci ga addini da kuma tunzura jama'a, zargin da ya sha musantawa.
Wakilin BBC da yanzu haka yake kotun ta Kofar Kudu a birnin Kano ya ce da alama Sheikh Abduljabbar yana cikin koshin lafiya sai dai ya dan rame.
Alkali Sarki Yola ya bayar da umarnin a shiga da Sheikh Albduljabbar cikin akwatin da wanda ake kara ke tsayawa.
Aisha Mahmud ita ce ke jagorantar lauyoyin gwamnatin Kano.
A bangaren Sheikh Abduljabbar, lauyoyinsa sun hada da Sale Mohammad Bakaro, da Yahuza mohd Nura da Bashir Sabi'u, RS Abdullahi, Y I Abubakar, Zaubairu Abubakar, Ya'u Abdullahi Umar, B S Ahmad, da kuma Umar Usman.
Yadda aka yi zaman kotun na yau Laraba
Alkali Sarki Yola: A ranar farko da aka gabatar da kara, an karnata wa wanda ake karar laifin da ake tuhumarsa da aikatawa, amma ya musanta aikata laifin, ya tambayi shaidu, lauyoyin gwamnati suka ce suna da shaidu bayan an tambaye su ko suna da shaidu.
Alkali Sarki Yola ya tambayi lauyoyin gwamnati shin sun zo da shaidun da suka ce suna da su?
Lauya Aisha: Mun samu dukkan bayanin shari'ar da ake kuma muna neman kotu ta ba mu wata rana domin gabatar mata da shaidu. Hakan zai ba mu dama mu hada bayananmu tare da tuhumar da muke yi wa Sheikh Abduljabbar.
Wannan shi ne rokon da muke yi wa kotu.
Daga nan sai Alkali Sarki Yola ya bai wa lauyan Sheikh Abduljabbar damar ya yi magana.
Lauya Sale Bakaro: An kawo wanda ake kara kwana 12 da suka gabata, amma abin bakin ciki ne masu gabatar da kara ba su shirya tuhumar da suke magana ba, wannan ya nuna cewar so suke su kawo tsaiko, ba so suke a yi shari'ar ba.
Wanda ake kara yana tsare a gidan yari bisa umarnin kotu, wannan shine abin da muke jayayya a kai game da bayanin mai gabatar da kara.
Lauyan ya ce akwai ka'idoji da ake bi wajen daukaka kara ba bayan kwashe tsawon kwanaki 12, yana mai cewa babban abin bukata shi ne a yi wa kowa adalci.Lauya Bakaro ya kara da cewa: Ina ishara ga suratul Hadid, Aya ta 20 inda Allah (SWT) yake cewar dalilin saukar da Alkur'ani shine domin a tsayar da adalci a tsakanin mutane.Idan sun ce basu da shaida babu yadda suka iya idan har kotu zata ɗaga wannan shari'a su kawo dukkan shaidun da za su gabatar a gabanta.
Lauyar gwamnati Aisha ta so ta yi tsokaci, amma Alkali ya ce ta saurara sai lokacin ta ya zo, yana mai cewa zai yi wa kowa adalci ta hanyar jin ta bakin kowa.
Daga nan lauyan Sheikh Abduljabbar ya bukaci lauyoyin gwamnati su kawo musu sunaye da hujjojinsu, da kayan nuni da adireshin da takaitaccen jawabai na shaidunsu da kwafi bayanan wanda ake karar ya yi a wajen 'yan sanda.

Kazalika sun bukaci a kawo rahoto - na murya, ko bidiyo da hoto ko wata takarda da za su yi amfani da ita a gaban wannan kotu kafin ranar da za a fara sauraren shaidu.
Lauya Aisha: Mun saurari jawabansa, kuma bayanansa azarbabi ne. Mun nemi kotu ta ɗaga shari'ar ne domin mu kawo tuhumar da muke yi masa.
Ai chaji ya kunshi dukkan wani bayani da muke bukata. Lauyan wanda ake kara ba shi ne zai fada mana yadda za mu tsara kararmu ba.
Kuma muna rokon kotu ta ba mu 25 ga watan Agusta, 2021, domin a ci gaba da shari'a.
Lauya Sale Bakaro:Na gamsu da bayanan da lauyar gwamnati ta yi.
Bayan jin bangarorin biyu game da ranar da ya kamata a ci gaba da zaman kotun, alkalin ya yanke hukunci kamar haka:
Alkali Ibrahim Sarki Yola: An ɗageshari'ar Sheikh Abduljabbar zuwa mako uku. Wato za a koma kotu ranar 18 ga watan Agustan 2021.
Daga nan ya bayar da umarni a koma da malamin gidan yari har sai ranar da za a ci gaba da sauraren kara.











