Sheikh Abduljabbar ya nemi afuwa cewa ba a 'fahimce ni ba'

Bayanan sautiSheikh Abduljabbar ya nemi afuwa, ya janye kalamansa kan Manzon Allah

Latsa hoton sama ku saurari muryar Sheikh Abduljabbar karo na biyu

Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara ya nemi afuwa tare da janye kalamansa game da Annabi Muhammadu SAW.

Cikin wani sauti karo na biyu da ya aike wa BBC Hausa ranar Lahadi, malamin ya ce yana fatan "hakan ya zama silar gafara da rahama da jin ƙai gare ni".

"Waɗannan maganganu da suka fito daga bakina suka jawo ce-ce-ku-ce game da Ma'aiki SAW, na janye su na kuma janye su."

Wannan na zuwa ne 'yan awanni bayan sautin farko da ya fitar a Lahadin yana neman afuwar waɗanda suka fahimci cewa shi ne ya ƙiƙiiri kalaman ɓatanci ga Annabi da ake zarginsa da yi.

A cikin saƙon na farko ya ce: "Idan har waɗannan kalamai daga ni suke, ƙirƙirarsu na yi, babu su a litattafai to lallai ya isa babban laifi da ya wajaba a gare ni na gaggauta tuba".

"Amma idan ba daga ni ba ne, daga cikin waɗancan litattafai ne, to wannan kuma ya zama wani abu daban. Sai mu yi roƙon Allah ya haska wa al'umma su tashi tsaye mu taimaki addininmu, mu fitar da hadisan ƙarya daga ciki domin gudun kar a rusa mana addinin da su."

BBC Hausa ta fahimci cewa shehin malamin ya nemi afuwar ce bayan wasu ɗalibansa sun nemi ya yi hakan.

Ranar Asabar ne gwamnatin Jihar Kano ta shirya muƙabala tsakanin Abduljabbar da wasu malamai a jihar domin tafka muhawara game da kalaman nasa.

Sai dai malamin ya ce bai gamsu da ita ba, yana mai cewa "ni ba zan kira ta muƙabala ba saboda ba a faɗa mani tsarin ba kafin na zo wurin", sannan ya ce ba a ba shi isasshen lokaci ba.

Presentational grey line

Afuwar wa Abduljabbar ya nema a karon farko?

Bayanan sautiSheikh Abduljabbar ya nemi afuwa cewa ba a 'fahimce ni ba'

Cikin hirar da ya yi da BBC jim kaɗan bayan ya nemi afuwar a karon farko, Abduljabbar ya jaddada cewa yana neman afuwar mutanen da suka fahinci cewa shi ne ya ƙirƙiri kalaman ɓatanci ga Annabi saboda kukan rashin isasshen lokaci da ya dinga yi a lokacin muƙabala.

Ya ce: "Gaskiyar lamari shi ne, sakamakon zaman jiya da aka yi wanda aka takura lokaci da yawa...ba zai yiwu a fitar da irin wannan mummunan al'amari da nake yaƙi da shi ba a minti 10 ko 20, kuma na roƙa [a ƙara] amma ban samu hakan ba.

"Da na ce babu lokaci sai suka tafi a kan cewa e lallai maganar babu ita a hadisai ni ne na yi.

"Idan har wasu sun ɗauka miyagun maganganu irin waɗannan da ake taɓa fiyayyen halitta - waɗanda nake yaƙin fahimtar da al'umma cewa hadisai ne jabu - kuma wasu suke zaton cewa ni na yi, to ya wajaba na nemi afuwarsu bisa wannan zato da suke yi na cewa maganata ce.

"In har tawa ce kamar yadda suka ɗauka, kafin afuwarsu afuwar Allah da mazonsa nake nema."