An kammala mukabala
Nan za mu dakatar da kawo bayanai da rahotanni kai tsaye kan mukabalar da gwamnatin Kano ta shirya tsakanin Sheikh Abduljabbar Nasir Kabara da kuma malaman Kano
Wannan shafin na kawo maku bayanai kai tsaye daga zauren muƙabala da gwamnatin Kano ta shirya tsakanin Malam Abduljabbar da malaman Kano
Awwal Ahmad Janyau
Nan za mu dakatar da kawo bayanai da rahotanni kai tsaye kan mukabalar da gwamnatin Kano ta shirya tsakanin Sheikh Abduljabbar Nasir Kabara da kuma malaman Kano
Sheikh Abduljabbar ya ce bai gamsu da mukabalar da aka yi ba tsakaninsu da malaman Kano.
Ya ce ba a sanar da shi ba game da tsarin muƙabalar kuma ba a ba shi lokaci isasshe ba.
Ya ce ba zai nemi gafara ba kamar yadda malaman da suka fafata da shi suka nema domin a cewar Abduljabbar yana kan hujjojinsa.
Amma ya ce a shirye yake ya halarci wata muƙabalar idan har gwamnatin Kano ta amince ta sake shiryawa.
Malamai hudu ne daga ɓangaren Izala da Kadiriyya da Tijjaniya suka fafata da Abduljabbar a ranar Asabar.
Alkalin muƙabalar a tsakanin Malam Abduljabbar da malaman Kano ya ce Abduljabbar ya kasa amsa dukkanin tambayoyin aka yi masa.
Alƙalin muƙabalar Farfesa Salisu Shehu shugaban cibiyar addinin Islama da tattaunawa tsakanin addininai ta Jami'ar Bayero ya ce "bisa muƙabalar da aka yi Abduljabbar ya cakuɗa bayanasa, kuma wasunsu ba a kan doron ilimin hadisi yake gina su ba."
"Na yanke hukunci Malam Abduljabbar bai bayar da amsoshin tambayoyin da waɗannan malamai suka yi masa ba," in ji alƙalin muhawarar.
Ya ƙara da cewa babu wata tambaya ɗaya da Abduljabbar ya tunkare ta ya bayar da amsarta.
Kuma ba ya tsayawa kan tambayoyin da aka gabatar masa.
Alƙalin muhawarar ya ce yanzu ya rage ga gwamnati ta yi nazari kan matakin da za ta ɗauka bisa muƙabalar da aka gudanar

Malam Abubakar Madatai ya yi kira ga Malam Abduljabbar ya tuba domin a cewarsa duk ya taɓa mutuncin Annabi SAW hukuncin kisa ne ya tabbata a kansa
Malamin ya shawarci Malam Abduljabbar ya fito ya tuba ya nemi afuwar alummar musulmi cewar ya yi kuskure a yafe masa
Sannan ya ce Abduljabbar ya cakuda maganganunsa wajen amsa tambayoyida malamai suka yi masa
“Kalubalantar Ayoyin Kur’ani yake ba hadisan Annabi ba.”
Sai dai Abduljabbar ya ce ba zai tuba a wajen wannan muƙabala ba har sai an ba shi cikakiyar dama sannan zai yi idan ya samu ƙwararan hujjoji
Abduljabbar ya ce zai tuba idan har aka ba shi hujjojin da suka fi nasa.
“Amma yanzu mutum ba zai tuba ba bayan yana kan gaskiya,” in ji Abduljabbar
A cewarsa ba a biyo turbar da zai tuba ba.

Malam Abduljabbar ya yi kira ga gwamnati ta sake samar da lokaci wadatacce domin sake wata mukabalar.
Ya ce yana buƙatar lokacin da zai fito da “matsalar yadda take”
Sannan ya roki idan za a sake yi a nun muƙabalar kai tsaye
Malam Abubakar mai Madatai daga ɓangaren Tijjaniyaya yi wa Abduljabbar tambayar ya faɗa masa hadisin ya ce an faɗi cewa Annabi “ya sha giya” lokacin da aka yi aurensa da Nana Khadija
Sannan kuma da inda ya ce Atsatson da annabi ya fito ba tsarkakakke ba ne
A lokacin da zai bayar da amsa Abduljabbar Ya ce abin ne mai sauki: “ji na ke ko dai ma’anar ce ba a fahimta ba.”
Ya ce dukkan kalaman da ake tuhumarsa akai shi kore su ya ke yi ga annabi SAW.
Abduljabbar ya kasa ba ni amsa

Mal Madatai ya ce maganar da Abduljabbar yake yi jurwaye mai kamar wanka yake nufi kan danganta annabi da dan giya
Sannan a cewar malamin ya gaza bayar da amsar abin da yake tambayarsa.
Ya ce sakamakon gazawarsa (Abduljabbar) na bayar da gamsashiyar hujja kan wannan batu, ya nemi afuwa saura ya rage gare shi da gwamnati
Malamin kuma ya sake jaddada tambayoyin da ya yi wa Abduljabbar Nasir kabara
Malam Ma’ud Hotoro ya tambayi Abduljabbar ya kawo masa hadisan da “aka mayar da Annabi Arne da Bunsuru da Bamaguje.
Ya kuma ce bai yarda a ba shi amsa da waya ba, sai dai ya fadi littafin a duba
Abduljabbar ya fara da cewar “duk a minti goma?”
Ya ce Hadisin 5564 a Bukhari ya ce annabi ya nunawa Sahabbai yana sa ta tara da iyalinsa, ya dawo ya shiga dakin matarsa ya saki labule, a cewar ruwayar Anas, Bukhari ya ce an ce annabi ya dakatar da Anas. Ya ce babu ita a ruwayance wanda shi kuma korewa annabi wadannan kalamai, kuma kage aka yi wa annabi
A cewar Abduljabbar babu lokaci isasshe da zai bankaɗo irin kagen da aka yi wa annabi SAW
“Dole na tsarkake annabi,” in ji shi
Sannan ya musanta cewa Annabi Bamaguje, kuma yana kore irin wadannan kalmomi da ake yiwa Annabi
Yace matsalar daga cikin hadisai take shi ya sa ya ke fito da irin wadan nan hadisai, don kare mutunci Annabi SAW.

Abduljabbar ya kasa ba ni amsa - Malam Mas’ud
Malam Mas’ud Mas’ud ya ce Abduljabbar bai ba shi amsar tambayar da ya yi masa ba saboda gazawa wajen bude littafin da hadisin da yake da’awa da su
Ya ce dukkan hadisan da mallam Abduljabbar ya kawo babu su “kagaggu ne”
Malamin ya sake dawowa da malam Abduljabbar tambayar da ya yi masa tun da faru
Malam Bashir ya kafa wa Abduljabbar hujja cewa babu wani lafazi da ya alakanta da “kawaliya”
Ya ce: “Annabi Ya tura Ummusulaimin ga wata budurwa da ta duba masa bakinta da digadiginta, ba da manufar da shi Malam Abduljabbar ya ambata ba. Yace al’aurar mace zuwa ga mace ba ya zama al’aura kamar yada yake ga namiji zuwa namiji.
Malamin ya kuma zargi Abduljabbar da cewar maganar ridda suna sane da ita, amma sai gashi a kwanakin baya, an jiyo shi ya ce mutum milliyan biyu sun yi ridda aMasar
Sannan ya ba shi amsar cewar bai je Masar din da yake da’awar zuwa ba Sudan ya je
Sannan mutumin da yake da’awar cewar yana yada farfaganda an kure shi, sai dai ya ce yana fadar hadisan da babu su.
Sannan akwai hadisan da yake fada da ba zai same su ba, domin da tuni malaman da suka gabata sun fito da su.
Malam Bashir ya ce dukkanin abin da suke fada shi Mallam Abduljabbar ne ya fada
Ya yi kira ga Abduljabbar da ya tuba, ya janye kalamansa.
Da aka ba Abduljabbar damar ya bayar da amsa sai ya nuna cewa har yanzu yana kan kalamansa na farko cewar minti goma ya yi kadan.
Kuma ya gaza bayar da amsar cewar a ina annabi SAW ya ke aika UmmuSulaim na zuwa ta gano masa tsiraicin mata.
Malam Bashir Ya ja hankalin Mallam Abduljabbar cewar da ya daure ya ringa fadar litattafan da yake da’awar a inda hadisan suke amma ya gaza
Ya ƙara jan hankalinsa da cewar dukkan abin da mutum ya fada abin tambaya ce ranar gobe kiyama

Malam Abduljabbar ya kasa tsayawa ya fuskanci abokan muƙabalarsa inda ya de minti 10 da aka ƙayyade ya masa kaɗan.
Ya ce littafan da ya zo dasu, minti goma tayi kadan a kwance su. A cewarsa shi yana ƙoƙarin rarrabe hadisan da ake yi wa annabi ƙarya ne.
Ya kuma zargi alƙalin muƙabalar da nuna goyon baya ga malaman da suke mukabala da shi.
An kunna jawabin da malaman Kano suka gabatarwa gwamnatin Kano kan kalaman Abduljabbar Nasir Kabara
Mallam Bashir ya sake dawowa a karon farko bayan saka jawabin malaman na korafi akan Abduljabbar da suka gabatar a gaban gwamna.
A cikin ƙorafin da suka gabatar akwai inda Abduljabbar ke cewa annabi yana da kawaliya da kuma inda yake cewa wasu haddisai da ya ƙaryata sun ce annabi ya biya wa wata mata bukata ‘ta saduwa’
Sai dai Malam Abduljabbar ya kasa kare kansa inda ya ce minti 10 ya yi masa kadan bisa dokar muƙabalar
Ya amsa cewar ya yi laifi a yi masa hukunci
Ya kuma yi zargin cewar ba a sanar da shi tsarin da aka yi na cewar miniti 10 aka ba bayar ba: “Da na sani ba zan zo da lattafai har 500 ba,” in ji shi.
Amma kuma ya musanta cewar “Annabi ya tura kawaliya don ta neman masa wata budurwa.”
Ya ƙara da cewa akwai gurɓatattun Hadisai cikin Hadisai”
Shugabancin zauren muƙabala da Malam Abduljabbar a Kano ya karɓi ƙorafin Malamin inda ya buƙaci a kunna kofarin da malaman Kano suka kai ƙararsa ga gwamnati.
Kuma shugaban shirya muƙabalar Dakta Tahar Adamu Baba Impossible ya amince a kunna ƙorafin tun daga farko har ƙarshe domin yin adalci ga Abduljabbar.
Kuma yanzu muƙabalar za ta karkata ne kan korafin na malaman Kano kamar yadda Abduljabbar ya buƙata.

Malam Kabir Bashir ƙofar Wambai ya kafa hujja da karatun Shiekh Nasir Kabara da kuma na ƙanin Malam Abduljbbar
Ya ce “ainihin hadisin shi ne wata mata mai larurar kwakwalwa ta zo wajen manzon Allah ta ce tana son ganinsa domin tana da bukata, sabodahikimar Manzon Allah, maimakon ya ba ta amsa a cikin majalisinsa, saboda kar ya kunyata ta, sai ya ce kije ki zaɓi dukkan inda kike so a cikin hanyoyon Madina, ya zabi ya zauna da ita kadai don kada a ji matsalarta.”
Kuma ya ce marigayi Mahaifin Abduljabbar Mallam Nasir Kabara haka ya fassara.
Sai dai bayan bayyana wa Abduljabbar damar bayar da Amsar abin da aka ce malamin ya ƙara nanata cewa ba a yi masa adalci ba yana mai ƙorafin cewa “an sauka daga cikin sharuddan da aka gindaya a muƙabalar”
Malam Kabir Bashir Kofar Wambai daga ɓangaren Izala yanzu ke yi wa Malam Abduljabbar tambaya.
Ya ce a kunna masa karatun da Abduljabbar inda yake cewa a cikin hadisin Buhari wata mata ta zo wajen manzon Allah tana yi wa annabi kwarkwasa, kuma har ya biya mata buƙata a ɓoye.

Malam Abduljabbar ya ƙi bayar da amsa
Mallam Abduljabbar y ƙi ba Malam Kabir Bashir Kofar Wambai amsa inda ya ce ba a yi masa adalci ba, saboda shi ba a ba shi damar da zai kunna murya ba kamar yadda abokan mukabalar sa suke yi.
Ya ce ba zai sake amsa wata tambaya kan wata murya da aka kunna ba sai dai waɗanda aka kai wa gwamna da Sarki da har ta kai ga kotu ta rufe masa masallacinsa aka hana shi wa'azi.
Ana kunna wa'azin Malam Abduljabbar a muƙabalar, kuma har yanzu Malam Rabiu Rijiyar Lemu yana jiran amsa daga Abduljabbar kan tambayar da ya yi masa

An fara fafatawa da Shiekh Abduljabbar a muƙabalar da gwamnatin Kano ta shirya tsakanin shi da wasu malaman jihar.
Malam Rabiu Rijiyar Lemo ne ya fara yi wa Abduljabbar tambaya kan auren Annabi SAW da Safiyatu da kuma batun yin fyade da tsirara.
Malamin ya nemi Abduljabbar ya kawo masa hadisin a Bukhari.
Amma Abuljabbar ya mayar da martani inda ya ce bai kamata an fara muƙabalar da tambayoyin da aka yi masa ba, ya kamata a ce ya yi bayani a kan kagen da aka yi masa na ɓata suna.
Amma duk da haka an buƙaci ya amsa tambayar.
Ya kuma amsa da cewa Anas ɗan malik shi ya kore hadisin "kore wa ma’aiki kalaman da ake masa batanci yake yi"
Sai dai an ƙalubalanci Abduljabbar, inda Malam Rabi’u Rijayar lemo ya ce bai bayar da amsar dai dai ba, inda ya ce hadisin ya bambanta da abin da ya faɗa

Alƙalin muƙabalar Farfesa Salisu Shehu ya ce za a tabbatar da gaskiya a muƙabalar sannan ya zayyana kai’dojin mukabalar kamar haka:
Za a gabatar da muƙabalar da Hausa
Dukkan bayanan da ake zargin Abduljabbar ke yi da ke tattare da rikici, za a fitar da su dalla dalla ga ɓangarorin biyu domin fahimtar juna
Dukkan bangarorin za a ba su dama ba tare da fifita wani
Kowane bangare za’a ba shi minti 10
Ana buƙatar hujjoji ingantattu kuma karɓaɓbu a musulunci
Dolo ne dukkan masu muƙabalar su kiyaye cakuda hadisai da kuma ayoyi, a gabatar da su cikin ladabi
Dole ne a girmama juna tare da yin amfani da lafazi na mutuntawa a yayin mukabala
Ba a yarda masu muƙabala su katse daya daga cikin masu mukabala a yayin da yake magana har sai lokacin da aka bayar ya cika
Babu zamba ko ɓatanci ko aibatawa ko cin mutuncin bangarorin biyu a yayin mukabalar
Babu zuga babu kirari, ko wani abu da zai nuna bangaranci a yayin mukabalar
Ba a yar da a nuna tasirin wasu kalamai da daya daga cikin ɓangarorin biyu suka gabatar a yayin taron
Dukkan Maudu’i suna da minti 30 tare da bayar min 5 na dauraya
Sannan za a bayar da dama na minti 5 na nuna hoto ko bidiyo ko na murya
An dade ana jiran wannan rana domin fafata muƙabala da Malam Abduljabbar a Kano
Wasu Malaman jihar Kano sun soki wa’azin malamin da yin kalamai na ɓatanci ga Annabi SAW, inda suka kai kukansu ga gwamnati.
Wannan ne ya sa gwamnatin jihar Kano ta dakatar da ayyukan Sheikh Abduljabbar daga yin karatu da tafsiri a masallacinsa.
Gwamnatin Kano kuma ta ba Abduljabbar damar amincewa da yin muƙabala domin ya kare kansa.
Gwamnatin Kano ta ce manufar muƙabalar shi ne tabbatar da gaskiya da inganci bisa dacewa kan abin da malam Abduljabbar yakebayyanawa ga Annabi Muhammad SAW, a rubuce-rubucensa, wandakuma za a bayar da hujja akan Ayoyin Kur’ani da hadisai
A cikin jawabinsa na buɗe taro muƙabalar, Kwamishinan lamurran addini na Kano Dakta Tahar Adamu, ya ce gwamnati ba ta goyon bayan kowa kan maƙabalar tare da cewa za a tabbatar da an yi wa kowane ɓangare adalci.
“Kowa ya san cewa Allah ɗaya ne kuma Annabi Muhammad Manzon Allah ne,” in ji shi.




