Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Sunday Igboho: Gwamnatin Benin tana bincike kan mai fafutikar kafa kasar Yarabawa
- Marubuci, Daga Nduka Orjinmo
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
Wata kotu a Benin ta bayar da umarnin a kai jagoran masu fafutikar kafa kasar Yarbawa a Najeriya gidan yari bayan 'yan sandan kasar sun tsare shi.
Ana tuhumar Sunday Adeyemo, wanda aka fi sani da Sunday Igboho, da laifin shiga kasar ba bisa ka'ida ba tare da kokarin tayar da husuma, amma ya musanta hakan.
Sai dai tun bayan kama shi, gwamnatin Najeriya ta yi gum da bakinta, ba kuma tare da ta fitar da wata sanarwa kan taso keyarsa gida domin fuskantar shari'a ba.
Maimakon haka, a yanzu kotu a birnin Cotonou tana tuhumarsa da aikata laifuka a can, kuma a jiya Litinin an sake mayar da shi kotu.
Me ya sa aka kama shi a Benin?
A makon da ya wuce ne aka kama shi a Benin tare da mai dakinsa, amma a yanzu an sake ta.
Rahotanni sun bayyana cewa Igboho da mai dakinsa suna kan hanyarsu ta tafiya kasar Jamus ne, inda suke da izinin 'yan kasa.
Gwamnatin Najeriya na zargin Mr Adeyemo da jibge makamai ba bisa ka'ida ba, da kiran al'ummar Yarabawa su balle daga Najeriya, da kokarin tayar da rikicin kabilanci da ka iya janyo kashe-kashe.
Sai dai magoya bayansa sun ce fursunan siyasa ne da aka tsare shi saboda yana kokarin kare al'ummar Yarabawa daga hare-haren Fulani makiyaya.
Me ya sa ya bar Najeriya?
Ya tsere ne daga kasar bayan samamen da 'yan sandan ciki suka kai gidansa a farkon watan Yuli, inda aka kashe biyu daga cikin yaransa.
An kuma kame 12 daga cikinsu lokacin samamen, kuma har yanzu ba a kai su kotu ba.
A makwannin da suka gabata, gwamnatin Najeriya na kokarin magance matsalar 'yan a-ware a kasar. A watan Yuni aka tsare jagoran 'yan a-waren da ke son kafa kasar Biafra Nnamdi Kanu.
An kama shi a wata kasa da ba a bayyana ba, aka taso keyarsa zuwa gida Najeriya.
Lauyoyinsa sun zargi cewa, an sato shi ne daga kasar Kenya, inda aka gana masa azaba, amma hukumomin Kenya sun musanta wannan zargin.
Za a iya taso keyarsa daga Benin?
Tawagar lauyoyin Mista Adeyemo ta ce Najeriya na fatan taso keyar wanda suke karewa gida, a lokacin da aka kama shi a Cotonou.
Sun ce an tashi jirgin sama da aka cika shi da mai, ana jiran a tsallaka iyakar kasar da Igboho.
A shekarar 1984 kasashen Najeriya, da Togo, da Benin da kuma Ghana, suka rattaba hannu kan yarjejeniyr taso keyar 'yan kasashensu da suka aikata laifi zuwa gida don fuskantar shari'a, amma ban da wadanda ake nema kan dalilan siyasa.
Wakilan Mista Adeyemo sun kafe cewa ya samu kan shi a cikin halin da ya ke ciki ne saboda kokarin kafa kasar Yarabawa.
Sannan Najeriya da Benin na cikin kasashe 15, da ke cikin kawancen kungiyar kasashen tattalin arzikin yammacin Afirka.
Karkashin dokokin taso keyar masu laifi na kungiyar Ecowas wadda jamhuriyar Benin na cikin kawancen, dole ne kasar da ke son taso keyar dan kasarta ta aika da bukatar hakan, ta kuma jera zarge-zargen da ake yi wa mutumin kafin a maida shi gida. Sanna kotu ce kadai ke da ikon tabbatar da hakan.
Shin an bukaci a taso keyarsa zuwa gida?
Amma ana zargin gwamnatin Najeriya da kokarin yi wa 'yar karamar kasar makociyarta murdiya, domin sako Mista Adeyemo ba tare da an kai batun shi gaban kotu ba.
Fitaccen lauyan nan dan Najeriya, Femi Falana, ya shaida wa BBC cewa, ofishin difilomasiyyar Najeriya ya rubutawa hukumomin Benin wasika, tare da bukatar a taso keyar Mista Adeyemo zuwa gida. Sai dai wannan baya daga cikin tsarin shari'a.
"Gwamnatin Najeriya ta bukaci hakan, amma ba kan tafarkin shari'a ba," inji shi.
Falana ya yi amanna da cewa, Najeriya wadda ta sha kan Benin a fadin kasa da karfin tattalin arziki, na kokarin amfani da matakin siyasa domin ganin an dawo da wanda ake tuhumar zuwa gida.
Mecece alakar Najeriya da Benin?
Dukkan kasashen biyu na da iyaka da juna, wadda a watan Agustan 2019 Najeriya ta rufe ta, inda ta ke zargin 'yar karamar makociyarta da taimakawa masu fasa kwaurin kayan da kasar ta haramta shiga da su.
Rufe iyakar dai ya dan janyo rashin jituwa tsakanin kasashen, lamarin da ya sanya shugaba Patrice Talon nikar gari har zuwa Najeriya, domin ganawa da gwamnati da kuma rokon a sake bude iyakar. Amma iyakokar kasashen biyu ta ci gaba da kasancewa a rufe har farkon wannan shekarar.
Mista Falana ya amince cewa batun Mista Adeyemo ya tabbatar da akwai jan aiki da kuma abubuwan da Najeriya za ta koya daga kankanuwar makociyarta, kan batun kare hakkin dan adam.
"Kotu ta saki matarsa da aka kama su a lokaci guda, saboda babu wata tuhuma akan ta," in ji Mista Falana.
Ya kara da cewa, yanayin halin da ake ciki a Najeriya, na daukar makwanni ba tare da an san makomar yaran Igboho 12 da aka kama ba a lokacin da aka kai samame gidanshi, saboda har yanzu ba a kai su kotu ba.
Wanene Sunday Adeyemo?
A watan Oktobar bara ne Mista Adeyemo ya fara yin suna lokacin da ya yi amfani da ranar bikin karbar 'yancin Najeriya, don kira ga al'ummar Yarabawa su fito domin kafa kasarsu, sai dai an soki wannan matakin.
Tun daga lokacin, ya yi tambari da fice a kasar, bayan sanya kan shi cikin daya daga rikici mafi muni da aka yi tsakanin fulani makiyaya da wasu kungiyoyi kan batun kawo karshen kiwon sake, lamarin ya janyo hasarar rayuka da dukiya.
Bayan kisan wani dan siyasa a watan Junairu, Mista Adeyemo ya ga lokaci ya yi da zai dauki mataki, inda ya umarci Fulani makiyaya da ke yankin Yarabawa su fice daga kudu masu gabas, wanda ake wa kallo da yankin Yarabawa, su koma inda suka fito wato arewaci tare da zarginsu da aikata dukkan laifukan da ake yi a yankin.
Hukumomin Najeriya sun ce matakin na sa ya janyo mutuwar mutane da dama a yankin kudu maso kudancin kasar, amma Mista Adeyemo ya musanta zarge-zargen da ake masa tare da cewa ana neman sa ruwa ajallo saboda kiran da ya ke yi.
Ya yin da magoya bayansa ke jinjina ma sa a matsayin gwarzo, su kuwa wadanda ba sa goyon bayan shi na ma sa kallon wani mutum mai hadari, wanda ya janyo kashe-kashen mutane.