An fara tsagaita wuta a yakin Isra'ila da Falasdinawa a Gaza

A Palestinian man inspect the damage at his room after Israeli airstrikes on his neighbourhood in Jabalia refugee camp, North Gaza strip on May 20, 2021

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A kalla mutum 232, cikinsu har da mata da kananan yara fiye da 100 ne su ka mutu a Gaza

Tsagaita wutar da Isra'ila da kungiyar Hamas ta Falasdinawa su ka amince da ita ta fara aiki.

An fara tsagaita wutar ne da sanyin safiyar Juma'a, wanda ya kawo karshen kwana 11 na jefa baba-bamai da su ka yi sanadin mutuwar fiye da mutum 240, mafi yawansu a Gaza.

Falasdinawa sun kwarar bisa titunan Gaza jim kadan bayan da yarjejeniyar tsagaita wutar ta fara aiki, yayin da wani jami'in Hamas ya yi gargadi cewa "hannayen mayakanta na nan kan kunamar bindiga".

Duka Isra'ila da Hamas sun yi ikirarin samun nasara a wannan yakin.

Shugaban Amurka Joe BIden ya ce tsagaita wutar zai bayar da wata dama ta samun ci gaba a fagen zaman lumana.

Ranar Alhamis Isra'ila ta kai harin sama fiye da 100 a arewacin Gaza. Ita kuma Hamas ta mayar da martani ta hanyar harba rokoki cikin Isra'ila.

A kalla mutum 232 cikinsu har da mata da kananan yara fiye da 100 sun rasa rayukansu a Gaza.

A Isra'ila, mutum 12, cikinsu har da kananan yara 2 ne su ka mutu. Isra'ila ta ce rokoki fiye da 4,000 Hamas ta harba cikin kasar.

Adi Vaizel, looks at the damage caused to the kitchen of his house after it was hit by a rocket launched from the Gaza Strip

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Wani dan kasar Isra'ila na duba barnar da wani roka ya yi wa gidansa