Labaran ƙaryar da aka yada kan rikicin Isra'ila da Falasdinawa
- Marubuci, Daga BBC Monitoring
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Sashen da ke bin diddigi
A yayin da rikicin Isra'ila da Falasdinu ke kara kamari, ana ta yada labarai da hotuna na karya a shafukan intanet a 'yan kwanakin nan.
Mun duba irin labaran karya da aka yi ta yadawa daga kowane bangare a shafukan intanet kan rikicin Isra'ila da Falasdinnawa wadanda ke janyo muhawara mai zafi.
Bidiyon roka mai cin wuta na Syria ne ba Gaza ba

Asalin hoton, YouTube
Wani mai magana da yawun Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya yada wani bidiyo a Tuwita, inda yake ikirarin cewa mayakan kungiyar Hamas ne suka harba wata roka mai cin wuta zuwa wani yanki mai cike da jama'a na Isra'ila.
Ofir Gendelman ya rubuta cewa: "Kashi daya bisa uku na wadannan rokokin fiye da 250 sun fada Zirin Gaza ne, sun kashe Falasdinawa."
Amma bidiyon tsoho ne, kuma a Syria abin ya faru ba a Gaza ba.
An dauke shi ne a yayin da gwamnatin Syria ke kai wasu hare-hare kan kungiyoyin 'yan tawaye a birnin Daraa a shekarar 2018.
Kamfanin Tuwita ta bayyana sakon a matsayin "wata kafa da ake juyawa", yana mai kara sanya hujjojin da suke tabbatar da cewa bidiyon na yakin Syria ne.
Bayan da ya sha suka, Mr Gendelman ya goge sakon.
Sakonnin tuwita kan dakarun Isra'ila da aka yada na karya ne
Wasu masu amfani da Tuwita sun yada abin da suke ikirarin hotunan rubutattun sakwannin da dakarun tsaron Isra'ila suka wallafa ne inda suka ce: "Muna so mu yi kisa kuma muna so mu tayar da bama-bamai su kashe yara."
Wadannan sakwanni na karya ne da ake ta yada su a saukake ta intanet.
Rundunar tsaron Isra'ila ta ce ba ta yi wadannan kalamai ba a shafinta na Tuwita ko wani wajen daban ba.
Shafukan da aka yada sakwannin karyar an gano wasu 'yan gani kashenin Falasdinu ne suka bude su.
Bidiyon 'jana'izar karya' a Gaza

Asalin hoton, Twitter
Wasu masu amfani da shafukan sada zumunta a Isra'ila sun yi ta yada wani bidiyo da ke ikirarin cewa Falasdinawa ne suke jana'izar wani da harin sama na Isra'ila ya hallaka a Gaza - don janyo hankalin duniya su tausaya musu.
A cikin bidiyon, wanda wani mai bai wa Ma'aikatar Harkokin Wajen Isra'ila ma ya yada, wasu matasa ne suke dauke da wani abu mai kama da gawa a lullube da likkafani a kan kafadunsu.
Amma a lokacin da suka ji karar jiniya sai suka ajiye gawar suka ranta a na kare. Daga bisani sai wanda aka nannade a matsayin gawar ya tashi ya runtuma a guje shi ma.
Mun gano cewa an wallafa wannan bidiyon dai a watan Maris din 2020, inda rahotanni a lokacin ke cewa wasu matasa ne a Jordan suke kokarin kauce wa dokar kulle ta Covid-19 ta hanyar nuna cewa suna jana'izar karya.
An yada bidiyon sau da dama ta hanyar amfani da maudu'in "Palywood" wato masana'antar fina-finai ta Palestine, kuma magoya bayan Isra'ila ne suka yi ta yadawa a shafukan sada zumunta.
Bidiyon da ke nuna an cinna wa Masallacin Kudus wuta

Asalin hoton, Twitter
Wasu magoya bayan Falasdinu sun yada wani bidiyo da suke ikirarin cewa Masallacin Kudus ne ke cin wuta, suna zargin Isra'ila da "kona Masallacin Kudus."
Bidiyon na gaske ne, amma ainihin abin da ya faru shi ne wata bisihiya ce da ke kusa da masallacin ta kama da wuta, ba shi masallacin ne ke ci da wutar ba.
Harabar masallacin da ke Birnin Kudus na daga cikin wurare mafiya tsarki na Musulunci, sannan kuma akwai wajen bautar Yahudawa ma a wajen da ake kira Temple Mount.
A cikin bidiyon, an ga dandazon wasu Yahudawan Isra'ila suna wakar adawa da Falasdinnawa a Bangon Yamma, inda ake iya hango hayaki daga nesa.

Asalin hoton, TWITTER/ARIEH KOVLER
An kaso gano ainihin abin da ya tayar da wutar.
'Yan sandan Isra'ila a wata sanarwa sun ce tartsatsin wutar da Falasdinawa masu ibada suka jefa ne ya tayar da wutar. Amma Falasdinawan sun ce jami'an Isra'ila ne suka jefa gurneti.
A cewar kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ce, bishiyar na da nisan mita 10 ne kawai daga masallacin.
An yi saurin kashe wutar sannan masallacin bai lalace ba.
Tsohon bidiyo da ke nuna makamai masu linzami a kan titunan Gaza

Asalin hoton, FACEBOOK/MIVZAK LIVE
Wani sakon Tuwita da aka yada sosai ya yi ikirarin nuna wata babbar mota ta kungiyar Hamas mai dauke da makamai masu linzami tana tafiya a kan titi a Gaza. Ana kuma iya jin muryar yaro a bidiyon.
Sakon, wanda wani shafi a tuwita mai goyon bayan Isra'ila da ke Amurka ya yi ikirarin cewa: "Mun sake ganin yadda Hamas ke amfani da fararen hula a matsayin kariya don yi wa Yahudawa kisan gilla.... don sun san Isra'ila ba za ta mayar da martani ba saboda gudun taba mutanen da ba su ji ba su gani ba."
Mun gano cewa an wallafa bidiyon ne a shafin Facebook ranar 25 ga watan Nuwamban 2018, inda aka rubuta cewa an dauki biidyon ne a garin Abu Snan a Galilee a Isra'ila.
Wani kwararren mai bincike a wata kungiya Aric Toler, ya ce yana tunanin bidiyon na nuna makamai masu linzami marasa illa na atisayen sojojin Isra'ila.
Daga baya an goge shafin da ya wallafa bidiyon, tare da bayar da hakurin kuskuren da suka yi.
Wadanda suka hada wannan rahoto su ne Alistair Colema da, Shayan Sardarizade da Christopher Giles da kuma Nader Ibrahim.











