'Yan sanda na bincike kan bidiyon da matasa suka zane 'ƴan mata da dorina a Bauchi

mace da ta juya

Rundunar ƴan sandan jihar Bauchi da ke arewacin Najeriya ta ce ta fara bincike kan wani bidiyo da ya yaɗu a intanet kamar wutar daji, da ke nuna yadda wasu matasa suka dinga zane wasu ƴan mata da dorina.

A sanarwar da rundunar ta fitar, ta ce an ja hankalinta ne kan wannan bidiyo, inda ta jajantawa waɗanda lamarin ya faru da su, tare da shan alwashin gano waɗanda suka aikata wannan abu da gurfanar da su gaban shari'a.

Sanarwar me ɗauke da sa hannun mai magana da yawun rundunar, SP Ahmed Mohammad Wakil ta ce tuni rundunar ƴan sandan ta gayyaci ƴan matan da abin ya shafa da su bayar da bayanan da za su kai ga kama tare da gurfanar da samarin a gaban shari'a.

Wannan layi ne

Me bidiyon ya ƙunsa?

Bidiyon yana nuna yadda wasu zaratan matasa ɗauke da dorina da adduna a hannayensu suka rutsa wasu ƴan mata wani kango.

A cikin bidiyon wanda BBC ta gani, an ga yadda samarin suke ta jibgar ƴan matan da dorina ɗaya bayan ɗaya, yayin da su kuma suke tsala ihu.

A wasu lokutan ƴan matan kan miƙa hannu don a yi musu bulalar a kai, amma sai samarin su ƙi su dinga tsala musu dorinar a jikinsu.

Da yawan yan matan sun dinga kuka da ihun neman a kawo musu ɗauki, amma duk da yawan samarin da ke wajen ba a samu wanda ya yi ƙoƙarin hanawa ba.

Wasu da ke wajen sun yi ta ƙirga yawan bulalar da ake yi wa kowace mace, inda hakan ya nuna cewa kowa sai an yi mata bulala 10 sannan ta koma gefe.

Akwai wacce da ta so bujirewa sai mai yi mata bulalar ya sanya kanta a tsakanin ƙafafunsa ya dage iya ƙarfinsa ya dinga lafta mata ta ko ina a jikinta, yayin da ita kuma wata aka ji tana ihun cewa "wayyo kunnena, kar ka dake ni a nan."

Sanarwar ƴan sandan ta ƙara da cewa bayan samarin sun gama dukan ƴan matan sai kuma suka saka reza suka aske musu gashinsu, sannan suka dinga zaginsu tare da gaya musu kalaman ɓatanci.

"Tuni mutanenmu suka fara bincike, kuma nan ba da daɗewa ba za a kamo waɗannan matasa a gurfanar da su a gaban shari'a.

"Irin wannan cin zarafi na keta haƙƙin ɗan adam ɗaga hankali kawai yake ba, abu ne na cin zarafin wani jinsi," in ji sanarwar.

Ta kuma ci gaba da cewa: "Kowace mace tana da damar yin rayuwa cikin daraja - da jin cewa ba ta cikin fargaba, ko tsoron cin zarafi da ƙyama, kuma za mu tabbatar da cewa rundunar ƴan sandan jihar Bauchi ta tabbatar da waɗannan abubuwa kamar yadda doka ta tanadar."

Wannan layi ne

Me ƴan matan suka yi?

Rahotanni sun ce samarin sun aikata hakan ne ga ƴan matan bisa zarginsu da yawon banza, wato abin da ake kira "good evening," a unguwar Ƙofar Dumi.

Ko a cikin bidiyon ma an ji inda suke gargaɗin ƴan matan da cewa abin da suka aikata ɗin ne ya sa suke musu wannan hukuncin.

Wasu mazauna Bauchi da BBC ta ji ta bakinsu sun ce dama unguwar ta yi ƙaurin suna wajen munanan ayyuka musamman na ƴan sara suka.

Amma sun tabbatar da cewa a yanzu an kafa kwamiti don magance matsalolin rashin tsaro a unguwar.

To sai dai mutane na dasa ayar tambaya kan cewa ko samarin suna da hurumin da za su yanke wa baligan ƴan mata irin wannan hukunci na duka kan abin da suke zarginsu da shi?

A dokokin Najeriya dai babu inda aka bai wa wasu izinin ɗaukar doka a hannunsu duk irin laifin da suke zargin wani da aikatawa.

Mutane da dama masu tsokaci a shafukan sada zumunta a kan bidiyon na ganin kamata ya yi idan ma har ƴan matan sun aikata hakan, to a kai batun gaban iyayensu ko hukumar Hisbah ko ta ƴan sanda.

A Najeriya ɗaukar doka a hannu da mutane ke yawan yi ta sha jawo a tafka kuskure da a wasu lokutan har a kan rasa rayukan waɗanda ake hukuntawar ba bisa ƙai'da ba.

Wannan layi ne