Fyade: Ɗan shekara 50 ya binne jikansa da ransa a Bauchi

Babban sufuton 'yan sandan Najeriya

Asalin hoton, @PoliceNG

Rundunar ƴan sandan Bauchi ta kama wani uba ɗan kimanin shekara 50 da ake zargin ya binne jikansa (jariri) a raye.

Kakakin rundunar 'yan sandan ta Bauchi DSP Ahmed Mohammed Wakil ya shaida wa BBC cewa mutumin da ta bayyana Bawada Audu ya aikata kisan bayan 'ƴarsa mai shekara 17 ta haifi namiji.

Ƴan sandan sun ce an yi wa yarinyar fyaɗe ne a watan Janairu, kuma ta samu ciki har ta haihu. Kuma ƴan sandan sun ce mahaifin yarinyar ya kashe jaririn ne saboda yana gudun abin faɗi.

Ƴan sandan sun ce sun samu labarin ne daga wata ƙungiyar kare haƙƙin ɗan Adam da ba su bayyana sunanta ba inda kuma suka ƙaddamar da samame a ranar 16 ga watan Satumban 2020.

"Mahaifin ya amsa cewa shi ya karɓi jaririn kamar misalin ƙarfe biyu na dare bayan 'ƴarsa ta haihu, ya tafi bayan gidansa ya binne shi da ransa," a cewar ƴan sandan Bauchi.

Mahaifin kuma ya shaida wa 'ƴan sandan cewa dalilin kashe jikansa saboda 'ƴarsa ta kawo masa abin kunya shi ne ya sa ya halaka shi.

Ƴan sandan sun kuma ce bayan jin cewa an binne jaririn da ransa suka tono shi inda aka binne shi - bayan garzayawa da jaririn asibiti, likitoci suka tabbatar da jaririn ya rasu bayan gudanar da bincike.

Yarinyar ta shaida wa ƴan sanda cewa wani mai suna Danjuma Malam Uba ne ya yi mata ciki, wanda kuma ya gudu.

Rundunar ƴan sandan Bauchi ta ce tana kan bincike domin kama shi don jin daga bakinsa kan zargin ciki da yarinyar ta ke zargin ya yi mata.

Ƴan sandan sun ce suna tsare da mahaifin yarinyar da ake zargi ya kashe jikansa, kuma suna kan gudanar da bincike don tabbatar da gaskiyar al'amarin.

Matsalar fyaɗe na neman zama ruwan dare a sassan Najeriya lamarin da ya sa wasu ke ganin ya kamata a rika ɗaukar tsauraran matakai a kan masu aikata wannan babban laifi.

A kwanan nan ne gwamnatin Kaduna ta kafa dokar yin dandaƙa ga duk wanda aka kama da laifin fyaɗe a jihar domin magance matsalar.