Zaɓen Uganda: Jagoran ƴan adawa Bobi Wine ya yi fatali da sakamakon zaɓe

Asalin hoton, AFP
Jagoran ƴan adawar Uganda Bobi Wine ya ce bai yarda da shan kaye a zaɓen shugaban ƙasar da aka yi ranar Alhamis ba, kana yana fargabar halin da zai iya faɗwa tun bayan da sojoji suka kewaye gidansa.
Ya shaida wa BBC cewa ɗaruruwan sojoji sun tare a gidansa tare da iyalinsa, baya ga cin zarafin wasu magoya bayansa da suka riƙa yi.
Ranar Asabar ne hukumar zaɓen ƙasar ta sanar da sakamakon zaɓen a hukumance, inda ta bayyana shugaba mai ci Yoweri Museveni a matsayin wanda ya samu nasara da tazara mai yawa.
Bobi Wine da sauran ƴan takara goma da suka shiga zaɓen sun yi zargin tafka maguɗi, da kuma hana wakilansu sanya ido.
Kwana biyu kafin zaɓen ne hukumomi suka katse hanyoyin sadarwa, wanda Bobi Wine ya ce ya taimaka wajen boye cuwa cuwar da aka tafka.
Me shugaba Museveni yace ?
Shugaba Yoweri Museveni ya yaba da zaɓen da ya kira a matsayin mafi adalci a tarihin Uganda, yana mai cewa ya yi matukar farin ciki da sakamakon.
Museveni ya kuma gargadi 'yan adawa game da tashin hankali yana mai cewa gwamnati za ta hukunta su.
An yi zanga-zanga nan da can a wasu garuruwan domin nuna goyon baya ga abokin hamayyarsa Robert Kyagulanyi wato Bobi Wine,.
Museveni ya ce a wannan lokacin, gwamnatinsa za ta samar da ilimi kyauta wanda aka fara gabatarwa a makarantun firamare a shekarar 1997 ya fuskanci kalubale.
Kungiyoyin magoya bayansa sun yi bikin murna a Kampala da wasu garuruwa bayan an bayyana nasarar tasa.
A sakamakon zaben, Museveni ya samu kashi 58.64% na kuri'un da aka kaɗ baki ɗaya yayin da abokin karawarsa Bobi Wine ya samu kashi 34.83%.











