Uganda: Shugaba Yoweri Museveni ya yi nasara a zaben kasar

Asalin hoton, AFP
Hukumar zaben Uganda ta ayyana shugaban kasar wanda ya dade a kan mulki Yoweri Museveni a matsayin wanda ya lashe zaben kasar, a yayin da babban abokin hamayyarsa Bobi Wine ya yi zargin an tafka magudi.
Mr Museveni ya lashe kusan kashi 59 na kuri'un da aka kada, yayin da Mr Wine ke bi masa da kashi 35, a cewar Hukumar zaben.
Mr Wine, wanda tsohon mawaki ne, tun da farko ya yi alkawarin gabatar da shaidun da ke nuna cewa an tafka magudi. Hukumar zaben ta musanta cewa an yi magudi a zaben wanda aka gudanar ranar Alhamis.
Masu sanya ido a zaben sun soki gwamnati bisa toshe shafukan intanet.
Sun ce hakan ya nuna cewa zaben ba shi da sahihanci. Mr Wine ya ce zai gabatar da shaidun tafka magudin zabe da zarar an sake bude hanyar intanet.

An kashe mutane da dama sakamakon rikicin da ya barke gabanin zaben. 'Yan jam'iyyun hamayya sun zargi gwamnati da cin zarafinsu.
Sakamakon zaben zai bai wa Shugaba Museveni damar yin mulki a wa'adi na shida.
Shugaban kasar mai shekara 76 - wanda ya hau kan mulki a 1986 - ya ce yana son tabbatar da kwanciyar hankali da ci gaba a kasar.
A nasa bangaren, Bobi Wine - mai shekara 38 wanda sunansa Robert Kyagulanyi - ya ce ya samu goyon bayan matasa a daya daga cikin kasashen da ke da mafi yawan matasa a duniya.
Ranar Juma'a, a yayin da ake fitar da sakamakon zaben, Mr Wine ya ce sojojin kasar Uganda sun yi wa gidansa kawanya sannan suka yi masa kutse.
Sai dai mai magana da yawun gwamnati ya zarge shi da mayar da batun kamar wani "wasan kwaikwayo" domin ya sa a ji tausayinsa.
Mene ne sakamakon zaben?
"Hukumar zabe ta ayyana Yoweri Museveni... a matsayin zababben shugaban kasar Uganda," a cewar shugaban hukumar zaben Mai sharia'a Simon Mugenyi Byabakama ranar Asabar.
Ya kara da cewa kashi 57 na masu kada kuri'a ne suka yi zabe wato kusan mutum miliyan 18 da suka yi rijistar zabe.
Tun da farko, Mr Byabakama ya ce an gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali, sannan ya yi kira ga Bobi Wine, wanda ya ce an kama wasu jami'an kula da zabensa ranar Alhamis, da ya gabatar da shaidu kan zargin da ya yi na tafka magudi.
Yaya girman rikicin zaben?
An yi fama da rikicin zabe wanda ba a taba gann irin sa ba gabann zaben kasar, kuma mutanern da dama sun mutu sanadin dirar mikiyar da jami'an tsaro suka rika yi musu.
Gwamnati ta ce ta haramta taron jama'a domin hana yaduwar cutar korona amma 'yan hamayya sun ce an yi hakan ne da zummar murkushe su.

Asalin hoton, AFP
Sau da dama an kama Bobi Wine da wasu 'yan takarar jam'iyyun hamayya, kuma a lokacin zanga-zangar da aka yi domin bijirewa wani kamu da aka yi musu a watan Nuwamba, an kashe mutum fiye da 50.
Wane ne Yoweri Museveni?
Mr Museveni, wanda ya kwaci mulki a wata tarzomar da masu da ke da makamai suka yi a 1986, yana matsayin shugaban the National Resistance Movement (NRM).
'Yan kasar Uganda sun dade da kallonsa a matsayin mai ceto kuma wanda ya kawo zaman lafiya.
Sai dai ya yi kokarin ci gaba da zama a kan mulki ta hanyar sakawa masu yi masa biyayya da yin alfarma da yin katsalandan kan harkokin hukumomi masu zaman kansasu da kuma nuna wariya ga 'yan hamayya, a cewa wakiliyar BBC Patience Atuhaire.
Wane ne Bobi Wine?
Ana kallon Bobi Wine a matsayin mutumin da ya fi samun goyon baya a tsakanin 'yan takarar jam'iyyun adawa 10 da suka fafata a zaben shugaban kasar.
Mawakin mutum ne da ke da farin jini a yankunan karkara.
Jam'iyyarsa, the National Unity Platform (NUP) ta sha alwashin samar da abubuwan bukata na yau da kummum kamar inganta harkokin lafiya da samar da ilimi da wutan sa mai tsafta da kuma tabbatar da adalci.










