Yoweri Museveni: Abin da ya sa muka rufe shafukan sada zumunta a Uganda

Asalin hoton, Reuters
Shugaban kasar Uganda Yoweri Museveni, ya zargi shafin sada zumunta na Facebook da girman kai da nuna fifiko a yayin da yake tabbatar da rufe shafukan sada zumunta ranar Alhamis.
A jawabin da ya yi ta gidan talabijin na kasar sanye da kakin soji, Mr Museveni, ya ce ba zai lamunce wani mutum ya yi wa kasarsa karan-tsaye ba ko kuma ya yanke hukunci kan dan takarar da ya dace ko wanda bai dace a zaba ba.
Ya kara da cewa idan Facebook zai yi aiki a Uganda, dole ne kowa ya yi amfani da shi daidai wadaida.
Ranar Talata, hukumar da ke sanya ido kan kamfanonin sadarwar Uganda ta umarci kamfanonin su rufe shafukan sada zumunta, sa'o'i kadan bayan Facebook ya rufe shafukan "bogi" wanda ya ce suna da alaka da gwamnatin kasar.
Facebook ya ce ana yin amfani da shafukan wajen sauya ra'ayin 'yan kasar game da zaben da za a gudanar.
Masu amfani da shafukan sada zumunta sun soma bayyana samun tsaiko a shafukan Twitter, WhatsApp, Instagram da Snapchat ranar Talata.
Twitter ya mayar da martani da cewa hakan keta hakkin masu amfani da intanet ne.
Kamfanonin dillancin labaran AFP da Reuters sun ambato jami'an hukumar da ke sanya ido kan kamfanonin sadarwa na Uganda suna cewa an dauki matakin ne domin yin raddi ga Facebook a kan rufe shafukan da ke da alaka da gwamnatin kasar.
Lamarin na faruwa ne kwana guda kafin gudanar da zaben shugaban kasar.
Shugaba Yoweri Museveni, wanda ke neman wa'adi na shida a kan mulki, ya kwashe shekara 35 yana mulkin kasar.
Shugaban mai shekara 76 yana fuskantar 'yan takara 10, amma fafatawar ta fi zafi tsakaninsa da Robert Kyagulanyi, wanda aka fi sani da Bobi Wine, mai shekara 38 a duniya.










