Zaben Uganda na 2021: Wane ne Bobi Wine da ke son kada Yoweri Museveni?

Bobi Wine raising his fist

Asalin hoton, AFP

Ba a taba mika mulki cikin kwanciyar hankali ba a Uganda, Amma tauraron mawakin nan da ya zama dan siyasa Bobi Wine na fatan sauya wannan al'ada, da kuma sauya shugaba Yoweri Museveni a zaben kasar da za a yi a ranar Alhamis.

Wakiliyar BBC a Afrika Catherine Byaruhanga ta yi duba kan wannan mawaki.

Yayin da ya rage 'yan makonnin a gudanar da zaben shugaban kasa, rana mafi muhimmanci mai tarihi ga Bobi Wine, ya gabatar da yakin neman zabensa ga ainihin gidan kakanninsa.

Tauraron mawakin mai shekarar 38, wanda ainihin sunasa Robert Kyagulani, ya gina rayuwarsa ne duka a Kampala babban birnin kasar, amma Kanoni da ke tsakiyar Uganda, nan ne inda magoya bayansa suka bayyana.

Matasa da dama sanye da jajayen kaya, suna fitowa daga dazuka da gonaki domin bin motarsa. Bobi Wine wanda ake kira shugaban kasar geto, ya fito ta saman motarsa yana ta yi wa mutane gaisuwa.

Bobi Wine supporter

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Yawancin magoya bayan Bobi Wine matasa ne

Ba kamar yadda aka saba gani ba ga masu takarar shugaban kasar, yanzu yana sanya riga mai silke da ke kariya daga harsashin bindiga da kuma hular kwano.

Dalilin haka kuwa, a watan Disamba an harbi motarsa, sai dai ya tsallake rijiya da baya. Bobi Wine daga nan ya ce ya gano rayuwarsa na cikin hadari.

A Kanoni hakan ya sha faruwar lokacin yaki neman zabensa, akwai randa sai da ya tsere cikin 'yan sanda da sojoji saboda hayaki mai sa hawaye da harsashi da aka yi ta harba wa.

Sai dai hukumomi sun ce sun yi hakan ne saboda tarwatsa taron mutane da suka ki bin dokar annobar korona.

'Yana fahimtarmu'

Marion Kirabo mai shekarar 23 da ke karantar shari'a ita ma mai goyon bayansa ce kuma tana son tsayawa takarar kansila.

"Tun kafin shigarsa siyasa yana daya daga cikin matasan da za ka iya yaba musu," in ji ta.

"Musamman idan kana sauraron kidansa, za ka fahimci ya san matsalolin rayuwa da matasa ke fuskanta, musamman matasan da ke yankin masu rangwaman gata."

Bobi Wine yana fatan yin abin da babu wani dan adawar Yoweri Museveni ya taa yi a shekaru 35

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Bobi Wine yana fatan yin abin da babu wani dan adawar Yoweri Museveni ya taa yi a shekaru 35

Lokacin da shugaba Museveni ya karbi mulki a 1986, Bobi bai fi shekara hudu ba a duniya, kuma a lokacin yana rayuwa ne a Kanoni.

Tsakiyar Uganda ya zama wani fagen yakin sari ka noke yanda ya yi sanadiyar fitowar 'yan tawayen Museveni, da kuma bangaren siyasa na National Resistance Movement NRM kan mulki.

Kakan Bobi Yozefu Walakira, na daga cikin 'yan tawayen da ke aikin wucin gadi lokacin-lokaci da rikicin ke ta shi.

Walakira ya mutu a lokacin yaki basasa bayan wani rauni da ya ji lokacin da aka sanya bam a gidansa - a wani hari da ya kashe mutum uku cikin iyalansu.

Daga nan ne Bobi suka koma Kampala da mahaifiyarsa.

A 2017, mawakin ya koma harkar siyasa a matsayin wata damar rayuwarsa ta gaba.

"Kinsan akan me nake wakata, kan abubuwan da suka shafi matsalolin rayuwar mutane ne," kamar yadda ya shaida wa wakiliyar BBC.

"Don haka sai ya zama kamar yakin neman zabe nake yi ta waka ta."

Wakarsa ta Tuliyambala Engule na daya daga cikin wakokinsa na kamfe.

Ya samu nasarar lashe zaben cike gurbin na dan majalisar Kyadodondo ta gabas.

Idan za a kwatanta tsakanin matashin da kuma Mista Museveni - ta bangaren cika ido da jini a jika da karfafa gwiwar matasa za ka ga Bobi ba zai sha ba.

Kwamandan 'yan tawayen ya karbi mulki ne yana dan shekarar 41 ya kuma yi alkawarin tabbatar da tsaro da kuma samar da tattalin arziki mai karfi.

'Yana da karancin manufofi'

A karshen shekarar, ta shiga jam'iyyar Bobi Wine amma ta fita saboda abin da ta kira karancin manufofi a kasa.

"An tambaye shi game tsa tsarin da yake da shi lokacin da yake shugaba, ta ce tana nufin a watan Yulin 2020 lokacin da Bobi yake tattaunawa da wani gidan wani radiyo a kasar.

"An kuma tambaye shi ko a hagu ko dama yana da wasu manufofi sai ya ce aa zai yi aiki da abin da yake kasa ne. Hakan kuma bai yi wani ma'ana ba a waje na."

Bayan wannan garugarumin taron da yake baibaye da shi, kamar wanda aka yi a Kanoni, yana da wahala ka fadi yawan goyon bayan da yake da shi ko kuma ihun da ake yi masa zai zama kuri'a anan gaba. Saboda tsarin zabensu na da matukar ka'ida.