GSS Ƙanƙara: Ɗalibai sun wayi gari cikin 'ƴanci

Gwamnatin Zamfara ta ce ɗaliban sakandiren Kankara da ta taimaka wajen ganin an sako su ta ce yanzu haka suna kan hanyarsu ta zuwa Katsina daga birnin Gusau.

A daren Alhamis ne gwamnatin Katsina ta tabbatar wa BBC cewa an sako ɗaliban, bayan sun shafe kwana shida a hannun mutanen da suka yi garkuwa da su.

Labarin sako ɗaliban ya sanya farin ciki da annushuwa a fuskoki da zuƙatan al'ummar Najeriya musamman iyayen yaran bayan shafe kwanaki hankula tashe.

Sakataren gwamnatin jihar Zamfara, Bala Bello Maru, ne ya jagoranci karɓo ɗaliban sakandiren Ƙanƙara, bayan shiga tsakanin da Gwamna Bello Matawalle ya yi da masu garkuwar.

Bala Bello ya shaida wa BBC cewa yaran suna cikin ƙoshin lafiya kuma sun kwana lafiya ba tare da samun ko guda cikin yanayi na rashin lafiya ko wata matsala ba.

Yadda aka karɓo ɗaliban

Tawagar gwamnatin Zamfara ce ta karɓo yaran a hannun sojojin da suka fito da su daga dajin Tsafe da ke Zamfara da misalin ƙarfe 6 na yammacin ranar Alhamis.

Sannan aka wuce da su barikin sojoji da ke birnin Gusau domin su rintsa kafin daga bisani a dangana da su Katsina, da wayewar gari.

Gwamna Matawalle na Zamfarar, ya ce sun bi hanyar sulhu ne, wacce ta basu nasarar ceto yaran ba tare da an kai wani lokaci mai tsawo ba.

Sannan ya tabbatar wa BBC cewa yara 344 aka sako, bayan samun jagorancin zaman sulhu ƙarƙashin shugaban Miyetti Allah na ƙasa.

"An yi zaman sulhu akalla sau uku kafin a kai ga cimma dai-daito ga sakin ɗaliban, da farko ya ci tura, haka zama na biyu amma a ƙarshe an yi nasara."

A hannun Boko Haram aka karbo yaran?

Gwamna Matawalle ya ce ba a a hannun Boko Haram aka karɓo shu ba, daga hannun fulani ƴan bindiga aka karbo ɗaliban.

Ya ce a zaman sulhun da suka yi da su, sun gindaya musu wasu matsalolin da ke ci musu tuwo a ƙwarya wanda kuma aka alƙawarta za a sasanta.

Daga cikin ƙorafin fulani akwai yadda ake kashe musu shanu da cin zarafinsu daga ƴan banga ko ƙato da gora.

Kuma ya ce a shirye yake a ci gaba da ƙoƙari irin wannan wajen sulhu don tsare ƙasa, kuma duk wanda ya ƙi zai fuskanci fushin hukuma, in ji Matawalle.

An biya kuɗin fansa?

Ƴan ƙasa da dama na diga ayar tambaya kan yadda aka sako waɗannan ɗalibai, lura da dagar da aka sha a baya lokacin sace ƴan matan Chibok da Dapchi.

Akwai masu ganin abu ne mai wuya a sako wadannan ɗalibai haka kawai.

Sai dai bayanan da muka samu daga ɓangarorin gwamnatin Zamfarar da na Katsina na tabbatar da cewa ba a biya ko sisin kwabo ba a matsayin kuɗin fansa.

Kuma gwamna Matawalle ya ce kawai an tattauna batutuwan da za su kare afkuwar irin wannan garkuwa ne a nan gaba, da kuma sauraron koken fulanin da suka sace ɗaliban.

Gwamnan ya kuma danganta irin wannan matsaloli na tsaro da ake samu da rashin haɗin-kai, inda ya yi gargadi cewa aiki tare da sauraron koken juna ne kawai zasu kuɓutar da Najeriya.

Sharhi, daga Umaymah Sani Abdulmumin

Ƙafin samun labarin sako wadanan ɗalibai da fari ƙungiyar Boko Haram ta sako wani bidiyo da ke nuna ɗaliban cikin jeji suna roƙon a ceto su.

Sai dai bayan lokaci ƙalilan da yaduwar wannan bidiyo, sai ga labarin sako yaran daga gwamnatin Katsina.

Kuma dai waɗanda suka shiga tsakani da nasarar kubutar da yaran sun tabbatar ba a hannun Boko Haram suke ba.

Wannan yanayi yazo da sarƙaƙƙiya da ɗiga ayar tambaya kan yada Boko Haram ta samu bidiyon da take ikirarin cewa ɗaliban ƙanƙara na hannunta.

Ko da yake, akwai masu sharhi da tun farkon sace ɗaliban suke cewa babu mamaki mayakan Boko Haram na aiki tare da, ko su fulanin masu garkuwa suna aiki da Boko Haram.

Haka zalika tana iya yiwuwa Boko Haram tayi amfani da wannan damar ce wajen yaɗa farfagandarta.

Burin ƴan ƙasa da dama shi ne inganta tsaro nan bada jimawa ba domin gudun abin da ke iya zuwa ya dawo.

Fatan da ake shi ne idan har ƙubutar da yaran ƙanakara an yi nasara ne ta hannun shugabannin ƙungiyar fulani ta Miyetti-Allah, to wannan hanya zata iya shawo kan matalar satar mutanen da ake yawaita zargin fulanin da kuma hare-haren da 'yan bindiga ke kai wa wasu ƙauyuka.

Abin da Buhari yace kan sako ɗaliban Ƙanƙara

To tuni dai shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi maraba da labarin sakin ɗaliban da aka yi inda ya bayyana sakin nasu a matsayin wani yanayi da zai kwantar da hankulan iyayen ɗaliban da ma al'umma na ciki da wajen ƙasa.

A cikin wani ɗan taƙaitaccen bayani da yayi jim kaɗan bayan sanar da sakin daliban, shugaba Buhari ya bayyana godiyarsa ga al'ummar ƙasar dama sauran masu ruwa da tsaki da suka taka gagarumar rawa wajen tabbatar da ganin an kuɓutar da ɗaliban.

Shugaban na Najeriya ya yaba da abin da ya kira haɗin kai da jajircewar da aka samu a tsakanin gwamnatin Katsina da Zamfara da kuma sojojin da suka ja gaba wajen sako ɗaliban.

Kazalika ya yabawa hukumomin leƙen asiri na ƙasa da kuma jami'an 'yan sanda wajen bayar da kyakkyawan yanayin da aka bi har aka sako daliban.

Shugaba Buharin yace gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari da rundunar sojin ƙasa sun yi ƙoƙari matuka gaya a don haka ko da aka samu labarin sakin ɗaliban ya yi musu murna ƙwarai da gaske kuma wannan ya nuna cewa sojojin sun san aikinsu.

Dangane da batun sauran mutanen da aka sace ake kuma riƙe da su har kawo yanzu, a wasu wurare, shugaban na Najeriya ya ce gwamnatinsa na sane da irin nauyin da ke kanta na kare rayuka da kuma dukiyoyin al'ummar Najeriya.

Daga nan shugaban ya buƙaci yan Najeriya da su ƙara haƙuri kuma su kasance masu adalci ga gwamnati yayin da suke ƙoƙarin magance matsalolin tsaro da cin hanci da rashawa.

Kazalika shugaban na Najeriya ya nunar cewa gwamnatinsa na sane da cewa an zaɓe tane domin ta magance waɗannan matsaloli da ake fama da su a ƙasa.

Shugaban na Najeriya ya nuna irin nasarar da gwamnatinsa ta samu wajen magance matsalolin tsaro a yankin kudu maso kudancin Najeriya da kuma na arewa masa gabashin kasa.

Ya ce a yanzu matsalar a arewa maso yamma take, kuma gwamnatinsa na nan na ƙoƙari wajen magance ta a yankin.

Daga ƙarshe shugaban na Najeriya ya yi addu'ar samun lafiya ga ɗaliban da aka sako waɗanda ya ce sun fuskanci duk wata wahala a yayin da suke tsare a wajen 'yan bindigar da suka sace su.

Wasu labaran masu alaƙa