Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Muhammadu Buhari: Shugaban Najeriya na shan yabo da suka a yayin da ya cika shekara 78 da haihuwa
A ranar Alhamis, 17 ga watan Disamban 2020 ne Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ke cika shekara 78 da haihuwa. Jama'a da dama ne a shafukan sada zumunta da kuma jaridun ƙasar ke taya shi murnar zagayowar ranar haihuwarsa da san barka kan cewa sun samu shugaba kamarsa.
A wani ɓangaren kuma, wasu sukarsa suke yi inda suke Allah-wadai da mulkinsa da kuma da-na-sanin zaɓarsa a matsayin shugaba.
Akasarin irin waɗannan zantuttuka da ra'ayoyin akan tattauna su ne a shafukan sada zumunta musamman Twitter, inda masu shaguɓe ke yi, masu yabo da suka duk ke cin karensu babu babbaka.
Mai magana da yawun shugaban ƙasar, Femi Adesina, ya rubuta wata doguwar buɗaɗɗiyar wasiƙar taya shugaban murnar cika shekara 78 da haihuwa.
Wasiƙar na cike da kalamai na yabo inda kuma Mista Adesina ya rinƙa wasa gwanin nasa da kwarzantasa da kuma bayyana irin alkhairan da ya samu ta sanadiyyar Shugaba Buharin.
A wani ɓangare na wasiƙar, martani ya rinƙa mayar wa waɗanda ba su fahimci shugaban ba da kuma masu adawa da shi, inda ya rinƙa zaro kalaman da ya danganta su da shiririta yana mayar da martani a kansu.
Wane martani Adesina ya mayar kuma me 'Yan Twitter ke ce masa?
A buɗaɗɗiyar wasiƙar da Mista Adesina ya rubuta wa Shugaba Buharin, ya ambato yadda wasu suka rinƙa zargin cewa an sauya shugaban an kawo me kama da shi a 2017 bayan rashin lafiyar da ya yi.
Mista Adesina ya nuna rashin jin daɗinsa kan wannan batu inda ya ce abin takaici ne da za a ce har wasu masu ilimi sun yarda da wannan batu, amma a wasiƙar, ya kawo wasu hujjojin da a cewarsa suka gamsar da shi kan cewa ba a sauya shugaban ba kuma shi ne dai Buharin da ya sani a baya.
A martanin da wannan ya mayar ya ce "Femi Adesina yana so mu yarda cewa Buhari ba Jubril bane, duk da rashin kunyar da aka yi a watannin da suka gabata. Ba shanu muhimmanci fiye da mutane da saka ƙasa cikin bashi da kuma taimakawa a gina matatar mai a Jamhuriyyar Nijar".
Tun a farkon wasiƙar, Mista Adesina ya nuna cewa da 'yan Najeriya sun san irin shugaban da suke da shi da kuma sanin muhimmancinsa, da sun sauya tunaninsu a kan shugaban sun rinƙa tattalinsa, in ji shi.
Wannan cewa ta yi duk da cewa Femi Adesina ya ce 'yan Najeriya ba su san irin shugaban da suke da shi ba, "ya manta cewa hanya ɗaya ta sanin mutum ita ce ta ayyukansa". A cewarta, gwara da Adesina bai ce ayyukan Buhari ba a bayyana suke ga 'yan Najeriya ba.
Da alama wannan kuma na goyon bayan Femi Adesina inda ya ce batun Adesina ya fito ya yi ƙarin haske kan cewa mutumin da yake Aso Rock Shugaba Buhari ne ba Jubril daga Sudan ba, babu amfani. "Idan za ku yarda za a iya ɓoye mutuwar shugaban ƙasa, to za ku iya yarda da komai." a cewarsa.
Cikin wasu kuma da suka aika da saƙon yabon ga shugaban, akwai Festus Keyamo, wanda shi ne ƙaramin ministan ayyuka a Najeriya, ya wallafa saƙon yabonsa a shafinsa na Twitter kuma ba a bar shi a baya ba wurin kwarzanta gwanin nasa.