EndSARS: Hillary Clinton ta yi kira ga Buhari da sojojin Najeriya kan kashe masu zanga-zanga a Legas

Hillary Clinton

Asalin hoton, Reuters

Lokacin karatu: Minti 3

Tsohuwar ƴan takarar shugaban ƙasa a Amurka Hillary Clinton, ta yi kira ga shugaban Najeriya da kuma sojin ƙasar su daina kashe matasa masu zanga-zangar EndSARS.

An ta yaɗa hotunan bidiyo a kafofin sadarwa na intanet da ke nuna yadda sojoji suka buɗe wa masu zanga-zanga wuta a Legas.

Tsohuwar sakatariyar harakokin wajen Amurka Hillary Clinton ta wallafa saƙon kira ga shugaban na Najeriya ne a Twitter tare da ƙirkirar wani maudu'i #StopNigeriaGovernment.

Sai dai kuma rundunar Sojin Najeriya ta ƙaryata rahotannin da ke cewa sojoji sun buɗe wa masu zanga-zanga wuta a Legas.

Kauce wa X, 1
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 1

A ranar Talata ne gwamnatin Legas ta sanya dokar hana fita ta sa'a 24, bayan zanga-zangar da aka fara ta lumana ta rikiɗe ta koma rikici.

Ba a tantance adadin waɗanda suka mutu ba a ranar Talata a Legas, amma ƙungiyar Amnesty Interntional a Najeriya ta ce tana da sahihan shaidu masu tayar da hankali da suka tabbatar da an yi amfani da ƙarfi da suka haddasa kashe-kashen.

An zargi sojojin Najeriya ne da buɗe wuta kan dubban masu zanga-zangar EndSARS a unguwar Lekki a Legas.

Masu zanga-zangar sun bijere wa dokar hana fita da gwamnati ta sanya wacce ta fara aiki tun ƙarfe huɗu na yammacin Talata.

Abin da duniya ke cewa

Ɗan takarar shugaban ƙasar Amurka Joe Biden, ya yi kira ga Shugaban Najeriya da kuma sojojin ƙasar da su daina amfani da ƙarfin da ya wuce kima wajen muƙushe masu zanga-zanga.

"Ina jajantawa ga waɗanda suka rasa masoyansu a wannan rikicin. Dole ne Amurka ta goyi bayan ƴan Najeriya masu gudanar da zanga-zangar lumana domin kawo sauyi ga 'yan sandan ƙasar da dimokraɗiyya da kuma cin hanci a ƙasar," in ji wata sanarwa da Mista Biden ya fitar.

Mataimakiyar sakatare janar na Majalisar Ɗinkin Duniya Amina Mohammed kuma tsohuwar minista a gwamnatin Buhari ta yi kiran dakatar da keta hakkin ɗan Adam tare da jaddada muhimmancin mutumta ƴancin masu zanga-zanga.

Kauce wa X, 2
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 2

"Ni ma na jaddada kiran da sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya ya yi kan mutunta masu zanga-zangar lumana," in ji Amina.

Tsohon kaftin din Super Eagles yana cikin waɗanda suka yi kiran dakatar da kashe masu zanga-zangar, kamar yadda ya rubuta a shafinsa na Twitter ɗauke da maudu'in EndSARS inda ya ce "a yi wa Najeriya addu'a da dakatar kisa."

Kauce wa X, 3
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 3

Kaftin ɗin Super Eagle Ahmed Musa, ya yi jaje ga waɗanda suka rasa rayukansu ga abin da ya kira kisan gillar da ta faru ranar Talata. "Abin takaici ne cewa mun rasa ƴancin yin zanga-zangar lumana. Ya kamata gwamnati ta yi abin da ya dace domin kawo ƙarshen wannan kariyar zuciya."

Kauce wa X, 4
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 4

Dan wasan Super Eagles na Manchester United Odion Jude Ighalo shi ma ya yaɗa bidiyo a shafinsa na Twitter inda ya kira abin ke faruwa a Najeriya a matsayin wani abin baƙin ciki. A cikin kalamansa, Ighalo ya soki gwmanatin Najeriya inda ya ce "gwamnati ta kunyata ƴan Najeriya a idon duniya. Ya kuma yi kira ga Majalisar Ɗinkin Duniya da gwamnatin Birtaniya su ɗauki mataki kan abin da ke faruwa a Najeriya."

Kauce wa X, 5
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 5

Mawaƙiyar Amurka Rihanna ita ma ta wallafa saƙo a Twitter kan zanga-zangar EndSARS inda ta wallafa hoton turar Najeriya da jini tana bayyana damuwa kan abin da ta kira ci gaba da azabtarwa da kisa da ke faruwa a duniya, "Wannan cin amana ne ga ƴan ƙasa, mutanen da aka ɗora wa alhakin tsaro sun koma waɗanda ake tsoro," in ji mawaƙiyar.

Kauce wa X, 6
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 6