EndSars: Jihohin Najeriya da zanga-zanga ta rikiɗe zuwa tarzoma

Gwamnonin jihohi da dama a Najeriya sun sanya dokar hana fita ta tsawon sa'oi 24 sakamakon rikiɗewar da zanga-zangar SARS ta yi zuwa tarzoma.
Gwamnonin wadanan jihohi sun ce sun sanya dokar hana fita ne sakamakon yadda ɓata-gari ke amfani da damar zanga-zangar SARS wajen haifar da rikici da kai hare-hare.
Ga jihohin Najeriya da aka ƙaƙaba wa dokar hana fita saboda zanga-zangar #EndSARS

Legas
A ranar Talata 20 ga watan Oktoba 2020 ne, gwamnan Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya sanar da dokar hana fita ta ba dare ba rana a faɗin Jahar, wadda ta soma aiki daga karfe 4 na yamma.
Sai dai daga baya ya tsawaita dokar zuwa 9 na dare domin bai wa mutanen da suka je aiki ko fita sana'a damar koma wa gidajensu saboda cunkoson ababen hawa.
Gwamnan ya ce ya dau wannan matakin ne saboda ganin yadda 'ƴan daba ko wasu ɓata gari ke amfani da zanga-zangar EndSars wajen aikata muggan ayyuka a faɗin jahar.
Mista Sanwo-Olu, ya ce ma'aikatan da ya zama wajibi su fita kaɗai aka amince a gani a kan titi.
Sai dai masu zanga-zangar sun bijirewa wannan umarni, inda suka ci gaba da gangamin su a titin Lekki lamarin da ya kai ga sojoji sun buɗe musu wuta.
Rahotanni sun ce da dama sun jikkata sannan akwai fargabar rasa rayuka.

Asalin hoton, Other
Abia
Gwamnan Abia Okezie Ikpeazu, shima ya sanya dokar hana fita ta ba dare ba rana a Aba da Umuahia daga karfe 6 na yamma har sai abin da hali ya yi.
Gwamnan ya ce wannan wani mataki ne na kare rayuka da dukiyoyin al'umma.
A cewar sanarwar kwamishinan yaɗa labarai, John Okiyi Kalu, 'ƴan daba sama da 30 dauke da makamai sun kai wa ginin ;ƴan sanda hari a titin Azikiwe.
Sun kashe ɗan sanda guda da kwace bindigogi da harsashai, sai dai an cafke mutum guda cikin wadanda suka kai harin bayan ya samu rauni daga harbin bindiga.

Asalin hoton, ScREENSHOT
Edo
A ranar Litinin 19 ga watan Oktoba 2020, gwamnatin Edo ta sanya dokar hana fita har sai abin da hali ya yi.
Dokar ta soma aiki ne daga karfe 4 na yamma.
Gwamnan jihar ya ce matakin sanya dokar ya zama dole ganin yadda ɓata gari ke haifar da kai hare-hare kan mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba da sunan zanga-zangar EndSARS.
Wannan yanayi har ya kai ga mutane dauke da makamai sun kai hari gidan yari tare da sakin fursunonin da ke daure.

Filato
Gwamnan Filato, Simon Lalong, shima ya sanya dokar hana fita a Kudancin Jos da kananan hukumomin arewacin Jos wadda ta soma aiki daga karfe 8 na daren Talata, 20 ga watan Oktoba 2020.
Gwamnati a wata sanarwa da ta fitar, ta ce a 'ƴan kwanakin da suka gabata zanga-zangar lumana ta #ENDSARS da ake gudanar wa sannu a hankali ta zama rikici, inda aka samu ɓata gari da ke amfani da zanga-zangar wajen kai hari da cin zarafin 'ƴan gari da ke harkokin gaban su.
Wannan yanayi ya shiga mummunan yanayi inda aka samu mutane cikin masu zanga-zangar da ke ta'adi da kone-konen motoci da farfasa shaguna a titin Ahmadu Bello da kona wani wajen ibada da ke titin Gyero a yankin Bukuru. Sannan akwai mutane 3 da suka mutu.
Ekiti

Asalin hoton, KFayemi
Ɓata gari sun yi wa zanga-zangar EndSARS kane-kane abin da ya tilasta wa gwamnan Kayode Fayemi umarta dokar hana fita ta sa'a 24 a faɗin Ekiti.
Dokar ta shafi kowanne fanin na jihar wadda ta soma daga karfe 10 na daren Talata, 20 ga watan Oktoba, 2020.
Gwamnatin Ekiti ta nuna damuwarta kan yadda gangamin #EndSARS da aka soma a cikin lumana ya ƙazance a sassan Jihar.
Osun da Imo
An sanya irin wannan doka ta hana fita a jihohin Imo da Osun.

Zang-zanga ta ƙazance Kano
Zanga-zanga ta zama rikici a Kano tsakanin masu zanga-zanga da wasu 'ƴan daba.
'Yan dabar ne suka fara kai wa masu zanga-zangar hari a dai-dai makarantar horas da sojojin sama a can hanyar filin jirgin sama na malam Aminu, sun tarwatsa masu zanga-zanga tare da yi musu duka da sare-sare, an kuma kashe mutum 2 a cewar masu zanga-zangar.
Hakan ya tunzura su suka rufe hanyar da za ta kai ka Sarkin Yaki a unguwar Sabon Gari. Daga nan su ma suka dauko makamai da katakwaye da adduna suka tare hanya suka kona tayoyi.
An kona motoci 2 da farfasa wasu da dama an kuma fasa kantin cin abinci na Chicken republic amma 'yan sanda sun tseratar da ma'aikatan wajen.
A yanzu dai lamarin ya lafa, amma ana ci gaba da zaman dar-dar a yankin Sabon Gari. Kuma ba a sanya dokar hana fita a jihar ba.
Tun da farko a ranar Talata Babban Sifeton 'ƴan sandan Najeriya ya umarci baza 'ƴan sandan kwantar da tarzoma a duk faɗin ƙasar.
Sanarwar Muhammad Adamu, na zuwa ne yayin da ake samun ƙaruwar tashin hankali a wasu jihohi sakamakon zanga-zangar nuna adawa da cin zalin da ake zargin jami'an 'yan sanda na yi.










