Zaɓen Amurka na 2020: Ƴan duba, dandazon jama'a da cire shafin Tiktok na taka rawa a zaɓen Amurka

Asalin hoton, Getty Images
Yayin da ya rage kwana goma sha biyar a gudanar da zaben Amurka, ga halin da takarar ke ciki.
Mutane da dama sun yi watsi da shawarwarin likitoci wajen taruwa a wurin saukar jirage a filayen jiagen sama na jihohi huɗu da Shugaba Trump ya ziyarta don yakin neman zabe, a daidai lokacin da wasu manyan taurari suka bayyana goyon bayansu gare shi, a gefe guda kuma shafin Tiktok ya sauke wasu hotunan bidiyo da aka yi ta yi wa shugaban ɓatanci a ciki.

Abubuwa huɗu dake faruwa

Asalin hoton, Getty Images
1. Shugaba Trump ya karaɗe jihohi huɗu a kwana biyu yayin kamfe a karshen mako, sannan a ranar Litinin ya kai ziyara jihar Arizona, jihar da ke da masu zaɓe 'yan Latin da yawa.
2. Joe Biden ya yi balaguro tare da jikarsa Finnegan zuwa jihar North Carolina, inda yake hanƙoron lashewa saboda ya san muhimmancinta ga duk ɗan takarar da yake so ya samu nasara.
3. Bayan fitattun mutane kamar su Taylor Swift, da Dwayne wato "The Rock" da Cardi B da suka bayyana goyon bayansu ga Biden, a yanzu wasu taurari kamar su Kid Rock, da Kirstie Alley da Jon Voigt sun sanar da mara wa Trump baya, ko da yake ba su sanar da hakan ba a shafukansu na sada zumunta.
4. Shafin TikTok ya cire wasu bidiyoyi da a ciki aka yi wa Trump ɓatanci, bayan wani binciken BBC ya gano cewa biyan waɗanda suka watsa bidiyon aka yi.

Asalin hoton, TikTok

Abin da yasa taron jama'a da yawa yafi muhimmanci ga Trump fiye da kowanne lokaci
Kusan kullum shugaban na ziyartar aƙalla jiha ɗaya ko biyu, ko ma uku.
Yana baya a ƙuri'ar jin ra'ayin jama'a da kuma tara tallafin yaƙin neman zaɓe, amma hakan bai hana shi tara mutane da yawa a yakin neman zaɓe ba.
Waɗannan hotuna da ke ƙasa na nuna abin da ya sa kwamitin yaƙin neman zaɓensa ke maraba da hakan.
Amfani da taro don kore sakamakon ƙuri'ar jin ra'ayin jama'a:
Ganin hulunan MAGA, wato ciyar da Amurka gaba da magoya bayan shugaban ke sanyawa na ƙara wa kwamitin yaƙin neman zaɓensa ƙwarin gwiwar ƙalubalantar ƙuri'ar jin ra'ayin jama'a.
Ɗansa Eric ya wallafa wani hoton yaƙin neman zaɓe da ya ɗauka a jihar Georgia a shafinsa na Tuwita, yana cewa ''Kuri'ar jin ra'ayin jama'a karya ce tsagwaronta''.

Asalin hoton, Getty Images
Magana ce kawai ta ƙwarin gwiwa:
Trump da magoya bayansa na samun ƙwarin gwiwa da irin lokutan nan masu jan hankali da yake barkwanci yayin magana, har ma a riƙa sowa.
Don haka ne suke hallara a taronsa, duk da kiraye-kirayen da masana ke musu cewa kar su taru a cikin jama'a saboda korona.

Asalin hoton, Reuters
Sai dai duk da wannan ƙwarin gwiwa, masana na ganin ba abinda zai canja musamman wajen fitowar mutane a ranar zabe.

Wahayi da kafe 4.30 'An shaida min cewa' ....

Asalin hoton, MANDEL NGAN
Daya daga cikin muhimman abubuwan da suka faru a karshen mako shi ne wa'azin da wani fasto na Cocin Las Vegas ya yi.
Da yake magana ga shugaban, Fasto Denise Goulet ya ce ''Da misalin kafe 4.30, Allah ya shaida min cewa zan bai wa shugabanku damar shaƙar iska a karo na biyu; yana magana dangane da kamuwa da cutar korona da Trump ya yi a kwanakin baya.
Ya kuma ci gaba da magana, har ma ya ce ''Zai sake zama shugaban ƙasa a karo na biyu''.
Har yanzu Trump na gaban Biden a ƙuri'ar jin ra'ayin jama'a da tazara mai yawa tsakanin kiristoci mabiya ɗarikar Evanjalika, sannan bincike na baya-bayan nan ya nuna yadda shugaban ke ƙara samun goyon baya a wajensu.
Hakan kuwa ba ya rasa nasaba da yin abin da ya fi damunsu, kamar naɗa alƙalai masu tsattsauan ra'ayi a Kotun Ƙoli.












