Yadda alamomin jam'iyyu suka fito da wayewar siyasar Afirka

Asalin hoton, AFP
Cikin jerin wasiƙun da muke samu daga 'ƴan jarida daga Afirka, Joseph Warungu, mai koyar da aikin jarida da harakokin watsa labarai, ya duba dalilin da ya sa launuka da alamomi ke da muhimmanci wajen neman mulki a Afirka yayin da nahirar ke tunkarar kakar zaɓe.

Ka tuna "red red wine?" A'a, ba abin da ke cikin kwalbar da ke ba ka damar warware tunaninka ba.
Ina magana kan Red Red Wine… ɗaya daga cikin fitattun waƙoƙin rege na baturen Birtaniya UB40. Ta kai matsayi na ɗaya a Birtaniya da Amurka a 1983.
Shekaru 37 bayan haka, Red Red Wine ta yi tasiri sosai ga mawaƙin Uganda Bobi Wine wanda ya zama ɗan siyasa.
Ɗan majalisa, wanda asalin sunansa shi ne Robert Kyagulanyi wanda da wahala ka gan shi ba tare da jar hula ba, yana son tsayawa takarar shugaban ƙasa a zaɓe mai zuwa.
Amma Bobi Wine yanzu yana fuskantar barazana bayan da hukumar zaɓe ta haramta wa jam'iyyarsa yin amfani da launin ja a zaɓe, tana mai cewa wata jam'iyya na amfani da launin ja.


Ba za a iya tantance ƙarfin amfani da launi ba ko alamomi a yaƙin neman zaɓe a ƙasashen Afrika.
"Sauƙin alama, ya fi taimaka wa jam'iyyu saurin isar da saƙonsu ga masu zaɓe. Wasunsu sun yi tunanin cewa ya fi kyau a yi amfani da alamar da take da alaƙa da rayuwa da fatan da mutane suke da shi," a cewar Dakta Isaac Owusu-Mensah, babban malami da ke koyarwa a ɓangaren kimiyyar siyasa a jami'ar Ghana.
Ya yi amfani da manyan jam'iyyun siyasa biyu da ke son lashe zaɓen watan Disamba a matsayin misali.
"Jam'iyyar adawa ta NDC tana da alamar lema, kuma ma'anar ita ce za ka iya shan inuwar lema, ko a cikin mawuyacin hali," in ji Dakta Owusu-Mensah.
"Jam'iyya mai mulki ta NPP a ɗaya ɓangaren, tana da alamar giwa da ke da girma. Za su iya maganin dukkanin matsalolin da suka shafe ka. Idan kana cikin matsala, ka je ka raɓi giwa za ka samu mafita."
'Ja na nufin rayuwa'
Dr Mshai Mwangola, wani masani a fagen wasan kwaikwayon a Kenya, ya ce yawancin launukan kasashen yamma suna da ƙarancin ma'ana ta fuskar alama.

Misali launin ja yana da alaƙa da jam'iyyar adawa ta Labour a Birtaniya da kuma jam'iyyar Republican ta Amurka - haka kuma jam'iyyar Conservatives ta Birtaniya na amfani ne da launin shuɗi haka ma jam'iyyar Democrats ta Amurka.
"Nan a Afrika, mutane sun san cewa waɗannan launikan suna cike da ma'ana… muna da wayewar kai sosai kan siyasa ta fuskoki da dama," in ji Dakta Mwangola.
Ana karanta waɗannan ma'anonin a tutocin ƙasashen Afirka da yawa inda aka yi gwagwarmayar 'yanci kuma mutane suka mutu, kamar Kenya.
"Launin ja yana nuna alamar jini da aka rasa; baƙi yawanci yana nuna alamar mutanen ƙasa yayin da kuma kore ke nuna alamar muhalli ko ƙasa da aka yi wa gwagwarmaya," a cewarta.
Wannan ma shi ne ra'ayin Dakta Owusu-Mensah.

Kakar zaɓe a Afirka
- Guinea: 18 ga Oktoba
- Seychelles: 22 zuwa 24 ga Oktoba
- Tanzania: 28 ga Oktoba
- Ivory Coast: 31 ga Oktoba
- Ghana: 7 ga Disamba
- Jamhuyar Afrika ta tsakiya: 27 ga Disamba
- Nijar: 27 ga Disamba
- Uganda: 10 ga Janairu zuwa 8 ga Fabrairun 2021

Hukumar ta zaɓi ƴaƴan itace biyu da aka fi sani - lemo da ayaba. Amma ƴan Kenya suna ganin suna tattare da ma'ana.
Yaƙin neman zaɓen ya fuskanci fannoni da yawa na gwagwarmayar siyasa, har da na ban dariya game da abin da ayaba za ta iya yi wa lemo da akasin haka.

Asalin hoton, AFP
Daga ƙarshe masu lemo ne suka yi nasara, kuma ƙuri'ar jin ra'ayin jama'a da gwamnati ke goyon baya aka yi watsi da ita. Masu ayaba ba su yi nasara ba.
Ƴan siyasar da suka yi nasara a ƙuri'ar suka ɗauki lemo a matsayin sunan jam'iyyarsu.
A yau jam'iyyar Orange Democratic Movement (ODM), ta tsohon Firaminista Raila Odinga, ita ce babbar jam'iyyar adawa a Kenya.
An haramta alamun maita
An yi amince da dukkanin alamomi a zaɓe kamar yadda muka gani a zaɓen Zimbabwe na 2018.

Wasu labaran da za ku so ku karanta:

Hukumar zaɓen Zimbabwe (Zec) ta haramta abubuwa da dama daga tambarin ƴan takara da suka ƙunshi dabbobi da makamai.
Za ka iya sa alamar bindiga a tambarinka amma ban da damisa ko giwa.
A cikin hikimarta, Hukumar Zec ta san cewa akwai zaɓuka da yawa a Afirka waɗanda ba ta hanyar ƙuri'a aka lashe su ba amma ta hanyar "juju" ko maita, wanda ake kira maguɗi.
Don haka maciji da mujiya - wadanda ke da alaƙa da tsafi a Zimbabwe - suna cikin jerin sunayen da aka haramta.
Dakta Owusu-Mensah na ganin alamomi suna da tasiri sosai, inda galibi suke wakiltar ɗan takara.
"Na fito daga wata mazaba a arewacin Ghana inda muka yi hira da mutanen yankin game da wanda za su zaɓa a zaɓe mai zuwa. Kashi 95 daga cikinsu sun yi amfani da alama me ta ko giwa ko lema. Babu wanda ya ambaci sunan jam'iyya ko dan takara."


Lokacin da na girma a ƙauyenmu a yankin tsakiyar Kenya, na yi tunanin ɗan majalisarmu mafi daɗewa sunansa "Tawa" ma'ana fitila a harshenmu.
Saboda fitila ce alamarsa a zaɓen. Idan tawagarsa suka shiga ƙauye, dukkanin yankin za ka ji ana ta yayata "Tawa! Tawa!"
Amma dole na amsa cewa, fitilarsa ta fara rage tasiri: domin bai bunƙasa iliminmu da ƙalubalen kiwon lafiya ba. Bai kawo wutar lantarki a yankin ba ko inganta hanyoyin da ba za a iya wucewa ba a lokacin damina.
Dakta Mwangola ya ce yayin da muke da ƙwarewa sosai wajen fito da ma'anar launuka da alamomi a Afirka, amma mun gaza ta hanyar samar da ci gaba.

Asalin hoton, AFP

Ƙarin wasiƙu daga Afirka:










