Sashen Larabci na BBC ya gano yadda ake azabtar da yara a makarantun allo a Sudan
Wani binciken kwakwaf na sashin larabci na BBC ya bankado wani irin cin zarafi da ake yi wa yara a makarantun allo a Sudan, inda ake yawan sanya wa yara 'yan shekara biyar mari, a daure su sannan shugabannin makarantar ko kuma mutanen da ke kula da su su lakaɗa musu duka.
A tsawon wata 18, dan jarida, Fateh Al-Rahman Al-Hamdani, ya dauki hotunan bidiyo a makarantu 23 a fadin Sudan.
Ya ga yadda ake yawan sawa yara sarka sannan ya shaida duka na cin zarafi da ake yi a kai a kai.
Wanda aka gudanar da binciken a kansa shi ne Mohammed Nder, wanda aka lakadawa duka har ya kusa mutuwa.
An tsare shi an ringa cuzguna masa tsawon shekara biyar a makarantarsa da ake kira Khalwa, ba abinci ba ruwa, sannan duk jikinsa na dauke da tabo.
Wannan bidiyon ya bibiyi yadda Muhammed Nadar yake warkewa da kuma yadda iyalensa ke fafutukar ganin an bi masa hakkinsa, domin sun gurfanar da mai makarantar wanda yake da karfin fada a ji a Sudan.
Mahaifiyar Mohammed Nader Fatim, ta yi tambayar cewa: Dole ne mu ringa sadaukar da 'yayanmu to girmama shugabannin addini?