Wasika daga Afirka: Abin da ya sa 'yan Najeriya ke kaunar masu damfara ta intanet

Romance scam

Asalin hoton, Getty Images

A jerin wasikinmu daga Afirka, marubuciya 'yar Najeriya Adaobi Tricia Nwaubani ta koka bisa yadda wasu matasan kasar ke kallon masu damfara ta intanet a matsayin ababen koyi.

A kwanakin baya hukumar binciken manyan laifi ta Amurka (FBI) na fitar da sunayen wasu 'yan Najeriya 77 a cikin jerin sunayen mutum 80 da ake zargi da yin damafara mafi girma ta intanet a tarihin Amurka.

Amma abu mafi daure kai ga 'yan Najeriya shi ne yadda aka tsare wani mashahurin dan kasuwa na kasa da kasa Obinwanne Okeke shi kadai.

Mista Okeke shi ne shugaban rukunin kamfanin Invictus Group wanda ke hada-hada a harkokin noma da gine-gine. A shekarar 2016 fitacciyar mujallar Forbes ta sanya shi a cikin jerin mayan 'yan kasuwa 30 'yan kasa da shekara 30.

Hukumomin Amurka na zargin Okeke da satar dala miliyan 11 (Fam miliyan takwas) a lokaci guda ta hanyar damfara ta intanet. Sai dai Mista Okeke ko Invictus Obi kamar yadda ake kiransa ya musanta zargin a gaban kotu a makon da ya gabata. Kuma yanzu haka yana can a tsare.

Hukumar FBI kan wallafa kamen da ta yi bayan shekaru, wanda yawanci akan gaggauta gurfanar da wadanda ake zargin kuma a yanke musu huncin dauri a wasu lokuta.

'Yan Najeriya a kasuwar wayoyin (Computer Village) inda ake hadahadar kayan wuta da wayoyin hannu a Ikeja dake jihar Legas a ranar 24 ga watan Fabrairu, 2015

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Najeriya na daya daga cikin manyan kasuwannin wayoyin hannu na kwamfyutoci a nahiyar Afrika

Amma hakan bai yi wani tasiri ba wurin hana matasan Najeriya shiga mummunar sana'ar damfara ta intanet wanda ke kara yawaita a fadin duniya.

A shekarun 1990 sadda 'yan Najeriya suka fara rasa ta'ido har suka fara damfarar turawa miliyoyin daloli, sai aka rika kiran damfarar da lakabin 419 - lambar shashen dokar penal code mai kula da laifukan damfara.

Kasancewar 'yan kasar mutane ne masu addini, har an gano cewa lamabr 419 ta yi daidai da littafin Psalm sura ta 41 aya ta 9 (wato Littafi na 9 Sura ta 41 aya ta tara). A cikin wannan ayar akwai bayanin yadda a yin cuta: "Na'am, aboki na da na amincewa kuma wanda ke ci a karkashina shi ke son ya cuce ni."

Amma a zamanin nan da yawanci ake damfanar ta intanet da sakonnin email da manhajojin aika sakonni, an koma kiran damfarar da suna Yahoo Yahoo.

Suna yaudarar jama'a cewa su manyan kamfanoni ne domin su samu bayanen sirrin mutanen. Jami'in hukumar FBI Michael Nail ya ce yin hakan shi ne fashin banki na zamani.

"Kana zaune a gidanka sanye da kayan barci, kana rike da laptop, sai ka iya yi wa banki fashi," inji shi.

Presentational grey line

Matakan kariya na intanet

Romance scam

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Fakewa da soyayya domin damfara
  • Masu damfara da sunan soyayya kan bibiyi bayanen jama'a su tattara bayanai kan arziki da yanayin rayuwa mai ban sha'awa da suke amfani da su su yaudari ja'ma'a
  • 'Yan sanda na iya bincike ko taimakawa, amma yawanci ba za su iya dawo maka da kudinka ba
  • Abu mai sauki ne ga 'yan damfara su badda sawunsu ta hanyar boye adireshin layin da suke amfani da ita ko yin amfani da layi mara rajista
  • Kar ka sake ka tura wa mutumin da baka taba haduwa da shi ba kudi ta intanet
  • Zurfafa tunani kafin tura bayanenka domin za a iya amfani da su a yaudare ka
Presentational grey line

Yawancin 'yan 419 da aka fara samu a Najeriya marasa ilimi ne.

Masu biye da su su ne matasa masu ilimi amma suke fama da rashin aiki a kasar saboda matsalolin tattalin arziki sakamakon tabarbarewar tattalin arzikin kasar da mulkin kama-karya na sojoji da kuma tsawon shekaru na facaka da dukiyar gwamnati.

Sun gano cewa 'yan damfara marasa ilimi na tara dukiya da martaba, don haka sai su ma masu ilimin suka biye musu.

Daga baya kuma sai aka samu wadanda ke ganin sha'awar 'yan damfarar.

'An kai samame a makarantar Yahoo Yahoo'

Sun gano cewa 'yan damfara sun kafa manyan kamfanoni da kudaden damfara har an wayi gari su ake gani a matsayin masu taimakon al'umma da manyan masu rike da mukamen 'yan siyasa.

Irin wadannan mutanen su ke ba da sha'awa ga wasu matasan 'yan Najeriya su shiga harkar damfara. A yanzu matasan Najeriya da yawa na ganin damfara ta intanet a matsayin halastacciyar hanyar samun kudi.

A watan Mayu, Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Ta'annati, EFCC, ta kai samame a wata makaratar 'yan Yahoo Yahooo a Legas inda ta tsare shugaban makarantar da dalibai takwas da ake zargi da koyon dabarun damfara a intanet.

Kamen da FBI ke yi jefi-jefi kan ba da mamaki da zubar da mutunci. Yana kuma zama lokaci na bincikar kai da kai ko yaya ne.

Gidajen jaridu na cikin gida sun wallafa labarai da sharhi kan Misata Okeke da sauran wadanda ake zargi - wadanda kotu ce kadai za ta iya tabbatar da laifinsu. A hannu guda kuma masana sun ba da shawarwari kan abubuwan da ya kamata a yi domin raba matasan Najeriya daga aikata miyagun ayyuka.

An yada wasu hotunan bidiyon wanda ake zargin yana facaka da dukiya.

Daga cikin hotuna akwai na wani biki da ya shirya inda mutane na rawa suna tattake dakartun dala dake zube a kasa. Akwai kuma inda aka nuna an jike shi da ruwan wata giya ta alfarma.

An kuma yada hotunan wasu daga cikinsu a tare da wasu manyan jami'an gwamnati.

Yawancin kusoshin gwamnatin da aka yi wa shagube saboda hotunan sun yi saurin nesanta kansu da wadanda ake zargin.

Amma gaskiyar ita ce a wasu lokutan sai ta kasance mun san wadannan 'yan damfaran.

Abokanmu ne da 'yan uwanmu da mazajenmu da samarinmu da danginmu masu durkusawa suna gaida mu.

Wani matashin da sunansa ya fito jerin mutanen da FBI ke nema ruwa a jallo kuma aka kama da laifin damfarar dala miliyan 40 dan wata kawar mahaifiyata ne. A iya sani na mahafiyarsa ita ce matar da ta fi iya ado a isadda nake tasowa a birnin Umuahia dake kudu masu gabashin Najeriya.

'Wadannan macutan na mana tunkaho da rayuwarsu ta karya. Muna halartar bukukuwansu na alfahari da almubazaranci.

EFCC da FBI

Asalin hoton, EFCC/FBI

Bayanan hoto, Hukumomin Najeriya da Amurka na yaki da damfara ta intanet

Su ne manyan baki a wuraren bukukuwanmu. Al'ummominmu da ayyukan agaji ma sun amfana da kudaden.

Amma mun ji kunya sosai da ganin sunayen a jerin sunayen da FBI ta fitar ko aka tsare su. Sun zama babban abin kunya a fadin kasar.

"Wannan babban abin kunya ne ga dukkan 'yan Najeriya," inji mai magana yawun shugaban Najeriya Garaba Shehu, jim kadan bayan an tsare Okeke da sauran 'yan Najeriya da ake zargi da laifin.

Ya kara da cewa "wannan babban tabo ne ga dukkanmu masu zuwa wasu kasashe inda za a rika kallonmu da lafin da wadannan 'yan uwan namu suka aikata."

Masana sun ce idan har kotu ta kama shi da laifin da ake zarginsa, Mista Okeke na iya fuskatan daurin shekara 30. Za a ci gaba sauraron shari'arsa a watan Fabrairun 2020.

Presentational grey line
Presentational grey line

'Yan Najeriya sun damu matuka cewa 'yan damfaran na iya kawo cikas ga karbuwar matasan kasar 'yan kasauwa a duniya.

Suna ganin cewa miyagun na iya kawo wa matasan kasar masu halastattun sana'o'i matsalar samun takardar bizar shiga kasar Amurka domin yin kasuwanci.

Akwai wasu 'yan Najeriya da ke sha'awar wadannan 'yan damfaran.

Karfin hali da basirar masu damfarar wurin cutar mayan masanan kimiya da shugabannin manyan kamfanoni miliyoyin daloli cikin dan lokaci na daga cikin abubuwa masu burge wasu matasan.

Kwatanta idan wadanna matasa masu aikata muggan laifuka na da ababen koyi da kuma karin dama. Kaddara irin gudumowar da za su iya bayarwa domin ci gaban al'umma.