Shugaba Trump ya ce bai damu da barazanar tsige shi ba

Asalin hoton, Reuters/Getty
Shugaban Amurka Donald Trump ya ce ba ya jin wani dar game da yiyuwar tsige shi kan ikirarin da ke cewa ya yi yunkurin jan ra'ayin shugaban Ukraine ya kaddamar da bincike a kan babban dan takarar jam'iyyar Democrat kuma tsohon mataimakin shugaban kasar, Joe Biden.
Da ya ke jawabi a birnin New York, Mista Trump ya zargi 'yan Democrat da yi masa makarkashiya.
An tambayi Trump kan ko ya dauki barazanar tsige shin da gaske, sai ya ce: ''Ko a jikina'' ita ce amsar da ya gaggauta bayar wa.''

Asalin hoton, Getty Images
Sai dai mista Trump na fuskantar matsin lamba kan ya fitar da bayanai game wayar da ya yi da shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky, inda a hirar, Trump ya tabbatar cewa sun tattauna game da zarge-zargen rashawa da ake yi wa Joe Biden da dansa, Hunter, wanda ya shafe tsawon shekara biyar yana aiki da wani kamfanin Ukraine.
Kawo yanzu, babu wata shaida da Mista Trump ya gabatar a kan zarge-zagren da yake yi wa Biden da dan nasa.
Da aka tambaye shi game da takardar bayanan, Shugaba Trump ya ce yana iya fitar da takardar, amma yana fargaba kan irin abin da za ta haddasa a nan gaba.

Asalin hoton, EPA
A halin da ake ciki, 'yan Democrat a majalisar dokokin kasar na matsa lamba kan samun bayanan zarge-zargen da wani mai tona asiri a cikin jami'an bayanan asiri, ya yi wanda shi ne mutum na farko da ya fara nuna damuwa kan wayar.
Shugabar majalisar wakilai, Nancy Pelosi ta sanya nan da Alhamis a matsayin ranar fara wani sabon bincike.











