Shin Birnin Kano ya zama mafakar masu aikata miyagun laifuka?

Kanostate.gov

Asalin hoton, Kanostate.gov

    • Marubuci, Yusuf Yakasai
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa, Abuja

Shekaru da dama, birnin Kano na ci gaba da rike kambunsa na kirarin ko da me ka zo an fi ka.

Masu yabon birnin da kuma masu sukar sa na cewa birnin Kano ya yi fice wajen abubuwan alheri da akasin haka.

Ta ko wane bangare a iya cewa lamarin haka yake, duba da abubuwan arzikin da alkhairi da birnin ya tattara.

Haka kuma a daya bangaren, babu shakka birnin Kano ya shahara wajen wasu miyagun halaye da kuma wasu matsaloli da suka yi wa birnin katutu, ciki har da zama matattara ko mafakar miyagun mutane.

A 'yan watannin nan, sunan Kano ya kara shiga bakin mutane, bayan da aka rinka kama wasu mutane da ake zargi da wasu manyan laifuka akai-akai.

A Kano ne aka kama shahararren wanda ake zargi din nan da satar mutane don neman kudin fansa da safarar makamai Hamisu Wadume, bayan an zargi wasu sojoji da kubutar da shi daga kwararrun 'yan sandan da suka kama shi a jihar Taraba.

Hamisu Wadume

Asalin hoton, Nigeria Police

Bayanan hoto, Hamisu Wadume

An kama Wadume ne a wani gida da ke Unguwa Uku a gabashin birnin Kano.

'Yan kwanaki kadan bayan nan, aka kama jagoran gungun wasu 'yan fashi da suka tare tawagar mataimakin gwamnan jihar Nasarawa a arewa maso tsakiyar Najeriya, inda har suka kashe 'yan sanda biyu da ke yi masa rakiya.

An kama mutumin da ake zargin ne a unguwar Rijiyar Zaki da ke yammacin birnin Kano. An kuma samu bindigogi a gidan.

A watan Yulin 2019 kuma, an kubutar da Magajin Garin Daura a Kano bayan da wasu masu garkuwa da mutane suka dauke shi a gidansa da ke garin Daura a jihar Katsina, bayan ya shafe sama da wata guda a hannun mutanen da suka yi garkuwar da shi.

A tsakiyar watan Agustan 2019 ma, 'yan sanda a Kano sun ce sun kama 'yan fashi takwas da masu garkuwa da mutane 16 a birnin na Kano.

Lokacin da ake tsaka da matsalar Boko Haram a Kano a baya, birnin ya kasance wajen da manyan 'yan Boko Haram suke samun mafaka.

Sau biyu Shugaban Kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau yana tsallake rijiya da baya a Kano.

A lokuta daban-daban, jami'an tsaro sun samu labarin cewa Shekau yana Kano. Sai dai a duka lokatun ba su yi nasara ba a yunkurin da suka yi na kama shi.

Haka kuma a Kano ne aka kama shararren mai magana da yawun Boko Haram Abu Qaqa, ko da yake wasu bayanan na cewa kashe shi jam'ian tsaro suka yi a Kano a kan titin Maiduguri yana gab da shiga birnin na Kano.

Wasu masana al'amuran tsaro na cewa akwai ma wasu gaggan masu aikata laifuka a Najeriya da suke shiga Kano suna fita a lokuta daban-daban, ba tare da hukumomi sun kai ga kama su ba.

Getty Images

Asalin hoton, Getty Images

Wannan Layi ne

Me ya sa Kano ta zama mafakar gaggan masu laifi?

Akwai dalilai da dama da masana harkokin tsaro suka bayar da suke ganin cewa sune suka sa Kano ta zama wani waje da masu laifuka ke zabar fakewa.

Girman birnin da yawan al'umma

Hasasahen hukuma na baya-bayan nan (na shekarar 2016, ya nuna cewa har yanzu Kano ce ke kan gaba wajen yawan al'umma a Najeriya, inda take da mutum sama da miliyan 13.

Ana kiyasin cewa akwai kimanin mutum miliyan hudu da ke rayuwa a kwaryar birnin Kano, ban da dubban daruruwa da ke shiga suna fita a kowace rana.

Masana harkokin tsaro kamar Malam Kabiru Adamu da wasu jami'an tsaro na ganin girman birnin da yawan jama'a na bai wa masu aikata laifuka damar samun mafaka a Kano da kuma sajewa da jama'ar birnin, ba tare da hankalin jama'a ko jami'an tsaro ya kai kansu ba.

A birni mai girma da bunkasa kamar Kano, wanda kuma yake da karancin tanade-tanade irin na sauran manyan biranen duniya masu bunkasa, zai yi wahala a ce an iya sanin duka masu shiga da fita a birinin da kuma bibiyar abubuwan da kowa yake yi.

Cikin sauki shahararren mutum a wani wajen zai iya rayuwarsa tamkar ta gama garin jama'a a Kano, ba ma tare da wani ya damu da ko waye shi ba.

Masana tsaron na da ra'ayin cewa cikin dalilan da ya sa masu laifuka ke samun mafaka a birnin har da yadda ake samun fadaduwar birnin ta duka bangarori, da yadda ake kafa sababbin unguwanni da yin gine-gine ba tare da ingantaccen tsari da sanin yawan gidajen ba.

Sannan akwai batun yadda jama'a ke yanka filaye yadda suka ga dama a gina su ba tare da sanin hukuma ba, shi ma yana taimakawa wajen samar da mafaka ga duk wani gagarumin mai laifi da ke neman maboya cikin sauki da kwanciyar hankali.

NIGERIA POLICE FORCE/TWITTER

Asalin hoton, NIGERIA POLICE FORCE/TWITTER

Karancin 'yan sanda da kayan aiki

Wani dalili da ke da dangantaka da wannan na baya shi ne karancin jami'an tsaro da za su yi dai-dai da yawan jama'ar birnin da kuma jama'ar da suke shiga a kowace rana.

Idan so samu ne ana so a ce duk dan sanda daya yana kula da mutum 450 kamar yadda Majalisar Dinkin Duniya ta bayar da shawara, ko kuma a samar da 'yan sanda 225 ga duk mutum 100,000.

A halin yanzu babu wata kididdiga a bainar jama'a da take nuna yawan 'yan sandan da ake da su a Kano, amma a shekarar 2011, kwamishinan 'yan sandan Kano na lokacin Tambari Yabo Muhammad ya ce akwai 'yan sandan da ba su wuce 10,000 ba a duka fadin jihar Kano.

Wani bincike da wasu malaman nazari kan bayanan kasa na Jami'ar Bayero Kano suka gudanar aka kuma wallafa a wata mujalla a 2013, ya nuna cewa akwai karancin 'ya sanda a Kano, domin kuwa kowane dan sanda daya a Kano yana kula da mutum 539.

Sai dai wasu masanan na ganin ba karancin 'yan sandan ne matsala ba, babbar matsalar ita ce rashin isassun kayan aiki, da karancin horas wa domin samun kwarewa, da kuma karancin amfani da hanyoyin zamani wajen ayyukan tsaro.

Masana al'amuran tsaro na ganin wadannan matsaloli na daga abubuwan da suka bai wa miyagu damar mayar da Kano tudun mun tsira.

Wannan Layi ne

Karbar baki

Kano birni ne da ya shahara da karbar baki da suke zuwa birnin saboda dalilai da dama. An amince cewa karbar baki da garin ke yi shi ya sa Kano ta bunkasa daruruwan shekaru da suka gabata.

Mafi yawancin mutanen garin a yanzu sun je birnin ne daga wasu garuruwa ko ma wasu kasashe da suka hada da kasashen Larabawa da wasu kasashen Afirka.

Wannan halayya ta mutanen birnin ba ta sauya ba daruruwan shekaru da suka gabata har zuwa yau.

Har yau duk wanda ya je birnin yana samun karbuwa cikin sauki, har ma cikin kankanin lokaci ya samu damar kafuwa da zama wani jigo a garin.

Jama'ar Kano a yanzu ba su fiye damuwa da bin diddigin bakon da ya je garin da niyyar zama ba, musamman ma idan ya je wajen wani da ya riga shi zuwa.

Irin wannan halayya ta sa masu neman mafaka suke samun saukin sajewa da jama'ar birnin, su kuma bace a cikin miliyoyin mutane ba ma tare da wani ya lura da su ba.

Majeeda Studio

Asalin hoton, Majeeda Studio

Rashin mayar da hankali daga masu sarautun gargajiya

Sauye-sauye a tsarin shugabanci da zamani ya zo da su, sun rage wa masu rike da sarautun gargajiya karfin iko, da kuma yin wasarare da ayyukan da suke yi a tabbatar da tsaro.

A baya duk bakon da ya je wani waje ya kan nemi izinin zama a wajen masaraucin gargajiya da ke yankin. Amma a yanzu masu unguwanni zuwa sama ba su san mutanen da ke bakunci a yankunansu ba, kuma ba su damu da su san hakan ba.

Hakan ya bai wa masu neman mafaka damar shiga su zauna a ko ina ba tare fargabar cewa za a bankado su ba.

Tawakkali ko kuma sakacin mazauna Kano

Tasirin da addini ya yi a rayuwar jama'ar Kano ya sa jama'a ba sa damuwa da cewa wani da ya zo zai iya yi musu illa a rayuwa.

Suna da yakinin cewa Allah zai karesu daga dukkan wani abu da zai iya samunsu, musamman ma da yake mafi yawan jama'ar birnin sun yarda da cewa babu abin da zai faru sai abinda Allah ya riga ya shirya.

Wannan halayya ta sa su kan zauna sakaka ba tare da daukar wani mataki na kariya ba.

Akwai kuma wasu dalilan da masana suka bayyana a matsayin abubuwan da suka sanya Kano ta zama mafakar miyagu.

Dalilan a cewar masanan sun hada da kasancewar jama'ar birnin ba sa damuwa da duk wanda ya zo da kuma abinda ya zo da shi.

Haka kuma kasancewar garin birnin kasuwanci ya sa jama'a kowa yana ta kansa, yana fatan samun abinda zai rufawa kansa asiri.

Ruwa yana karewa dan kada

Duk da yake cewa ana samun yawaitar masu miyagun laifuka da suka mayar da Kano tudun mun tsira, a sau da dama lissafi yana kwacewa masu neman mafakar a Kano, kuma birnin yana zama tarko ga irin wadannan jama'a.

Bayan ya shafe kwanaki a hannun masu garkuwa da shi, an kubutar da Magajin Garin Daura a Kano, aka kuma kashe daya daga cikin mutanen da suka yi garkuwa da shi, sannan aka kama wasu.

Haka kuma bayan wasu sojoji sun kubutar da Wadume a Taraba, sannan ya koma Kano, jami'an tsaro sun kama shi a inda ya fake a unguwar Hotoro.

Sannan jami'an tsaro sun gano tare da kama jagoran 'yan fashin da suka tare tawagar mataimakin gwamnan jihar Nasarwa har suka kashe 'yan sanda, a unguwar Rijiyar Zaki.

Masana al'amuran tsaro sun bayyana wasu dalilan da suke sa ana samun irin wannan gagarumar nasarar.

Getty Images

Asalin hoton, Getty Images

Hadin kan jami'an tsaro

Kowane bangare na hukumomin tsaro suna da huruminsu da kuma yanayin aikin da ya kamata su yi.

Wani jami'in tsaro ya shaida mani cewa hukumomin tsaro a Kano suna aiki kafada da kafada tsakanin su a duk lokacin da wata hukuma take wani aiki.

Haka kuma ya shaida mani cewa akwai musayar bayanai sosai tsakanin hukumomin.

Jami'in ya kara da cewa, bibiyar duk wani mai laifi da hukumomin tsaro ke yi na taimakawa wajen bankado duk masu laifi.

Wannan Layi ne

Jajircewar jami'an tsaro

Duk da karancin horo da samun hakkokin da suka kamata, jami'an tsaro suna da kazar-kazar wajen kokarin ganin sun yi aikinsu bisa kwarewar da suke da ita.

Hakan ya sa ba su yin kasa a guiwa wajen ganin sun bankado duk wani mai laifi, musamman ma idan wani babban mai laifi ne.

Jami'an tsaro su kan samu karfin gwiwa a duk lokacin da aka ce sun yi wani babban kamu.

Shigar da jama'a cikin al'amuran tsaro

Malam Kabiru Adamu ya ce shirin da 'yan sanda suka fito da shi a Kano a shekarun 2014/2015 kan fadakar da jama'a dangane da al'amuran tsaro, ya taimaka sosai wajen farkar da jama'a da saka su bibiyar abubuwan da ke faruwa a yankunansu.

A cewar masanin "hakan ya sa jama'a sun fadaka tare da daukar cewa samar da tsaro aiki ne da ya rataya a wuyan kowa, ba wai jami'an tsaro su kadai ba."

Salihu Tanko Yakasai

Asalin hoton, Salihu Tanko Yakasai

Wannan Layi ne

Addu'a

Tasirin da musulunci ya yi a rayuwar mutanen Kano da shugabanninsu ya taimaka sosai wajen bankado duk wani mai mummunar dabi'a da ya tunkari jihar da wani mugun nufi.

Mutanen Kano sun yarda da addu'a sosai, don haka sun yi amanna cewa duk wani abin da ya tunkarosu za su ga bayansa da addu'a.

A kowace rana ana gudanar da addu'o'in neman kare Kano a masallatai da makarantu da sauran wuraren taruwar jama'a musamman duk wani taro da yake da nasaba da addini.

Ba wai daidaikun jama'a ba, shugabannin Kano su ne kan gaba wajen jagorantar addu'ar neman kariya ga jihar.

A duk safiya sai malamai sun taru a babban masallacin Kano domin yin addu'a ta musamman ga jihar, sannan a duk ranar Juma'a sai sarkin Kano ya halarci addu'ar mako-mako da malaman suke yi a masallacin karkashin kulawar sarkin, wanda shi ne ya sa suke addu'ar.

Balancy_Emirate photography

Asalin hoton, Balancy_Emirate photography

Ita ma gwamnatin Kano ta kan shirya irin wannan addu'a lokaci zuwa lokaci inda ake gayyatar malamai gidan gwamnati domin yin addu'a ta musamman ga jihar.

Wasu na ganin duk nasarar da ake samu ta bankado masu laifuka a Kano tana samo asali ne daga irin wannan jajircewa wajen addu'a.

Wannan Layi ne

Mafita

Masu lura da al'amuran tsaro dai na ganin akwai hanyoyin da ya kamata a bi domin kakkabe Kano daga miyagun mutane da ke neman mafaka a birnin.

A ganin Malam Kabiru Adamu da wasu manyan manyan jami'an tsaro da ba su so a bayyana su ba, akwai bukatar karin jami'an tsaro a duka fadin jihar.

Suna ganin idan aka duba yawan jama'ar da Kano ke da shi da hada-hadar da ake yi, jami'an tsaron da ke jihar a yanzu sun yi matukar kadan, kuma ba za su iya samar da tsaron da ake bukata ba.

Baya ga karin jami'an tsaro, akwai kuma bukatar samar da kayan aiki na zamani da za su taimaka wajen ganowa da kuma dakile miyagun ayyuka a birnin, kamar yadda wasu masana harokin tsaro suka bayyana.